An Yanke wa Dalibin Jami'a Hukuncin Kisa a Najeriya, Za a Rataye Shi har Lahira
- Wata kotu a Rivers ta yanke hukunci cewa dalibin jami'ar UNIPORT, Damian Okoligwe ne ya kashe Justina Otuene a 2023
- Kotun ta bayyana cewa hujjoji da shaidun da gwamnati ta gabatar sun tabbatar da cewa Damian ya yi kisan da gangan
- Mai shari'a Nsirim-Nwosu ta yanke hukunci cewa a rataye dalibin jami'ar, Damian har sai an tabbatar da cewa ya mutu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Rivers - Wata babbar kotu a Fatakwal, jihar Rivers, ta samu Damian Okoligwe, ɗalibin jami'ar Fatakwal (UNIPORT) da laifin kashe budurwarsa, Justina Otuene.
Damian Okoligwe ya kasance dan aji hudu a sashen Petrochemical Engineering yayin da masoyiyarsa da ya kashe, Justina Otuene, ta ke aji uku a sashen Biochemistry na jami’ar.

Source: Getty Images
Alkalin kotun, Justice Chinwe Nsirim-Nwosu, ya yanke wa Okoligwe hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan an gabatar wa kotu isassun hujjoji da suka tabbatar da laifin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka gano dalibin jami'ar ya kashe Justina
Rahoto ya nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar 20 ga Oktoba, 2023, a sabon gidan dalibin jami'ar da ke Mgbuoba, karamar hukumar Obio/Akpor LGA.
An bayyana cewa Okoligwe ya kashe Justina sannan ya yi gunduwa gunduwa da naman jikinta, ya nannaɗe a cikin jaka sannan ya sanya ta a baro.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar a lokacin, ya ce jami’an 'yan sanda na ofishin Ozuoba ne suka yi bincike bayan makwabta sun koka kan warin gawa da ke fitowa daga gidan dalibin.
Bayan an balle kofar gidan, an samu babbar jaka cike da sassan jikin marigayiyar. Da fari an ce dalibin ya tsere, amma daga bisani aka kama shi.
Abin da dalibin jami'a ya ce da aka kama shi
A lokacin da aka gabatar da shi gaban manema labarai suna yi masa tambayoyi a hedikwatar 'yan sanda da ke Fatakwal, Okoligwe ya fadi alakar da ke tsakaninsa da Justina.
Damian Okoligwe ya ce shi da Justina saurayi da budurwa ne, kuma ba wai sun yi wani zurfi a soyayyar ba, kawai suna haduwa ne idan suna son ganin juna.
Ya kuma tabbatar da cewa ya kama hayar gidan da aka tsinci gawar matashiyar ne makonni ƙalilan kafin mummunan lamarin ya faru, in ji wani rahoto na Premium Times.

Source: Original
Hukuncin da kotu ta yanke wa dalibin jami'ar
A hukuncin da ya karanta a ranar Juma’a, Mai shari'a Nsirim-Nwosu ta bayyana cewa gwamnati ta tabbatar da dukkan sassan da ake bukata wajen tabbatar da laifin kisa.
Alkalin ta ce:
“An tsara wannan mummunan aiki, an aikata shi da gangan, kuma tsantsar mugunta aka nuna. Babu wani abu da ya ci karo da shaidu da hujjojin da aka gabatar.”
Mai shari'a Nsirim-Nwosu ta ba da umarnin a rataye Damian Okoligwe har sai an tabbatar da rasuwarsa.
An yanke wa mutane 5 hukuncin kisa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wata kotu a Oyo ta samu wasu mutane biyar da laifin kashe direban tasi, bayan wata hatsaniya a Ibadan.

Kara karanta wannan
Kanu da mutanen da suka wakilci kansu a kotu ba tare da lauya ba da yadda ta kaya
Alkalin kotun ta fara yanke wa mutanen biyar hukuncin daurin shekaru 20, sannan ta yanke masu hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Rahotanni sun bayyana cewa wadanda ake zargin sun yi wa direban tasin dukan kawo wuka da ya zama silar ajalinsa a watan Afrilun 2024.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

