An Rasa Rai bayan Gwabza Fada tsakanin Monoma da Makiyaya a Bauchi

An Rasa Rai bayan Gwabza Fada tsakanin Monoma da Makiyaya a Bauchi

  • Fada tsakanin manoma da makiyaya ya ɓarke a ƙauyen Bursali da ke Zaki, jihar Bauchi, bayan samun rikici kan amfani da gonakin yankin
  • Rikicin ya yi sanadin mutuwar wani makiyayi, inda rundunar ’yan sanda ta damke mutane shida da ake zargi suna da hannu cikin faruwar lamarin
  • Lamarin ya samo asali ne daga zargin cewa makiyaya daga Jigawa sun shiga gonaki ba tare da izini ba, abin da ya janyo tashin hankali

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - A kalla mutum ɗaya ya rasa ransa yayin da fada tsakanin manoma da makiyaya ya ɓarke a ƙauyen Bursali da ke cikin ƙaramar hukumar Zaki a jihar Bauchi, a ranar 26 ga Nuwamba.

Wani rahoto ya nuna cewa lamarin ya kuma kai ga kama mutane shida da ake zargi da hannu a cikin rikicin.

Kara karanta wannan

Yadda jikin Shehu Dahiru Bauchi ya yi tsanani, aka tafi da shi asibiti ya rasu

Taswirar jihar Bauchi
Taswirar jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa makiyaya Fulani masu yawo daga jihar Jigawa ne suka shiga cikin gonakin mutanen yankin, lamarin da ya tayar da jijiyar wuya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda manoma suka gwabza da makiyaya

Majiyoyi sun bayyana cewa da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar ranar, wasu makiyaya daga Jigawa sun shigo cikin gonakin manoman yankin ba tare da izini ba.

Wani rahoto ya bayyana cewa dabbobin makiyayan sun lalata amfanin gona, hakan ya fusata manoma, suka yi zargin cewa ba shi ne karo na farko makiyaya ke shiga gonaki suna barna ba.

Fadan ya fara da gardama, amma daga bisani ya rikide zuwa tashin hankali, har ya kai ga salwantar rai.

Mutane da dama sun ruga neman mafaka, yayin da wasu kuma suka yi ƙoƙarin shiga tsakanin bangarorin biyu kafin zuwan jami’an tsaro.

Matakin da ’yan sanda suka dauka

Bayan samun labarin faruwar rikicin, ’yan sanda sun isa wurin domin kwantar da tarzoma tare da tabbatar da cewa an dakatar da duk wani yunkurin daukar fansa.

Kara karanta wannan

Jonathan ya makale a Guinea Bissau, sojoji sun rufe kasar bayan juyin mulki

A cikin matakan farko, jami’an tsaro sun cafke mutane shida da ake zargi da rawar gani a cikin fadan.

Sufeton 'yan sandan Najeriya
Sufeton 'yan sanda na kasa, IGP Kayode. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

An kara tabbatar da cewa yankin yanzu yana ƙarƙashin kulawa sosai domin hana sake ɓarkewar wata tarzoma yayin da ake ci gaba da bincike.

Karuwar rikicin manoma da makiyaya a Arewa

Lamarin ya faru ne a wani lokaci da ake kara samun yawaitar rikicin manoma da makiyaya a jihohin Arewa irin su Gombe, Bauchi, Benue, da Taraba.

Irin waɗannan rikice-rikice na ta’azzara lalacewar amfanin gona, salwantar rayuka da dukiyoyi, da kuma sakawa mutane tsoro musamman a karkara.

A kwanakin baya ma, jihar Bauchi ta warware wani rikicin manoma da makiyaya da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama kafin jami’an tsaro da shugabannin al’umma su shiga tsakani.

An kashe shanu kusan 300 a Benue

A wani rahoton, kun ji cewa wasu makiyaya sun yi korafi da cewa an kashe musu shanu kusan 300 a jihar Benue.

Makiyayan sun bukaci gwamnatin tarayya da ta jihar da su gaggauta daukar mataki game da irin abin da ke faruwa da su.

Kara karanta wannan

Abin da muka sani game da Oke, Are da Dalhatu, sababbin jakadu da Tinubu ya nada

Jihar Benue dai na cikin jihohin Arewa da ke shan fama sosai da matsalolin rashin tsaro, musamman tsakanin manoma da makiyaya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng