Jerin Gwamnonin da Suka Halarci Jana'izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi
- Bauchi ta cika makil yayin jana'izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, jagoran Tijjaniyya, inda dubban mabiya suka taru daga sassa daban-daban
- Gwamnan Kano, Abba Kabiru Yusuf tare da wasu gwamnoni Arewa sun halarci sallar jana'izar tare da manyan jami’an gwamnatin Najeriya
- An jinkirta sallar jana'izar da Sheikh Sharif Ibrahim Saleh ya jagoranta saboda taron jama'a da suka mamaye filin Idi da titunan kusa da shi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi – Bauchi ta cika makil jiya yayin da dubban mutane suka taru a babban birnin jihar domin halartar jana'izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
An taru ne domin sallar gawar shahararren malamin addini da jagoran Darikar Tijjaniyya, wanda ya rasu ranar Laraba da dare.

Source: Facebook
Mai magana da yawun shugaban gwamnonin Arewa, Ismaila Uba Misilli ya wallafa a Facebook cewa gwamnan Gombe ya halarci jana'izar.

Kara karanta wannan
Allahu Akhbar: An yi jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi, an birne gawarsa a masallaci
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnonin da suka je jana'izar Dahiru Bauchi
Gwamnonin jihohi daban-daban, ciki har da na Kano, Abba Kabiru Yusuf sun halarci jana'izar Dahiru Usman Bauchi.
Baya ga Abba, an ga manyan jami'an gwamnatin Kano da wasu 'yan siyasar jihar irinsu Sanata Kawu Sumaila.
Kama yadda Legit Hausa ta fahimta, Gwamnanonin jihar Neja, Umaru Bago da na Gombe, Inuwa Yahaya sun halarci jana'izar.
Mai masaukin baki, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya shaida sallar jana'izar.

Source: Facebook
A kalla gwamnoni masu ci aka yi sallar jana'izar babban malamin da su a Bauchi.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, Atiku Abubakar da Nuhu Ribadu ma sun hallara wajen jana'izar.
Sallar jana'iza da hada dubban mabiya
An shirya sallar jana'izar ne da misalin karfe 3:00 na rana, amma ba a fara ba har sai karfe 4:36 saboda taron jama'a da suka mamaye filin Idi.
Hakan ya sa dubban maza, mata, yara da tsofaffi suka yi sallah daga titunan kusa da filin ba tare da samun damar shiga ba.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa filin idin ya cika sosai, lamarin da ya tilasta wa mutane da dama halartar sallar daga waje.
Mutane sun je Bauchi daga jihohi
Mahalarta sallar jana'izar sun fara isa Bauchi tun safiyar ranar Alhamis bayan sanarwar rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi.
Zuwa ranar Juma’a, an ga mutane suna shiga babban birnin ta dukkan manyan hanyoyi, suna tafiya cikin manyan motoci, bas, da sauran motocin haya.
An samar da motoci kyauta a Gombe
Yayin tattauna da malam Ahmadu Adamu da ke jihar Gombe, ya bayyana wa Legit cewa an samar da motocin zuwa jihar Bauchi kyauta.
"Duk wanda ya so zuwa jana'izar mota kyauta ne. mutane sun kawo motoci domin ba jama'a damar shiga su je sallar jana'izar."
Ya kara da cewa:
"An ce gwamnatin Gombe ta kawo motoci amma dai shi kam ban tabbatar ba."
Yadda Dahiru Usman Bauchi ya rasu
A wani labarin, mun kawo muku cewa sakataren Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayar da labarin yadda malamin ya rasu.
Malam Baba Ahmad ya bayyana cewa marigayin ya ci abincin dare kafin jikinsa ya fara nuna alamun rashin lafiya.
Ya kara da cewa bayan kai malamin asibiti likitoci sun yi kokarin ceto rayuwarsa amma rai ya riga ya yi halinsa cikin dare.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

