Lambar Sojojin da Suka Janye kafin Sace Dalibai a Kebbi Ta Fito, Hedkwatar Tsaro Ta Dauki Mataki
- Janyewar da sojoji suka yi daga makarantar GGCSS Maga a jihar Kebbi ya jawo musu suka daga wajen gwamnati da sauran jama'a
- Gwamnatin Kebbi ta bukaci a gudanar da bincike domin gano dalilin da ya sanya sojojin suka janye kafin harin da 'yan bindiga suka kai
- Wannan koken ya kai wajen hedkwatar tsaro ta kasa inda ta gayyaci sojojin da ke da alhakin gadin makarantar domin fara binciken lamarin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta fara bincike kan sojojin da suka janye kafin harin 'yan bindiga a makarantar GGCSS Maga da ke jihar Kebbi.
Dukkanin sojojin da aka tura makarantar inda aka sace dalibai mata 25 na shan tambayoyi a hedkwatar tsaro ta kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan
Obasanjo ya fadi matsayarsa kan tattaunawa da 'yan bindiga, ya ba gwamnati shawara

Source: Twitter
Wani babban jami’in gwamnati ya tabbatar da hakan ga jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane mataki Hedikwatar sojoji ta dauka?
Ya bayyana cewa DHQ ta fara bincike kan yadda aka janye sojojin daga makarantar kwatsam kafin harin na ’yan bindiga.
Jami’in ya ce gwamnatin Kebbi tana jiran sakamakon binciken da sojoji ke yi kan wanda ya bayar da umarnin janye sojoji daga makarantar kafin harin.
"An umarci sojojin da aka tura makarantar da su bayyana Abuja domin yi musu tambayoyi. Hedikwatar tsaro ta kira su tun ranar Litinin. Muna bibiyar lamarin.”
- Jami'in gwamnati
Jami’in ya kara da cewa sojojin sun fito ne daga barikin sojoji da ke Zuru.
Ana bincike kan sojojin da suka janye a Kebbi
Wata sahihiyar majiyar tsaro da ta sha bayar da ingantattun bayanai ga jaridar ya tabbatar da cewa an kira sojojin zuwa DHQ.
“Ban da cikakken bayani, amma na ji daga abokai a rundunar sojoji cewa sojojin sun isa hedikwatar."

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta biya kudin fansa kafin ceto 'daliban Kebbi? Majalisa ta yi bayani
"Dukkan manyan shugabannin tsaro ba su ji dadin abin ya faru a Kebbi da Neja ba. Sojoji ko ’yan sanda ba su yi abin da ya kamata ba. Amma ana ci gaba da bincike.”
- Wata majiya
Wani babban jami’in soja wanda ya nemi a boye sunansa ya tabbatar da cewa bincike yana gudana.
“Ana gudanar da bincike, kuma duk wanda ya taba aiki a makarantar za a tambaye shi domin gano ainihin abin da ya faru. Duk wanda aka samu da laifi tabbatacce za a hukunta shi.”
“Ba abin mamaki ba ne idan aka kira sojojin saboda wannan lamari, amma bincike har yanzu yana gudana.”
- Wani jami'in soja

Source: Twitter
Abin da hukumomi suka ce kan lamarin
An nemi jin ta bakin daraktan yada labarai na hedkwatar tsaro, Manjo-Janar Michael Onoja, amma ba a iya samun shi ba yayin da ake kammala hada wannan rahoton.
Da aka tuntubi kakakin gwamnan jihar Kebbi, Ahmed Idris kan lamarin, ya ce ba zai iya tabbatar da kiran sojojin ba.
“Hedkwatar tsaro ce ke gudanar da binciken, saboda haka ba mu da cikakken bayani. Amma muna son mu ga sakamakon binciken, kuma muna sa ran sojoji za su dauki matakin da ya dace.”

Kara karanta wannan
Majalisa ta tsoma baki da Jonathan ya makale a kasar da sojoji suka yi juyin mulki
- Ahmed Idris
An ceto daliban sakandaren Kebbi
A wani labarin kuma, kun ji cewa daliban da 'yan bindiga suka sace a makarantar GGCSS Maga da ke jihar Kebbi, sun shaki iskar 'yanci.
Majiyoyi sun tabbatar da ceto daceto ɗalibai mata guda 25 da aka sace daga makarantar mata da ke Maga a jihar Kebbi.
Gwamnatin Kebbi ta bayyana cewa ba a biya 'yan bindiga kudin fansa ba kafin su sako daliban da suka sace.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng