Babbar Magana: Gwamnatin Kano Ta Bukaci a Kama Tsohon Shugaban APC, Ganduje

Babbar Magana: Gwamnatin Kano Ta Bukaci a Kama Tsohon Shugaban APC, Ganduje

  • Gwamnatin Kano ta nuna damuwa kan kalaman tsohon shugaban APC, Dr. Abdullahi Ganduje da shirinsa na kafa Hisbah mai zaman kanta
  • Majalisar Zartarwa ta Kano ta cimma matsaya a taron da ta gudanar karo na 34 a fadar gwamnatin jihar yau Juma'a 28 ga Nuwamba 2025
  • Kwamishinan yada labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya ya ce gwamnatin ta bukaci a kama Ganduje domin ya yi bayani dalla-dalla

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta sake taso tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Gwamnatin ta nemi a kama kuma a binciki tsohon gwamnan bisa zargin yin maganganun da ka iya tayar da tarzoma da kuma kawo cikas ga kokarin tabbatar da tsaro a jihar Kano.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Tsohon shugaban APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje CFR
Source: Facebook

Daily Trust ta ce gwamnatin Abba ta dauki wannan mataki ne a taron majalisar zartarwa na 34, wanda aka gudanar a ranar Alhamis a Fadar Gwamnatin Kano.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta biya kudin fansa kafin ceto 'daliban Kebbi? Majalisa ta yi bayani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane kalamai Abdullahi Ganduje ya fada?

Majalisar ta tattauna kan wasu kalamai da Ganduje tare da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, suka yi kan lamarin tsaron jihar Kano.

Ganduje da Barau sun yi ikirarin cewa Kano na kara fuskantar barazanar ’yan bindiga tare da shirin daukar jami'ai 12,000 na Khairul Nas, wata sabuwar rundunar Hisbah mai zaman kanta.

Da yake karin haske kan sakamakon taron ga 'yan jarida, Kwamishinan Yada Labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce maganganun na iya dagula kokarin gwamnatin tarayya da ta jiha wajen samar da tsaro.

Gwamnatin Kano ta nemi kama Ganduje

Ya ce abin damuwa ne ganin cewa kasa da awanni 48 bayan wadannan maganganu, an sami rahoton cewa wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun yi yunkurin shiga wasu kauyuka a iyakar Kano.

“Ba mu san abin da Ganduje ke nufi da waɗannan kalamai ba, shi ya sa muke kira a kama shi. Dole a bincike shi, domin ba za mu bari ya tayar da hankalin Kano ba,” in ji Waiya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya nada shugaban NIA da ya shiga badakalar $43m lokacin Buhari a matsayin Jakada

Gwamnatin Kano ta gode wa gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro bisa hadin kai da taimakon jihar, tana mai nanata cewa ba za ta lamunci haka kurum wani mutum ko kungiya ta kafa rundunar tsaro ba.

Gwamma Abba Kabir.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnatinsa Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Ta kuma yi kira ga manyan ’yan siyasa da su guji kalaman da za su iya haifar da tashin hankali ko kara dagula matsalar tsaron da ake fama da ita.

Gwamnatin ta tabbatar wa al’ummar Kano cewa za ta ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya, tsaro, da bin doka a ko’ina cikin jihar, cewar rahoton Leadership.

An samu tsaiko a shari'ar Ganduje

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Kano ta kawo tsaiko a zaman shari'ar tsohon shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Yayin da aka dawo zaman shari’ar a ranar Laraba, lauyan gwamnatin Kano, Jedidiah Akpata ya shaida wa kotu cewa ba su shirya ci gaba da zaman ba.

Bayan sauraron kowane bangare, Babbar Kotun Kano ta dage shari’ar tsohon gwamna, Ganduje da wasu mutum bakwai zuwa 3 ga Fabrairu, 2026.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262