'Manyan Mutane 5 Ke Daukar Nauyin 'Yan Ta'adda a Najeriya,' Malami Ya Fasa Kwai

'Manyan Mutane 5 Ke Daukar Nauyin 'Yan Ta'adda a Najeriya,' Malami Ya Fasa Kwai

  • Fitaccen malamin addini, Primate Elijah Ayodele ya ce mutane biyar masu karfin iko a Najeriya ne ke jagorantar ta’addanci
  • Primate Ayodele ya ce har sai gwamnatin Bola Tinubu ta gano wadannan mutane ta kawar da su za a samu zaman lafiya
  • Ya gargadi Tinubu da kada ya bari kowa ya jagoranci tattaunawa da ‘yan ta’adda, inda ya kalubalanci Sheikh Ahmad Gumi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya sake tayar da kura a cikin tattaunawar da ya yi game da tsaro a Najeriya.

Primate Ayodele ya bayyana cewa akwai manyan mutane biyar masu rike da madafun iko da ke daukar nauyin ta’addanci da garkuwa da mutane a Najeriya.

Primate Elijah Ayodele ya ce akwai manyan mutane 5 da ke bayan ayyukan ta'addanci a Najeriya.
Fitaccen malamin addinin Kirista, Primate Elijah Ayodele ya na jawabi ga manema labarai. Hoto: @primate_ayodele
Source: Facebook

'Mutane 5 ke daukar nauyin ta'addanci' - Ayodele

Fitaccen malamin addinin Kiristan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa wajen watsa labarai, Osho Oluwatosin, ya fitar, in ji rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Daga cacar baki, matasa sun caccaka wa babban dan sanda wuka, ya sheka lahira

A cikin sanarwar, Primate Ayodele ya ce ba za a taba samun cikakken tsaro ba har sai gwamnati ta gano wadannan mutane ta kuma “kawar da su daga hanya."

A cewarsa, waɗannan manyan mutane suna da karfi sosai, suna kuma ci gaba da daukar nauyin ayyukan ta’addanci a sassan kasar.

Ya ce:

“Mutane biyar ne ke da hannu a yawan sace-sacen nan. Sai gwamnati ta gano su ta kuma kawar da su daga hanya, idan ba haka ba Najeriya za ta ci gaba da zama a hannun ‘yan ta’adda.
"Ba sa sassautawa, idan gwamnati ta yi sake, za su ci gaba da addabar kasar da munanan hare-hare.”

Malamin ya gargadi Tinubu kan sulhu da ‘yan ta’adda

Primate Ayodele ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kada ya amince da kiran tattaunawa da ‘yan ta’adda, ko me zai faru.

Ya ce irin kiran da malamai ko wasu shugabanni ke yi, ciki har da Sheikh Ahmad Gumi, yana kara saurin yawaitar hare-hare.

Kara karanta wannan

"Mun san su": Sanata Maidoki ya ba gwamnati zabi 2 kan kawo karshen 'yan bindiga

A cewar Ayodele:

“Ya kamata Tinubu ya gargadi wadanda ke goyon bayan tattaunawa da ‘yan ta’adda su shiga taitayinsu.
"Bai kamata a bar mutanen da ke da irin wannan ra’ayi su wakilci gwamnati ba. Yawan tattaunawa na jawo karin ta’addanci, kuma shi (Tinubu) ganin illar hakan.”
Primate Elijah Ayodele ya ce dole a kawar da mutane 5 daga hanya domin kawo karshen matsalar tsaro
Primate Elijah Ayodele ya gargadi Shugaba Bola Tinubu kan sulhu da 'yan ta'adda. Hoto: @primate_ayodele, @officialABAT
Source: Facebook

“Sulhu ya mayar da ta’addanci babban kasuwanci”

A cewar malamin, tattaunawar sulhu da wadanda ke sace mutane ya kara basu kwarin guiwar, tare da mayar da ta’addanci wata babbar hanyar samun kudi.

Malamin ya kuma nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta amincewa da kirkirar 'yan sandan jihohi domin yakar 'yan ta'adda, cewar rahoton Daily Post.

Ya kara da cewa akwai tasirin wasu kasashen waje da ke tallafawa ko ingiza ta’addanci a Najeriya, abin da ya sa yaki da matsalar ya zama mai wahala.

“Tattaunawa ta mayar da ta’addanci cibiyar kasuwanci. Akwai kasashen waje da ke da hannu cikin wannan matsala. Idan ba a dauki mataki ba, ta’addanci zai yi amfani da matsalar tsaro wajen murkushe gwamnatinku. Ba talakawa kadai zai shafa ba, hatta masu kudi za su sha kuka.”

Kara karanta wannan

Kaduna: Limamin addini ya mutu a hannun 'yan ta'adda kafin a biya kudin fansa

- Primate Elijah Ayodele.

Ayodele ya ba Tinubu shawara kan tsaro

A wani labari, mun ruwaito cewa, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya gargadi Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ayodele ya gargadi Tinubu cewa matsalar tsaro ba za ta kare ba, muddin ba a ɗauki matakin kama masu karfafawa da ɗaukar nauyin ta’addanci ba.

Malamin ya dage cewa ci gaba da bada kariya ga manyan mutane da ake zargi suna tallafa wa ayyukan ta’addanci shi ne babban dalilin ta'azzar rashin tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com