Allahu Akhbar: An Yi Jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi, An Birne Gawarsa a Masallaci

Allahu Akhbar: An Yi Jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi, An Birne Gawarsa a Masallaci

  • An yi sallah tare da birne gawar jagoran Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi a masallacinsa da ke cikin garin Bauchi
  • Manyan malamai da shugabannin daga Najeriya da kasashen nahiyar Afirka daban-daban sun halarci jana’izar yau Juma'a
  • Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, da gwamnonin Kano, Bauchi da Neja na cikin manyan da suka halarci jana'izar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - Bayan kwana daya da rasuwarsa, an yi jana'izar fitaccen jagoran Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, a ranar Juma’a 28 ga Nuwamba, 2025.

Rahotanni sun nuna cewa bayan yi masa sallah kamar yadda addinin musulunci ya tanada, an birne gawar Sheikh Dahiru Bauchi a wani bangare a cikin masallacinsa da ke Unguwar Jaki a cikin Bauchi.

Wurin jana'iza.
Yadda mutane suka yi cincirindo wurin jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi Hoto: Rayyan Tilde/Facebook
Source: Facebook

Rahoton Leadership ya ce shehin malamin ya rasu ne da safiyar Alhamis a Asibitin Koyarwa na Jami’ar ATBU, Bauchi, bayan ya yi jinya, yana da shekaru 98 a kalandar miladiyya.

Kara karanta wannan

Shettima da wasu manyan 'yan Najeriya sun halarci jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsawon shekaru da dama, Sheikh Dahiru ya yi fice a duniya wajen yada ilimin addinin Musulunci, gina Darikar Tijjaniyya da yaye dubban mahaddata Alqur’ani ta hanyar tsangayoyinsa.

An yi jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi

A bisa wasiyyarsa, an gudanar da sallar jana’iza a filin Idi na Bauchi, wadda fitaccen malamin addini, Sheikh Shariff Ibrahim Saleh Al-Hussaini ya jagoranta.

Da yake jan hankali, Sheikh Shariff Saleh ya bukaci mabiyan Darikar Tijjaniyya da su ci gaba da nuna tawali’u, tsoron Allah, da girmama juna, yana mai cewa waɗannan su ne ginshikan rayuwar Shehu Dahiru.

Ya ce rasuwar marigayin, “ta bar gibi da ba kowa zai iya cikawa ba, amma koyarwarsa za ta ci gaba da haskaka miliyoyin mutane.”

Manyan bakin da suka halarci jana'izar

Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya halarci jana’izar tare da gwamnonin Bauchi, Kano, da Neja.

Shettima ya yi ta’aziyya ga iyalan marigayin, yana mai cewa rayuwar Sheikh Dahiru abin koyi ce wajen jagoranci, zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin addinai.

Kara karanta wannan

Daga karshe, an ji dalilin da ya sa aka jinkirta jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi

Tawagogin Darikar Tijjaniyya daga kasashen Morocco, Mauritania, Kamaru, Nijar Benin da Chadi duk sun halarci jana’izar, alamar da ke nuna tasirin Shehun a duniyar Musulunci a Afirka.

Shehu Dahiru Bauchi.
Dubbban daruruwar musulmi da suka halarci jana'izar Dahiru Bauchi Hoto: Rayyan Tilde
Source: Facebook

Sauran jiga-jigan da suka halarci jana'izar sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu.

Mataimakin gwamnan Borno, Umar Kadafur, Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tiggar, Ministan Lafiya, Farfesa Ali Pate da sauransu sun halarci jana'izar Dahiru Bauchi, in ji rahoton Daily Trust.

Dalilin jinkirta jana'izar Dahiru Bauchi

A wani labarin, kun ji cewa 'daya daga cikin 'ya'yansa, Nasiru Dahiru Bauchi ya yi bayani kan abin da ya jawo jinkirin jana'izar zuwa ranar Juma'a.

Naziru Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewa sun yanke shawarar jinkirta jana'izar Shehun ne saboda bai wa wadanda ke nesa damar halarta.

Ya ce daga cikin wadanda aka duba aka jinkirta jana'izar domin su halarta akwai Sheikh Shariff Ibrahim Saleh, wanda marigayin ya yi wasiyyar cewa shi yake so ya masa sallah.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262