Yan Bindiga Sun Harbe Matar da Ke Daukarsu Bidiyo yayin Hari kan Tsohon Gwamna

Yan Bindiga Sun Harbe Matar da Ke Daukarsu Bidiyo yayin Hari kan Tsohon Gwamna

  • Wata mata ta rasa rayuwarta bayan ‘yan bindiga sun harbe ta yayin da take ɗaukar bidiyon harin da aka kai wa tsohon minista
  • Maharan sun farmaki jerin gwanon motocin tsohon gwamnan Anambra, Chris Ngige a jihar wanda aka rasa rayuwa da dama
  • Ba a cikin jerin motocin yake ba lokacin harin, sai dai jami’an sa biyu sun ji rauni, yayin da rundunar tsaro ya ceto rayukansu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Awka, Anambra - Wata baiwar Allah da ba a gano sunanta ba ta mutu bayan harbin da aka yi mata lokacin da take ɗaukar bidiyo.

Matar ta rasa ranta ne a harin da ‘yan bindiga suka kai wa jerin gwanon motocin tsohon gwamnan Anambra, Chris Ngige.

Yan bindiga sun bindige mata da ke daukarsu bidiyo yayin hari
Taswirar jihar Anambra da ke shan fama da matsalar tsaro. Hoto: Legit.
Source: Original

Mata ta mutu yayin bidiyo a harin 'yan bindiga

Kara karanta wannan

Daga cacar baki, matasa sun caccaka wa babban dan sanda wuka, ya sheka lahira

The Cable ta ce maharan sun farmaki Ngige wanda kuma tsohon ministan kwadago ne a zamanin mulkin marigayi Muhammadu Buhari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fred Chukwuelobe, tsohon mai magana da yawun Ngige, ya ce ‘yan bindigan sun yi kwanton bauna ne ga jerin motocin a kan titin Nkpor–Nnobi da ke Jihar Anambra.

A cewarsa, lamarin ya faru ne a ranar Laraba 26 ga watan Nuwambar 2025 inda ya ce Ngige bai shiga cikin jerin motocin ba lokacin da hakan ya faru.

Ya ce an harbe wani ɗan sanda da ke cikin motar gaba, kuma maharan wadanda suka saka kayan sojoji da na ‘yan sanda sun kwace bindigarsa, cewar Vanguard.

“Abin takaici, wata mata da take ɗaukar bidiyon harbe-harben nan aka bindige ta har lahira.”
Mata ta mutu yayin daukar bidiyo a harin yan bindiga
Tsohon minista, Chris Ngige ya tsira daga harin da 'yan bindiga suka kai wa tawagarsa. Hoto: @SenNgige.
Source: Twitter

An kuma harbe mai shago yayin harin

Chukwuelobe ya ƙara da cewa wani mai shago da ya fito domin ganin abin da ke faruwa shima an harbe shi, ya zubar da jini sosai, kuma za a yi masa tiyata don cire harsasai, sai dai ya ce za a samu cikakkiyar kulawa.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun farmaki tawagar tsohon ministan Najeriya, an samu asarar rayuka

Ya bayyana cewa babu ɗan sandan da ya mutu, kuma sauran yan rakiyar Ngige da suka ji rauni sun riga sun samu kulawa domin har an yi musu tiyata, ana sa ran za su murmure.

“Mai shagon ya yi sa’a saboda harsashin bai makale a kashin bayansa ba wanda ya sa aka kai shi asibiti domin jinya.”

- Fred Chukwuelobe

Tsohon gwamnan ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya yi alhinin mutuwar matar da ta mutu tana bidiyo, tare da alƙawarin kula da wadanda suka ji raunuka domin samun cikakkiyar lafiya.

Kakakin ‘yan sandan Jihar Anambra, Ikenga Tochukwu, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an gano wata motar SUV kirar Mercedes-Benz farar fata da maharan suka kwace a lokacin harin.

Ngige ya fadi dalilin rasa kujerar gwamna

Mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan Anambra, Chris Ngige, ya bayyana dalilin cire shi daga mukaminsa na gwamnan Anambra.

Sanata Ngige ya ce an cire shi ne saboda ƙin naɗa Chris Uba a matsayin mataimakinsa kamar yadda aka bukata.

Tsohon ministan kwadagon ya ce ya fi son rasa kujerarsa fiye da bai wa Uba mataimaki, saboda zai iya cutar da shi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.