Tuna Baya: Gargadin Dahiru Bauchi Lokacin da Ganduje Ya Tube Sanusi II a Kano
- An tono tsohon bidiyon Sheikh Dahiru Bauchi yana jan hankalin al’ummar Kano da su guji tayar da hankula da gargadin cewa fitina za ta jawo hasara
- A bidiyon, marigayin ya bayyana cewa tashin hankali na iya jawo barna saboda masu kuɗi da iko za su iya ba da umarnin harbin mutane
- Sheikh Dahiru Bauchi ya shawarci mutane su bar komai ga ikon Allah, yana rokon Ubangiji ya kare jama’a tare da yi wa Sarki Sanusi II fatan alheri
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - An sake fito da wani tsohon bidiyo wanda marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ke magana game da masarautar Kano.
Wannan ya biyo bayan rasuwar marigayin a jiya Alhamis 27 ga watan Nuwambar 2025 bayan fama da jinya na tsawon lokaci.

Kara karanta wannan
Allahu Akhbar: An yi jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi, an birne gawarsa a masallaci

Source: Facebook
Bidiyon da Dahiru Bauchi ke shawartar yan Kano
A cikin bidiyon da shafin Muhammad Sanusi II Study Snippets ya wallafa a X a yau Juma'a 28 ga watan Nuwambar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayin ya yi magana mai kama hankali game da lamarin musamman wurin yin gargadi ga mabiyansu a Kano.
A bidiyon, dattijon ya shawarci al'umma da ka da su tayar da hankula saboda rashin sanin abin da ka iya biyo baya.
Ya ce:
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, tun jiya muke aikawa mutanenmu a Kano a gaya wa kowa da kowa ka da a tada hankali.
"Muna fada musu ka da a tada hankali, wannan tada hankalin, wani abu ne zai faru da bai faru ba, wannan kam ya riga ya faru mun gani.
"Idan an tada hankali kuma wani abu ya faru, su ke da wuta da kudi a hannunsu, suna iya ba da umarni a harbe mutane babu yadda aka iya."

Source: Facebook
Addu'o'in Dahiru Bauchi ga Sanusi II a baya
Marigayin a wancan lokaci ya ce a zubawa sarautar Allah ido saboda ba a san abin da tashin hankali zai kawo ba.
Daga karshe, Dahiru Bauchi ya yi wa Sarki Muhammadu Sanusi II addu'o'i na musamman tare da fatan Allah ya albarkaci rasuwarsa.
"Saboda haka gwara a yi shiru din a zubawa sarautar Allah ido, Ubangiji ya saka mana da alheri, ita kuma wannan kaddara Allah ya riga ya kawo ta, amma ba mu san karshensa ba.
"Muna rokon Allah ya kiyaye mu da jama'armu, yanzu tun da ba mu da gwamnati a hannunmu, mune ihunka banza, komai muka yi, ba za a saurare mu ba.
"Shi kuma Sarkin Kano Sanusi Allah ya saka masa da alheri, Allah ya gyara rayuwarsa bayan wannan lamari."
- Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi
'Zan yi shekaru 102' - Sheikh Dahiru Bauchi
An ji cewa malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya taba bayyana adadin shekarun da zai kwashe a raye.
Daya daga cikin makusantansa, kuma mai magana da yawunsa, Muhammad Daha Al-Azahari ya ce malamin ya nanata masa shekarun.
Ya ce daga baya ya fahimci ba shi kadai ya san da maganar ba, kuma malamin ya rasu a wadannan shekaru da ya bayyana masu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

