Gwamnoni 19 Sun Hada Kai, Sun Fitar da Sanarwa kan Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi

Gwamnoni 19 Sun Hada Kai, Sun Fitar da Sanarwa kan Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi

  • Kungiyar gwamnonin Arewa ta NSGF ta bayyana rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin babban rashi ga Musulmai
  • Shugaban kungiyar kuma gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya ya ce Shehun malamin ya shafe ƙarni yana yaɗa ilimin addini da raya Darikar Tijjaniyya
  • Gwamnonin Arewa su 19 sun yi addu’ar Allah Ya jikan fitaccen malamin kuma ya saka masa da Aljannatul Firdaus

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe, Nigeria - Gwamnonin jihohin Arewa 19 ƙarƙashin inuwar kungiyarsu ta NSGF sun bayyana alhini da jimamin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Kara karanta wannan

Sheikh Zakzaky ya fadi abin da ya ji kan rasuwar Shehu Dahiru Bauchi

Fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran Darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rasu ne da safiyar yau Alhamis a Bauchi.

Dahiru Bauchi da Inuwa Yahaya.
Babban shehun Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Bauchi tare da Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe Hoto: Ibrahim Misilli
Source: Facebook

Gwamnoni 19 na Arewa sun mika sakon ta'aziyya a wata sanarwa da shugaban kungiyarsu kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya fitar a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnoni sun tuna alheran malamin

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana marigayin a matsayin malami mai zurfin ilimi da hikima, wanda ya koyarwarsa ta amfani rayuwar miliyoyin mutane tsawon shekaru.

Ya ce Sheikh Dahiru Bauchi ya sadaukar da tsawon rayuwarsa ta kusan ƙarni guda wajen yaɗa ilimin Musulunci, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen zurfafa fahimtar Alƙur’ani mai girma da hadisai da fikihu.

“Sheikh Dahiru Bauchi malami ne mai zurfin ilimi da tawali’u. Kwarewarsa a cikin littattafan Musulunci, haɗe da basirarsa sun tabbatar da shi a matsayin jagora na gaskiya ga musulmi a Najeriya da wajen ta.

Kara karanta wannan

Bukola Saraki: "Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi babban rashi ne ga Musulmai

"Koyarwarsa ta haskaka rayukan mutane da dama, kuma za ta ci gaba da haskaka wa a tsawon shekaru da dama masu zuwa,” in ji Gwamnan.

Sheikh Dahiru Bauchi ya bada gudummuwa

Shugaban NSGF ya ƙara da cewa marigayi jagoran Tijjaniyya ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta zaman lafiya, haɗin kai, juriya da ɗabi’a ta gari har ƙarshen rayuwarsa.

“Gwagwarmayar da ya sha wajen gina ɗabi’a ta taimaka wajen tsara halayen mabiyansa, ‘ya’yansa da al’ummar Musulmi gaba ɗaya.
"Rayuwarsa ta kusan ƙarni guda shaida ce ta bauta wa Allah, hidima ga mutane, da kuma nagarta,” in ji shi.

Gwamnoni 19 sun mika sakon ta'aziyya

Gwamna Inuwa Yahaya ya miƙa sakon ta’aziyyar Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ga iyalan marigayin, mabiyan Tijjaniyya da dukkanin al’ummar Musulmi bisa wannan babban rashi.

Ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya ji kan fitaccen malamin, Ya ya sa mutuwa ta zama hutu a gare shi, Ya kuma saka masa da Aljannatul Firdaus saboda hidimar rayuwarsa.

Gwamna Inuwa Yahaya.
Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe Hoto: Muhammad Inuwa Yahaya
Source: Twitter

A rahoton Daily Trust, Gwamna Inuwa ya ce:

“Allah Madaukaki Ya ji kansa, Ya masa rahama mara yanke wa, Ya sanya shi a cikin gidan Aljannatul Firdaus bisa hidimar da ya yi wa addini da al’umma.”

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi, ya fadi alherin da ya yi masa

Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar Dahiru Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bi sahun manyan mutanen da suka mika sakon ta'aziyyarsu kan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi.

Tinubu ya yi juyayin rasuwar jagoran Tariqar Tijjaniyya, yana bayyana shi a matsayin tushe na nagarta wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa da wa’azi.

Shugaban kasan ya ce rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi babban gibi ne ba.ga iyalinsa da dimbin almajiransa kaɗai ba, har ma ga kasa baki ɗaya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262