Bukola Saraki: "Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi ne ga Musulmai"
- Bukola Saraki ya bayyana alhini kan rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya bayyana a matsayin jagora a ilimin addinin Musulunci
- Tsohon shugaban majalisar dattawa ya yabawa malamin kan shekarun da ya sadaukar wajen koyar da Al-Kur’ani da Sunnah a fadin Najeriya
- Bukola Saraki ya mika ta’aziyya ga iyalai, Sarkin Musulmai, gwamnatin Bauchi, mabiya Tijjaniyya da dukkannin Musulmai, tare da yi masa addu'a
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin babban rashi ga Najeriya, musamman Musulmai.
A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis bayan ya samu labarin rasuwar Malamin, Bukola Saraki ya yi ta'azziyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Source: Twitter
A sakon, wanda ya wallafa a shafinsa na X, ya ce fitaccen malamin addinin jagora ne ga miliyoyin mutane.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bukola Saraki ya yi ta'aziyyar Dahiru Bauchi
Sanata Bukola Saraki ya bayyana cewa ya shiga matukar takaici da bakin ciki a lokacin da ya samu labarin rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi.
A cikin jawabin da ya fitar, Saraki ya ce:
“Inna lillahi wa inna ilayhi raji’un. Na shiga bakin ciki bayan na samu wannan labari. Sheikh Dahiru Usman Bauchi mutum ne mai tarbiyya, jagora na ruhaniya da uba ga miliyoyin Musulmai a Najeriya.”
Ya kara da cewa:
“Muna gode wa Allah (SWT) da Ya ba shi damar rayuwa mai albarka ta kusan shekara 100, wanda ya sadaukar gaba ɗaya wajen hidimar Allah da yada koyarwar Alkur’ani da Sunnah.”
Saraki ya tuno gudunmawar Dahiru Bauchi
Saraki ya bayyana cewa Sheikh Dahiru Bauchi ya kafa makarantu na almajirai da kuma gudanar da tafsiri wanda ya tabbatar da cewa ana koyar da littafin Allah SWT yadda ya dace.

Source: Facebook
Ya ce:
“Ta hanyar makarantu da zaman tafsirinsa, Sheikh Dahiru ya tabbata cewa umarnin Allah SWT sun zauna a zukatan matasa a fadin kasa."
Ya mika ta’aziyya ga iyalinsa, Sarkin Musulmai, gwamnatin Bauchi, mabiya Tijjaniyya da dukkannin Musulmai.
Ya kuma kara da addu’ar Allah Ya gafarta masa dukkannin kuskuren da ya yi a duniya, Ya jikansa, Ya kuma saka shi a cikin Al Jannah Firdaus.
Tsohon Shugaban majalisar ya kara da cewa:
“A yayin da muke makokin rasuwarsa, ina mika ta’aziyya ta musamman ga iyalinsa da al’umma baki ɗaya. Allah Ya gafarta masa, Ya jikansa, Ya kuma sanya ya huta cikin rahama."
Kwankwaso ya yi ta'aziyyar Sheikh Dahiru Bauchi
A wani labarin, mun ruwaito cewa Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana matuƙar bakin ciki bayan samun labarin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, inda ya ce an yi babban rashi.
Kwankwaso ya jaddada cewa Sheikh Dahiru Bauchi ya bar tarihi mai tarin darussa ga al’umma, musamman wajen tarbiyya, ilimi da zaman lafiya da ba za taba mantawa da shi ba.
A cewarsa, Sheikh Dahiru Bauchi ya kasance fitila ta ilimi da tarbiyya a Najeriya — malami ne da ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada Alƙur’ani, tafsiri da koyarwar addini yadda ya dace.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


