"Mun San Su": Sanata Maidoki Ya Ba Gwamnati Zabi 2 kan Kawo Karshen 'Yan Bindiga

"Mun San Su": Sanata Maidoki Ya Ba Gwamnati Zabi 2 kan Kawo Karshen 'Yan Bindiga

  • Ana ci gaba da muhawara mai zafi kan yadda matsalar rashin tsaro ke kara tabarbarewa a sassa daban-daban na kasar nan
  • Sanata Garba Maidoki ya bayyana cewa hukumomi sun san inda 'yan bindiga suke da kuma abin da suke so a yi musu
  • Ya bukaci gwamnati ta zabi hanyar da za ta bi domin kawo karshen ayyukansu ta yadda jama'a za su zauna cikin kwanciyar hankali

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Sanata Garba Maidoki, mai wakiltar Kebbi ta Kudu, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.

Sanata Maidoki ya ce hukumomi sun san sunaye, wuraren zama, da kuma dalilan 'yan bindigan ke da alhakin garkuwa da mutane da suka yawaita a yankin Arewa a 'yan kwanankin nan.

Sanata Maidoki ya koka kan rashin tsaro
Sanata mai wakiltar Kebbi ta Kudu, Garba Maidoki Hoto: Sen Garba Musa Maidoki
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta ce Sanata Maidoki ya yi wannan bayani ne a zauren majalisar dattawa a ranar Laraba, 26 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace mai martaba sarki a jihar Kwara

Ya yi magana ne yayin tattaunawa kan halin tsaro da ke kara tabarbarewa a jihohin Kwara, Kebbi da Neja.

Me Sanata Maidoki ya ce kan ceto dalibai?

Sanatan ya bayyana cewa yana cikin murna da ɓacin rai a lokaci guda saboda sako ’yanmata 24 da aka sace a mazabarsa.

“Ina matuƙar farin ciki kuma a lokaci guda ina cikin damuwa. Ina farin ciki saboda ’yan mata 24 daga Maga da aka sace wadanda suka fito daga mazabata, dukkansu an sako su lafiya kuma ba a ci zarafinsu ba.”

- Sanata Garba Maidoki

Wace shawara Sanatan ya bada?

Sai dai ya yi tambaya kan dalilin da ya sa hare-hare ke ci gaba duk da cewa akwai tabbataccen bayanan sirri kan waɗanda ke aikata su.

“Mun san waɗanne ’yan bindiga ne. Mun san inda suke. Mun san abin da suke nema. To me ya rage mu yi? Idan tattaunawa za mu yi, a yi a gama. Idan yaki za mu yi, a yi shi har ya ƙare.”

Kara karanta wannan

Ngige: Ministan Buhari ya fadawa Obi yadda 'yan ta'adda suka bude masa wuta

- Sanata Garba Maidoki

Sanata Maidoki ya bukaci a yi bincike

Sanata Maidoki ya kuma nemi a gudanar da bincike kan zargin cewa an janye jami’an tsaro daga makarantar kafin harin ya faru, Sahara Reporters ta kawo labarin.

Sanata Maidoki ya bukaci ta yi sulhu ko ta yaki 'yan bindiga
Sanata Garba Maidoki mai wakiltar Kebbi ta Kudu Hoto: Sen Garba Musa Maidoki
Source: Facebook
“Babban abin da ya fi muhimmanci shi ne: wa ya bayar da umarnin janye sojojin daga makarantar Maga? Kuma a bisa umarnin wa? Duniya na son ta sani."
"’Yan Najeriya na son su sani. Mu da abin ya shafa kai tsaye muna son mu sani. Domin idan ba mu zurfafa bincike mun gano gaskiya ba, irin wannan abin zai sake maimaita kansa.”

- Sanata Garba Maidoki

Kabir Ibrahim ya shaidawa Legit Hausa cewa tabbas kalaman da sanatan ya yi abin dubawa ne.

Ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a san abin yi kan matsalar rashin tsaro domin ba zai yiwu a ci gaba da tafiya haka ba.

"Tabbas ya kamata a san abin yi, idan sulhu za a yi ko yakarsu za a yi. Matsalar nan ta wuce inda ake tunani. Mutane na ta rasa rayukansu ba gaira ba dalili."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta biya kudin fansa kafin ceto 'daliban Kebbi? Majalisa ta yi bayani

"Ni na fi son a kawo karshensi ta hanyar yaki domin ko an yi sulhu da su, saba alkawari suke yi."

- Kabir Ibrahim

Gwamna ya ba daliban Kebbi shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yi nasiha ga daliban makarantar Maga da 'yan bindiga suka sace.

Gwamna Nasir ya bukace su da su dauki abin da ya faru da su a matsayin wani kalubale na rayuwa.

Hakazalika, ya ba su shawarar da ka da su bari sace su da 'yan bindiga suka yi, ya sanya su hakura da ci gaba da neman ilmi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng