Gwamnatin Tinubu Ta Biya Kudin Fansa kafin Ceto Daliban Kebbi? Majalisa Ta Yi Bayani

Gwamnatin Tinubu Ta Biya Kudin Fansa kafin Ceto Daliban Kebbi? Majalisa Ta Yi Bayani

  • Har yanzu ana ci gaba da ce-ce-ku-ce kan hanyar da gwamnatin tarayya ta bi wajen ceto daliban Kebbi da Neja daga hannun 'yan bindiga
  • Mai magana da yawun Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu ya yi bayani kan zargin cewa gwamnati ta biya kudin fansa
  • Majalisar dattawa ta kafa kwamitin bincike kan yadda aka sace daliban Kebbi da kuma mutuwar Birgediya Janar Musa Uba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ana ci gaba da yada jita-jitar cewa gwamnatin tarayya ta biya 'yan bindiga kudin fansa kafin ceto daliban da aka sace a jihohin Kebbi da Neja.

Majalisar Dattawan Najeriya ta fito ta yi karin haske kan zargin biyan kudin fansa tare da daukar matakan bincike don gano abin da ya jawo sace daliban.

Sanata Yemi Adaramodu.
Mai magana da yawun Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu Hoto: @YemiAdaramodu
Source: Twitter

Da yake hira da Channels TV a shirin Morning Brief ranar Juma’a, Mai magana da yawun majalisa, Sanata Yemi Adaramodu ya ce gwamnatin tarayya ba ta biya kudin fansa ba.

Kara karanta wannan

"Mun san su": Sanata Maidoki ya ba gwamnati zabi 2 kan kawo karshen 'yan bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalaman sanatan na zuwa ne bayan Bayo Onanuga, Mai ba Shugaba Tinubu shawara kan yada labarai, ya ce jami’an tsaro sun tattauna kai tsaye da masu garkuwa don ceto wasu daga cikin mutanen da aka sace a Kwara.

Gwamnatin Tinubu ta biya kudin fansa?

Sanata Yemi Adaramodu ya ce:

"A bangaren Majalisa, mun yarda cewa gwamnati ba ta biya kudin fansa ga kowa ba. Batun an yi mu’amala da ’yan bindiga, na iya zuwa ta hanyoyin daban-daban — na tilastawa, na lallashi ko a hada duka biyu.”

Adaramodu ya ce ba dole ba ne hukumomin tsaro su fito su bayyana cikakken dabarar da suka yi amfani da ita wajen ceto wadanda aka yi garkuwa da su ba.

Dangane da shakkun da jama'a ke yi kan yadda aka ceto mutane ba tare da kama maharan ko musayar wuta ba, sanatan ya ce hakan ba yana nuna ba yi arangama ba.

Kara karanta wannan

Shawarar da Gwamna Nasir ya ba daliban da 'yan bindiga suka saki a Kebbi

“Idan ba ku ga an kama su ko gawawwakin su ba, hakan ba yana nufin ba a yi faɗa ba. Sau da yawa suna gudu su bar wadanda suka sato idan suka ga jami’an tsaro sun kusa cimmasu," in ji shi.
Sanata Yemi Adaramodu
Mai magana da yawun Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu Hoto: @NGRSenate
Source: Twitter

Majalisa ta kafa kwamitin bincike

Sanata Adaramodu ya tabbatar da cewa Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin wucin-gadi domin bincikar yanayi da dalilan sace daliban Kebbi da kira Birgediya Janar Uba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Rahotannin farko daga jami’an tsaro da gwamnatin Kebbi sun nuna cewa sojojin da ke gadin makarantar sun bar wurin kafin maharan su isa, lamarin da ya jawo ayar tambaya.

Gwamnan Kebbi ya roki a yi bincike

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kebbi ya sake nuna damuwarsa kan yadda sojoji suka janye kafin 'yan bindiga su kai hari makarantar GGCSS Maga.

Ya bukaci a binciki dalilin da ya sa aka janye sojojin da aka tura zuwa makarantar sakandire ta Maga, mintuna kaɗan kafin ’yan bindiga su sace dalibai 25.

Gwamna Nasir Idris ya bukaci rundunar sojojin da ta canja dabarar da take amfani da ita wajen yaki da matsalar tsaro a jihar da ma Najeriya.baki ɗaya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262