Kwankwaso Ya Tuno Gudunmawar Sheikh Dahiru Bauchi, Madugu Ya Yi Masa Addu'a

Kwankwaso Ya Tuno Gudunmawar Sheikh Dahiru Bauchi, Madugu Ya Yi Masa Addu'a

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana matukar bakin cikin game da rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
  • Ya ce marigayi malamin ya yi tasiri wajen tarbiyya, zaman lafiya da haɗa kan al’umma, kuma almajiransa da sauran al'umma ba za su manta da shi ba
  • Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kara da addu'ar Allah Ya sada babban malamin da rahamarSa, tare da ba shi aljanna madaukakiya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Jagoran jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana yadda ya ci karo da labarin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Ya bayyana cewa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, ya bar jama'a a cikin matukar takaici, amma dole a mika wuya ga hukuncin Allah SWT.

Kara karanta wannan

Bukola Saraki: "Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi babban rashi ne ga Musulmai

Kwankwaso ya yi takaicin rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
Sanata Rabi'u Musa Kwwankwaso, Sheikh Dahiru Usman Bauchi Hoto: @KwankwasoRM
Source: Twitter

A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Kwankwaso ya fara da tuno irin gudunmawar da malamin ya bayar wajen zaman lafiya a Najeriya.

Rabiu Kwankwaso ya yi ta'aziyyar Dahiru Bauchi

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kara da bayyana cewa jama'ar kasar nan ba za su taba mantawa da gudunmawar Sheikh Dahiru Usman Bauchi ba.

Ya fara da rubuta cewa:

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.”

Kwankwaso ya kara da cewa rasuwar malamin babban rashi ne saboda rawar gani da ya taka wajen koyarwa, gyaran halayya da wayar da kan al’umma a duk faɗin Najeriya.

Kwankwaso ya tuno halayyar Dahiru Bauchi

Kwankwaso ya bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin fitila ta ilimi da jagora mai gaskiya wanda darussansa suka karɓu a cikin al’umma.

Ya ce dubunnan mutane suna halartar tafsiransa a kowace shekara, kuma makarantu da cibiyoyinsa sun tallafa wa dalibai tun shekaru aru-aru.

Kara karanta wannan

Gwamnan Katsina ya fitar da sanarwa bayan saka lokacin jana'izar Dahiru Bauchi

A cewar Kwankwaso, Sheikh Dahiru Bauchi ba malami kaɗai ba ne, amma jigo ne, mai sasanci da haɗa kan al’umma.

Ya ce mutuwar malamin ta bar gibi mai faɗi musamman ga dalibansa, mabiya darikar Tijjaniyya da dukkan masu sauraron nasa a lokacin tafsiri.

Kwankwaso ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi addu'a
Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiri Bauchi Hoto: Naziru Usman Dahiru Bauchi
Source: Facebook

Kwankwaso ƙara da cewa marigayin ya rayu ne wajen ƙarfafa zaman lafiya da bin koyarwar Alƙur’ani da Sunnah, tare da tabbatar da cewa jama’a sun samu ingantaccen ilimi.

Ya miƙa ta’aziyya ga iyalan Sheikh Dahiru Bauchi, almajiransa da gwamnatin jihar Bauchi bisa wannan babban rashi.

Ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa, Ya yawaita masa rahama kuma Ya saka masa da Aljannar Firdausi.

Gwamna ya yi alhinin rasuwar Dahiru Bauchi

A baya, mun wallafa cewa Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi a matsayin babban rashi ga Katsina da Najeriya baki ɗaya.

Wannan jawabi na Gwamna Radda ya fito ne daga wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ibrahim Kaulaha Muhammad, yayin da Musulmi ke alhinin rasuwar fitaccen malamin.

Kara karanta wannan

Nasihar da Sheikh Dahiru Bauchi ya yi kan mutuwa kafin Allah ya karbi rayuwarsa

Sanarwar ta zo ne bayan gwamnatin Katsina ta kaddamar da sanarwar da ta tabbatar da cewa za a gudanar da jana’izar malamin gobe Juma’a, tare da addu'ar Allah Ya jikansa da rahama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng