Tsohon Gwamnan da ake Zargi da Yunkurin Kifar da Gwamnatin Tinubu zai Kai Kansa EFCC

Tsohon Gwamnan da ake Zargi da Yunkurin Kifar da Gwamnatin Tinubu zai Kai Kansa EFCC

  • Tsohon ministan mai, Timipre Sylva, ya rubuta wa EFCC wasika yana neman a saka masa ranar bayyanarsa a gaban hukumar
  • Ya yi zargin cewa an ayyana shi a matsayin wanda ake nema ba tare da gayyata ta gaba ba, duk da cewa yana cikin jinya mai tsanani
  • Timipre Sylva ya ce abubuwan da suka faru cikin makonnin da suka wuce sun jefa shi da iyalinsa cikin tashin hankali da abin mamaki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon karamin ministan man fetur, kuma tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Cif Timipre Sylva, ya rubuta wasika ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC.

Ya aika wasikar ga EFCC yana rokon a saka masa ranar da zai bayyana gaban hukumar domin amsa tambayoyi game da zarge-zargen da aka yi masa.

Kara karanta wannan

Kaduna: Limamin addini ya mutu a hannun 'yan ta'adda kafin a biya kudin fansa

Tsohon gwamnan Bayelsa ya bayyana cewa zai je EFCC
Tsohon gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva Hoto: Timipre Sylva
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa wannan na zuwa ne bayan da hukumar ta ayyana shi wanda ake nema bisa zargin almundahanar $14.8m.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon minista zai je EFCC

The Nation ta ruwaito cewa a cikin takardar da ya sanya hannu kansa, wacce aka rubuta ranar 24 ga Nuwamba, ta isa hannun hukumar EFCC ranar 26 ga watan.

Timipre Sylva ya ce yana karɓar magani a kan wata mummunar rashin lafiya wadda ke bukatar kulawa ta gaggawa.

EFCC ta zargi Timipre Sylva da badakala
Shugaban hukumar yaki da cin hanci, EFCC Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Source: Facebook

Ya ce yana tattaunawa da likitocinsa kan yiwuwar dakatar da maganin na ɗan lokaci domin ya samu damar zuwa ofishin EFCC idan yanayin lafiyarsa ya ba shi damar hakan.

Sylva ya ce abubuwan da suka faru cikin makonnin da suka gabata sun girgiza shi da iyalinsa inda aka rika lakanta shi da matsalar badakala.

Timipre Sylva ya musanta zargin EFCC

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa lamarin ya fara ne da wani zargi mara tabbas da ya danganta shi da wani yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Atiku: "Ba a taba jam'iyyar da ta azabtar da 'yan Najeriya kamar APC ba"

Ya kara da cewa, duk da wannan tashin hankali, sai ga shi ranar 10 ga Nuwamba 2025 an ayyana shi wanda ake nema kan zargin almundahanar $24.8m.

Tsohon ministan ya bayyana cewa EFCC ta riga ta gayyace shi tun watan Disamba 2024, inda ya bada bayanai kuma ya samu beli.

Sylva ya ce ya yi mamakin jin cewa wai ya yi gudun beli, alhali babu wata ka'ida da ya karya, ya tabbatar da cewa yana bin doka yadda ya dace.

Ana zargin tsohon gwamna da shirin juyin mulki

A wani labarin, mun wallafa cewa wasu majiyoyi sun bayyana cewa wani tsohon gwamna daga Kudancin Najeriya na karkashin binciken hukumomin tsaro bisa zargin shirin juyin mulki.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun kama hafsoshi 16 na rundunar sojin Najeriya, wadanda ake zargin sun jagoranci wani shiri na kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Tsohon gwamnan na daga cikin mutanen da ake zargin sun bayar da tallafin kudi domin ganin shirin ya tabbata, inda ake zargin an tsara gudanar da juyin mulkin ne a ranar 25 ga Oktoba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng