Majalisa Ta Tsoma Baki da Jonathan Ya Makale a Kasar da Sojoji Suka Yi Juyin Mulki
- Majalisar Wakilai ta bukaci gwamnatin Najeriya ta fara bin matakan diflomasiyya domin dawo da Goodluck Jonathan gida
- Jonathan da sauran masu sa ido kan zaɓe sun makale a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar Laraba da ta shige
- Sojoji sun karɓi iko, sun dakatar da zaɓe, sun rufe iyakoki tare da kafa dokar hana fita da daddare a fadin kasar Guinea-Bissau
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - A jiya Laraba ne rundunar sojojin Guinea-Bissau ta tabbatar da karbe mulki tare da tsare shugaban kasa nan take.
Wannan juyin mulki da ya auku ya rutsa da tsohon shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan, wanda ya je sanya ido kan zaben shugaban kasa da 'yan majalisu a Guinea-Bissau.

Source: UGC
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Majalisar Wakilai ta shiga lamarin domin tabbatar da Jonathan ya dawo gida Najeriya cikin koshin lafiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisa ta bukaci a dawo da Jonathan
Majalisar ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta gaggauta amfani da diplomasiyya da duk wasu matakai domin tabbatar da dawo da tsohon Shugaba Jonathan daga Guinea-Bissau.
Wannan matakin ya biyo bayan amincewa da wani kudirin gaggawa da shugaban masu rinjaye, Farfesa Julius Ihonvbere, ya gabatar a zaman yau Alhamis.
Ihonvbere ya shaida wa Majalisar cewa Jonathan, wanda ya je Guinea-Bissau domin sa ido kan zaɓe, ya makale bayan sojoji sun karɓi iko.
Rahotanni sun nuna cewa tsohon shugaban ƙasar ya makale tare da sauran masu sa ido na ƙasashen waje, bayan Sojoji sun karɓi iko da yammacin Laraba.
Wane hali Jonathan ke ciki a kasar?
"A halin yanzu, yana Guinea-Bissau saboda juyin mulkin," in ji Ihonvbere, yana mai jaddada cewa duk da cewa Majalisa ba ta tattauna kan juyin mulkin ba, tsaron Jonathan "abu ne mai muhimmanci ga ƙasa."
Ya ƙara da cewa hukumomin gwamnati da abin ya shafa sun san da wannan ci gaba kuma sun riga sun ɗauki matakai don tabbatar da cewa Jonathan ya dawo lafiya.
Shugaban marasa rinjaye, Hon Kingsley Chinda ya goyi bayan wannan kira, yana mai jaddada cancantar Jonathan a fannin dimokuradiyya da kuma huldar da ke tsakaninsa da duniya baki daya.
Dan majalisar ya kuma lura cewa dole ne a ceto sauran 'yan Najeriya da juyin mulki ya rutsa da su ba tare da an yi watsi da su ba.

Source: Facebook
Matakin da Majalisar wakilai ta dauka
Daga nan, majalisar wakilai ta kasa ta amince da kudirin ta hanyar kada kuri'ar murya, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kara himma wajen kokarin diflomasiyya don sauwaka dawowar Jonathan da kuma fifita tsaron dukkan 'yan Najeriya da rikicin ya shafa.
Majalisa ta nemi a rage tsadar taki
A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar Wakilai ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta dauki mataki game da tsadar takin zamani da kayan noma a Najeriya.
Yayin zaman majalisa, Hon. Yusuf Galambi ya nuna damuwa game da tsadar takin zamani a kasuwa wanda ya ke jefa manoma cikin masifa da kuma asara mai tarin yawa.
Bayan tattake wuri, majalisar wakilai ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta rage farashin takin zamani da sauran kayan noma.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

