Kaduna: Limamin Addini Ya Mutu a Hannun 'Yan Ta'adda kafin a Biya Kudin Fansa
- Limamin Cocin Anglican na Ungwan Maijero, Ven. Edwin Achi, ya gamu da ajalinsa a hannun masu garkuwa da mutane suka sace shi
- Kungiyar kiristoci ta CAN ta tabbatar da mutuwar jagoran, yayin da matarsa da ’yarsa ke hannun masu garkuwa da mutane har yanzu
- Lamarin ya faru ne a lokacin da Najeriya ke fama da matsanancin rashin tsaro, har ta kai ga Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Kiristoci a Kaduna sun shiga cikin wani mawuyacin hali bayan tabbatar da mutuwar Venerable Edwin Achi, Limamin Cocin Ebenezer Anglican, Ungwan Maijero.
Achi, wanda aka sace tare da matarsa da ’yarsa a Nissi, a karamar hukumar Chikun ranar 28 ga Oktoba 2025, ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane.

Source: Original
Wata majiya ta tabbatarwa Daily Trust faruwar lamarin ba tare da bayani dalla-dalla ba, sannan kungiyar kiristoci ma ta tabbatar da lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fasto ya mutu a hannun 'yan ta'adda
Daily Post ta wallafa cewa amma Reverend Joseph John Hayab, shugaban CAN na jihohin Arewa 19 da Abuja, ya tabbatar da wannan labari.
Ya bayyana cewa:
“(Kashe faston) Gaskiya ce mai ban takaici ga cocinmu da danginsa."
Dangin Achi sun koma kauyen Nissi ne kwanaki kadan kafin mahara su kai hari suka yi awon gaba da su.

Source: Twitter
Bayan sace jagoran kiristocin ne 'yan ta'addan suka nemi a biya su kudin fansa na N600m kafin sake su.
Achi ya fito daga Umuaja, a Karamar Hukumar Ukwuani ta Jihar Delta, kuma ya shafe shekaru yana hidimtawa coci.
Kungiyar CAN ta yi tir da kashe Fasto
A cikin wata sanarwa, Darikar Anglican ta Kaduna ta bayyana mutuwarsa da cewa babban rashi ne ga cocin ga duk wanda ya amfana da aikinsa.
Mutuwar Achi ta zo ne a wani lokaci da Najeriya ke fuskantar hare-haren ’yan bindiga, satar mutane da ta’addanci.
A ranar Laraba, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan batun tsaro, ya kuma umarci ’yan sanda da sojoji su fara daukar jami’ai da yawa don ƙarfafa rundunonin tsaro.
Tinubu ya kuma umarci DSS ta bazama da dakaru na masu gadin daji domin fatattakar ’yan ta’adda da ’yan bindiga da ke fakewa a karkara.
Shugaban ƙasar ya roki Majalisar Dokoki ta fara duba dokoki domin bai wa jihohi damar kafa rundunar ’yan sandan jiha idan suka ga bukata.
An kubutar da 'yan ta'adda a Kaduna
A baya, mun wallafa cewa gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa ta samu nasarar kubutar da mutane fiye da 500 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na jihar.
Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ahmed Maiyaki, ne ya bayyana haka yayin taron “aikin jarida a bangaren zaman lafiya” da aka gudanar a Kaduna domin karin haske a kan batun.
A cewarsa, nasarar ta samo asali ne daga sabon tsarin samar da zaman lafiya da gwamnatin Uba Sani ta ƙirƙira, wanda ya haɗa da haɗin gwiwa da gwamnatin tarayya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


