Gwamnan Katsina Ya Fitar da Sanarwa bayan Saka Lokacin Jana'izar Dahiru Bauchi

Gwamnan Katsina Ya Fitar da Sanarwa bayan Saka Lokacin Jana'izar Dahiru Bauchi

  • Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi a matsayin babban rashi ga Najeriya
  • Dikko Umaru Radda ya ce marigayin ya kasance ginshiƙin zaman lafiya, fahimtar addini da haɗin kai tsakanin al’umma
  • Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayi Dahiru Usman Bauchi tare da ba iyalansa da mabiyansa haƙurin jure rashin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana alhini game da rasuwar jagoran darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Gwamna Radda ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai tarbiyya, nagarta da hangen nesa, wanda ya kasance abin koyi ga miliyoyin mutane a fadin kasar.

Dikko Umaru Radda, Dahiru Usman Bauchi
Gwamna Radda da marigayi Shehu Dahiru Bauchi. Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Maganar gwamna Radda ta fito ne daga sanarwar da mai magana da yawunsa, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Bukola Saraki: "Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi babban rashi ne ga Musulmai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Katsina ta fitar da sanarwar ne jima kadan bayan sanar da cewa za a yi jana'izar malamin a gobe Juma'a.

Gwamna Radda ya yi ta'aziyyar Dahiru Bauchi

A cikin sakonsa, Gwamna Radda ya jaddada cewa Sheikh Dahiru Usman Bauchi uba ne ga al’umma kuma jagora mai haɗa kan jama’a daga kowane yanki na ƙasar nan.

Ya ce rayuwar malamin ta kasance misali ta koyarwar Musulunci, musamman wajen karantar da tausayi, haƙuri, fahimtar juna da hidima ga al’umma.

Gwamnan ya ce a tsawon shekaru kusan 100 da malamin ya rayu, ya kasance muryar fadin gaskiya da yada kwanciyar hankali, kuma ginshiƙi wajen jan hankalin mutane su yi rayuwa ta gari.

Marigayi Dahiru Usman Bauchi
Sheikh Dahiru Usman Bauchi kafin ya rasu. Hoto: Naziru Usman Dahiru Bauchi
Source: Facebook

Ya yi nuni da cewa marigayin ya kasance madogara ga dimbin musulmai waɗanda ke dogaro da shawarwari da karatuttukansa a wajen gudanar da al’amuransu.

Haka kuma, Gwamna Radda ya tuna rawar da Sheikh Dahiru ya taka wajen inganta zaman lafiya a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi, ya fadi alherin da ya yi masa

Ya bayyana yadda wannan kokari nasa ya taimaka wajen rage tashin hankali da inganta rayuwar zamantakewa a tsakanin al’umma masu bambancin fahimta da ra’ayi.

Radda ya yi wa mutanen Bauchi ta'aziyya

Gwamnan Katsina ya yi ta’aziyya ga gwamnan jihar Bauchi, al’ummar jihar, da kuma darikar Tijjaniyya baki ɗaya bisa wannan rashi da ya kira mai girma sosai.

Ya ce irin gudummawar da marigayin ya bari za ta ci gaba da zama abin alfahari ga Darika da kuma ga al’ummar Musulmi.

Dikko Radda ya roƙi Allah madaukakin sarki ya gafarta wa marigayin tare da ba shi Aljannal Firdausi mai daraja.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya bai wa iyalan Sheikh Dahiru Usman, mabiyansa da masoyansa juriya da ƙarfin hali wajen jure wannan babban rashi.

Bala Mohammed ya yi ta'aziyyar Dahiru Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Bauchi ta fitar da sanarwa game da rasuwar Shehu Dahiru Usman Bauchi.

Gwamna Bala Albdulkadir Mohammed ya nuna matukar damuwa game da rasuwar malamin da ya ce ya shafe shekaru yana karantarwa.

Kara karanta wannan

Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta girgiza Sanata Barau, ya fadi yadda ya ji

Haka zalika ya roki Allah ya ba iyalan marigayin hakurin rashi tare da rokon Allah ya gafarta masa ya sanya shi a Aljanna.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng