Malamai da Manyan Ƴan Siyasa da Suka Yi Ta'aziyyar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi
A ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamba, 2025 aka wayi gari da labarin rasuwar fitaccen malamin Tijjaniya, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Bauchi –Tun bayan samun labarin rasuwar Malamin, daruruwan jama'a da kungiyoyi suka fara bayyana alhini da irin girman rashin da duniyar Musulmi ta yi.

Source: Facebook
Legit ta tattaro wasu daga cikin wadanda suka mika ta'aziyyar rasuwar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi a wannan rahoto.
1. Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III
Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ƙarƙashin Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ta yi ta'aziyya kan rasuwar Sheikh Dahiru Buchi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Leadership ta ruwaito a sanarwa da sakataren JNI, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu ya fitar, kungiyar ta bayyana marigayin a matsayin fitilar shiriya.

Kara karanta wannan
Bayan birne shi a masallaci, Sheikh Abdullahi Pakistan ya yi magana kan Dahiru Bauchi

Source: Twitter
Kungiyar ta kuma ce Shehin ya yi tsayin daka a kan hidimar addini, inda ta ce wannan rashi babban gibi ne da ba zai cika ba.
JNI ta ce Sarkin Musulmi ya karbi abarin rasuwar marigayin cikin alhini mai taɓa zuciya da miƙa wuya ga ƙaddarar Allah SWT a yadda ya zo.
Kungiyar ta kara da cewa rasuwar Sheikh Bauchi ta kawo ƙarshen wata muhimmiyar kaka ta ilimi, kuma JNI na cikin bakin cikin wannan babban rashi.
2. Shugaban Kasa Bola Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana jimami kan rasuwar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, yana mai cewa labarin rasuwar ya sosa masa rai matuka.

Source: Facebook
A cikin sanarwar da Bayo Onanuga ya sanya wa hannu kuma aka wallafa a Facebook, Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin ma’aunin ɗabi’a wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa da wa’azi.
Ya ce rashin Sheikh Bauchi babban rashi ne ba ga iyalansa da mabiyansa kaɗai ba, har da kasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan
Allahu Akhbar: An yi jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi, an birne gawarsa a masallaci
Shugaban kasan ya tuna albarkar addu'o’i da goyon bayan da ya samu daga Sheikh Dahiru a lokacin shirye-shiryen zaben 2023.
3.Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana kaduwa da rashi, inda ya ce an yi babban babban rashi.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a shafin X, ya ce:
“Tsawon rayuwarsa mai albarka da tasiri, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya kasance fitila ta ilimin addinin Musulunci da shiriya madaidaiciya. Ta manyan makarantu da cibiyoyinsa na addini, da kuma tafsiran da ke tara dubban jama’a, ya gina al’ummomi tare da sahihin ilimin Musulunci, kyawawan ɗabi’u da ƙaunar Alƙur’ani da Sunnah.”
4. Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Tsohon Shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya nuna alhini kan rasuwar marigayin.

Source: Facebook
A shafin X ya rubuta cewa:
“A yau na samu labarin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi cikin tsananin baƙin ciki. A madadina, iyalina da dukkanin abokan siyasa na, ina mika ta'aziyyar ga iyalansa, dalibansa da kasa baki ɗaya. Allah Ya yi masa Aljanna.”
5. Sanata Shehu Sani
Tsohon Sanatan Kaduna, Shehu Sani, ya bayyana takaicin abin da ya kira babban rashi, tare da mika ta'aziyya.
A sakonsa a shafin X ya rubuta cewa:
"Ya kasance cikakken abin koyi a fannin ilimi, ruhaniya da imani. Malami ne fitacce wanda koyarwarsa ta haskaka zukatan miliyoyin mabiyansa… Za a yi rashinsa, amma ba za a taba mantawa da shi ba. Allah Ya ba shi Aljanna Firdausi. Amin.
6. Farfesa Isa Ali Pantami
Tsohon Ministan Sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami, ya nuna jimami kan rasuwar babban malamin.

Source: Facebook
Ya wallafa a Facebook cewa:
"Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji'un! Muna mika ta'aziyyar rasuwar babanmu, Shaykh Dahiru Usman Bauchi... Muna rokon Allah Ya yafe masa kura-kurensa, Ya sanya Aljannah ce makoma gare shi. Allah Ya bada ladan hakuri."
7. Aminu Waziri Tambuwal Tsohon
Tsohon gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana marigayin a matsayin jagora mai tsantsar basira da zaman lafiya.
A wani rubutu da ya yi a shafin X, ya ce:
“Sheikh Dahiru Bauchi ba malami ne kawai ba. Jagora ne, malami, mai gyaran al’umma, kuma mai haɗa kai… Gudummawarsa za ta ci gaba da kasancewa tubalan tunawa da shi a zukatanmu.”
8. Kungiyar gwamnonin Arewa
Gwamnonin Arewa 19 ƙarƙashin NSGF sun mika sakon ta'aziyya a madadin al’ummar Arewa.
Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe ya bayyana marigayin a matsayin malami mai zurfin ilimi da hikima, wanda ya yi tasiri wajen fahimtar Alƙur’ani.
Ya kafa da bayanan tasirin Malamin a bangaren fikihu da hadisi, inda ya shafe kusan karni guda yana hidima.
Sauran gwamnoni a daidaikunsu kamar na Bauchi, Katsina da Kaduna duk sun fitar da sakon ta'aziyya tun daga rana

Source: Facebook
Ya ce:
“Sheikh Dahiru Bauchi malami ne mai zurfin ilimi da tawali’u… Koyarwarsa ta haskaka rayuwar mutane da dama.”
9. Barau I Jibrin
Mataimakin Shugaban Majalisar dattawa, Barau I Jibrin ya bayyana kaduwarsa bayan samun labarin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Sanata Barau ya bayyana marigayin a matsayin tushen ilimi da jagora ga al’ummar Musulmi a Najeriya da ma duniya.
Sanata Barau ya ce mutuwar Sheikh Dahiru ta zo a wani lokaci da al’ummar Musulmi ke bukatar jagorori masu hangen nesa, masu iya shiryarwa da tsarkakakken ilimi irin nasa.
10. Bukola Saraki
Tsohon Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki na daga cikin na farko-farko da suka fara mika ta'aziyya bayan rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Ya bayyana rasuwar fitaccen malamin Musuluncin a matsayin babban rashi ga Najeriya, musamman al’ummar Musulmi.
11. Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi a matsayin babban rashi.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce bayyana marigayin a matsayin ginshiƙi na ilimi, zaman lafiya, tarbiyya.
Ya yi addu'ar Allah Ya sada Sheikh Dahiru Usman Bauchi da rahamar, tare da sanya shi a cikin aljanna madaukakiya.
Ana shirin birne Sheikh Ɗahiru Bauchi
A baya, mun wallafa cewa gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya ayyana ranar Juma’a, 28 ga Nuwamba, 2025 a matsayin ranar hutu.

Kara karanta wannan
Sarkin Musulmi ya yi nasiiha mai ratsa zuciya kan rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar a ranar Alhamis, 27 ga Nuwamba, 2025.
Sanarwar ta ce an bada hutun ne domin bai wa ma’aikata, dalibai da sauran mabiyan marigayi damar halartar jana’izar Jagoran Tijjaniyya cikin sauki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


