Martanin Barau da Gwamnatin Kano Ta Nemi a Cafke Shi saboda Zargin Ingiza Rashin Tsaro
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya zargi Gwamna Abba da siyasantar da batun tsaro a Kano
- Wannan na zuwa a matsayin martani ga kalaman gwamnatin Kano da ta zarge shi da kalaman da suka ingiza matsalar tsaro
- Babban 'dan majalisar ya ƙalubalanci gwamnati da ta fitar da bidiyon da take cewa ya yi kalaman da suka karfafa wa ƴan ta'adda guiwa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya roƙi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya daina siyasantar da batun tsaro da ke damun jihar.
Ya ce a halin da ake ciki, kamata ya yi gwamnati ta mayar da hankali a kan warware matsalolin da ke addabar Kano, musamman ta tsaro.

Kara karanta wannan
Shugaban hukuma a Kano ya caccaki Ganduje, ya goyi bayan Abba a kama tsohon gwamna

Source: Facebook
Sanata Barau ya mayar da martani a sakon da ya wallafa a shafin Facebook bayan gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta nemi a kama shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barau ya magantu kan gwamnatin Kano
A cikin sakon da Mai taimaka masa na musamman a kan harkokin labarai, Isma'il Mudashir ya fitar, Sanata Barau ya shawarci gwamnati.
Ya yi mamakin zargin da gwamnatin jiha ta yi cewa maganganunsa na iya kawo cikas ga kokarin da ake yi na inganta tsaro.
Mataimakin shugaban majalisar ya ce rashin tsaro a sassan Kano, na bukatar haɗin kai daga dukkannin masu ruwa da tsaki.
Sanata Barau ya karyata zargin gwamnatin jiha, yana mai cewa kamata ya yi ta nuna bidiyon da ta ke cewa ya yi kalaman da za su iya ta’azzara rashin tsaro.
Ya ce:
“An ja hankalin ofishin mataimakin shugaban majalisar dattawa kan ƙarya maras tushe da gwamnatin jihar Kano ta yada ta bakin Kwamishinan yaɗa labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya, cewa mai girma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya yi magana da ka iya kawo cikas ga harkokin tsaro.”
Sanata Barau ya shawarci gwamnatin Abba
Sanata Barau, wanda shi ne Mataimakin Kakakin Majalisar ECOWAS, ya roƙi Gwamna Abba da ya tashi tsaye wajen gyaran Kano a maimakon ƙirƙirar ƙarya.
Ya ce:
“Kafin a lalata mulki, jihar mu Kano tana kusa da Legas wajen bunƙasa. Amma rashin ingantaccen shugabanci ya lalata wannan. Muna da duk abin da ake bukata don dawo da martabar jihar, amma gwamnan bai ɗauki mataki ba.”
Barau ya ce ya ba da tallafi mai yawa don inganta tsaro, ciki har da motocin aiki ga dukkanin rundunonin ‘yan sanda a mazabarsa.

Source: Facebook
Ya kafa da cewa ya raba babura ga jami’an da ke aikin Kano ta Arewa, tare da gyaran sassan hedikwatar ‘yan sanda da gina sababbin ofisoshi.
Ya kuma tallafa wa DSS da kuma samar da cibiyoyin horo na NSCDC a Gwarzo, na hukumar PSC mai kula da harkokin 'yan sanda da na hukumar lura da shige da fice Bichi. Barau ya ce ya kuma saka fitilu masu aiki da hasken rana a dukkanin mazabarsa da wasu sassan jihar don sauƙaƙa sintiri da daddare. Ya kara da cewa:
"Gwamnati ta yi koyi da shi maimakon yin zarge-zarge marasa amfani.”
A kan wannan dambarwa, kungiyar ƴan jarida masu kishin Kano ta KCJF ta nuna damuwa yadda batun siyasa ke ƙoƙarin mamaye tsaro.
Ta shaidawa Legit cewa wannan na shi ne lokacin da manyan ƴam siyasar Kano ya kamata su rika zargin nuna da ingiza rashin tsaro ba.
Mai magana da yawun kungiyar, Mukhtar Yahya Usman ya ce:
"Idan suka ci gaba da irin wannan musayar kalamai, zai kara yamutsa harkar tsaro, lamari zai dagule, jama'a za su wahala."
Ya shawarci ƴan siyasa da su ajiye batun bambancin ra'ayin siyasa, a ceto Kano daga zama kamar wasu jihohi a Najeriya.
Gwamnatin Kano na so a kamo Ganduje
A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ta sake dura a kan tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
A wannan karon, ana neman a kama shi kuma a bincike shi bisa zargin yin kalaman da ka iya tayar da tarzoma da kuma kawo cikas ga kokarin tabbatar da tsaro a jihar. Wannan matakin, ya fito ne daga taron majalisar zartarwa ta jihar karo na 34 da aka yi a ranar Alhamis a Fadar Gwamnatin Kano, inda ta caccaki kalaman tsohon gwamnan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

