Tuna Baya: Sheikh Usman Dahiru Bauchi Ya Fadi Yadda Ya Rungumi Sufanci

Tuna Baya: Sheikh Usman Dahiru Bauchi Ya Fadi Yadda Ya Rungumi Sufanci

  • Bayan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi, an fara waiwaye a kan abubuwan da ya fada a kan rayuwarsa a lokacin da ya ke raye
  • Fitaccen malamin addinin Musulunci ya ce ya koyar da Alƙur’ani bisa tsarin Tijjaniyya, kuma su ne ginshiƙan rayuwarsa
  • Shahararren malamin ya ce babu abin da ya fi so a rayuwarsa fiye da haddar Alƙur’ani, zikiri da kuma aiki da koyarwar Tijjaniyya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi – A ranar 1 ga Agusta, 2022 wacce ta yi daidai da 2 ga Muharram, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya cika shekara 98 a doron kasa.

Marigayin, wanda ya rasu a ranar 26 ga Nuwamba, 2025, ya kasance ɗaya daga cikin fitattun malaman addinin Musulunci a Najeriya, kuma ginshiƙi wajen yada tsarin Tijjaniyya a Afrika.

Kara karanta wannan

Yadda jikin Shehu Dahiru Bauchi ya yi tsanani, aka tafi da shi asibiti ya rasu

Sheikh Usman Dahiru Bauchi ya bada tarihinsa kafin ya rasu
Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, fitaccen malamin Tijjaniya Hoto: Naziru Usman
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana cewa shi cikakken Bafulatani ne, daga ɓangaren iyayensa huɗu gaba ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rayuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi

A wata hira da Premier Radio ta wallafa a shafin Facebook, ya ce daga gidan mahaifinsa asalinsu Konkiyel ne a Darazo, Jihar Bauchi.

Ya kara da cewa a ɓangaren mahaifiyarsa ya fito daga Nafada, Jihar Gombe. An haife shi a watan Yuni 1927, ranar Laraba, 1 ga Muharram 1346H.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya fadi abin da ya fi so a rayuwarsa
Fitaccen malamin addinin Musulunci a Afrika, Sheikh Dahiru Usman Bauchi Hoto: Naziru Usman
Source: Facebook

A cikin hirar da aka tattauna da shi a Bauchi, ya ce tun yana ƙarami ya yi karatun allo karkashin mahaifinsa har ya haddace Alƙur’ani.

Daga nan mahaifinsa, Alhaji Usman ɗan Alhaji Adamu, ya ɗora shi kan tsarin Tijjaniyya, bayan shi ma ya gaji tsarin daga Alhaji Gwani Abba.

Koyarwar Sheikh Dahiru Bauchi

Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana cewa bayan haddace Alƙur’ani, Allah ya ba shi damar yin tafiyar neman ilimi a ƙasashe daban-daban.

Kara karanta wannan

Malamai da manyan ƴan siyasa da suka yi ta'aziyyar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi

Ya bayyana cewa wasu na kiran shi Gwani, wasu kuma Gangaran saboda fahimta da haddar Alƙur’ani. Ya ce daga shekarun 1950 ne ya fara gudanar da tafseer a bainar jama’a.

A lokacin da ya ke raye, Malamin ya bayyana cewa ya fara tafiye-tafiyen neman iliminsa bayan ya shiga cikin Failar Sheikh Ibrahim Inyass.

Sheikh Dahiru ya yi aure na farko a 1948, kuma ya ce ɗaya daga cikin ni’imomin da Allah ya yi masa shi ne yadda ’ya’yansa ke haddace Alƙur’ani tun suna ƙanana — wasu ma tun suna shekara bakwai.

A cewarsa, abin da ya fi burge shi a rayuwa shi ne yadda ya rungumi Alƙur’ani da rike ibada, zikiri nda Salatul Fatihi da sauransu.

Gwamnati ta karrama Dahiru Bauchi

Game da ilimin da ya fi kwarewa, ya ce yana da zurfin fahimta a Alƙur’ani da Tafseer, sannan Ma’arifa (Tarbiyya), Hadisi, Nahawu, Sarf da Fikihu.

A rayuwarsa, marigayi Sheikh Dahiru ya karɓi lambobin yabo da dama, ciki har da digirin girmamawa daga cikin gida da ƙasashen waje.

Sannan gwamnatin Najeriya ta taba karrama shi da kambar girmamawar ta OFR, ya rasu yana da shekaru sama da 100.

Kara karanta wannan

Abin da Malam Kabiru Gombe ya ce bayan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi

Tinubu ya yi ta'aziyyar Dahiru Bauchi

A baya, mun wallafa cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ta’aziyya kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi da ya cika a ranar Alhamis.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, inda ya ce Najeriya ta yi babban rashi.

A cewar sanarwar, Shugaba Tinubu ya nuna alhininsa kan labarin mutuwar jagoran Tijjaniyya, yana cewa marigayin ya rayu a matsayin tushen ilimi, nagarta, sadaukarwa da wa’azi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng