Kiristocin Jihohin Arewa 19 Sun Yi Magana kan Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi

Kiristocin Jihohin Arewa 19 Sun Yi Magana kan Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi

  • Kungiyar Kiristoci ta CAN ta bayyana mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin babban rashi ga kasa baki daya
  • Ta ce koyarwar malamin a tsawon shekaru ta jawo zaman lafiya, ladabi da mutunta juna tsakanin addinai
  • Kungiyar ta bukaci ’yan Najeriya su riƙe darussan zaman lafiya da marigayin ya bari domin kawo cigaba a kasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen jihohin Arewa 19 da Abuja ta bayyana bakin ciki kan rasuwar malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

A cewar kungiyar, marigayin ya kasance ɗaya daga cikin fitattun malamai da koyarwarsu ta samar da zaman lafiya, tawali’u da mutunta juna a tsakanin mabiya addinai daban-daban a Najeriya.

Shehu Dahiru Usman Bauchi
Shehu Dahiru Bauchi kafin rasuwarsa. Hoto: Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa shugaban kungiyar, Fasto Joseph Hayab ne ya bayyana hakan a wata sanarwar ta’aziyya da ya fitar daga Kaduna.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya fadi yadda ya rungumi Sufanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hayab ya yi magana yana mai cewa mutuwar malamin ta bar babban gibi ga harkokin zaman lafiya da tarbiyya, musamman a Arewacin ƙasar.

CAN ta yaba wa Sheikh Dahiru Bauchi

A cikin sanarwar, Hayab ya ce Sheikh Dahiru Bauchi ya shafe tsawon rayuwarsa yana ba da gudummawa wajen bunƙasa karatun Alƙur’ani.

Ya ce koyarwar malamin ta yi tasiri ga mutane, abin da ya taimaka wajen inganta zaman lafiya a Arewa.

Hayab ya bayyana cewa CAN na ganin marigayin a matsayin mutum mai hikima wanda ya yi amfani da tasirinsa wajen jawo hankalin mutane kan muhimmancin zaman tare.

Faston ya kara da cewa malamin ya yi kira da a yi watsi da rikici ko tayar da tarzoma a lokutan da ake fuskantar matsaloli a Arewa.

Ya ce irin rawar da malamin ya taka wajen kwantar da hankali da karfafa hakuri tsakanin al’ummomi ya kasance ginshiƙi mai muhimmanci wanda rashin sa ya haifar da babban gibi ga kasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Yadda jikin Shehu Dahiru Bauchi ya yi tsanani, aka tafi da shi asibiti ya rasu

Kiraye-kirayen wanzar da zumunci

Shugaban CAN ya ce ya kamata rasuwar malamin ta tunatar da ’yan Najeriya muhimmancin ƙarfafa zumunci, musamman a lokacin da ake fama da rikice-rikicen addini da rashin tsaro.

Ya ce kungiyar za ta ci gaba da tallafa wa duk wani yunkuri na wanzar da zaman lafiya da hada kan al’ummomi domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Marigayi Shehu Dahiru Usman Bauchi
Dahiru Bauchi yayin wata ziyara Saudiyya. Hoto: Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Source: Facebook

Hayab ya kara da cewa girmama marigayin da gaske shi ne ’yan Najeriya su dage wajen bin sawunsa ta hanyar inganta zaman lafiya, hakuri da fahimtar juna.

Dahiru Bauchi: CAN ta yi wa Tijjaniyya ta'aziyya

Kungiyar CAN ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, darikar Tijjaniyya, Masarautar Bauchi da al’ummar Musulmi a faɗin ƙasar.

Hayab ya jaddada bukatar Musulmi da Kiristoci su yi amfani da wannan lokaci wajen zurfafa tattaunawar addini da gina amana a tsakaninsu.

Sharif Saleh zai yi wa Dahiru Bauchi jana'iza

A wani labarin, kun ji cewa iyalan Sheikh Dahiru Usman Bauchi sun sanar da cewa za a masa jana'iza a yau Juma'a.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 19 sun hada kai, sun fitar da sanarwa kan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi

Rahotanni sun bayyana cewa Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Maiduguri ne zai yi wa marigayin sallar jana'iza.

Sakataren marigayin, Malam Baba Ahmad ne ya bayyana cewa Shehu Dahiru Bauchi ya yi wasiyyar Sheriff Saleh ya masa sallah.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng