Shugaba a Izala, Jalo Jalingo Ya Yi Ta'aziyyar Rasuwar Shehu Dahiru Bauchi

Shugaba a Izala, Jalo Jalingo Ya Yi Ta'aziyyar Rasuwar Shehu Dahiru Bauchi

  • Shugaban malaman Izala, Dr Ibrahim Jalo Jalingo, ya yi ta’aziyya ga iyalan Sheikh Dahiru Usman Bauchi bisa rasuwar malamin
  • Binciken Legit Hausa ya gano cewa rubutun Dr Jalo ya jawo martani daga jama’a da dama da suka yi addu’a da ta’aziyya
  • Mutane da dama sun bayyana irin gudummawar da Sheikh Dahiru Bauchi ya bayar tare da roƙon Allah ya jikansa da rahama

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Taraba - Shugaban malaman kungiyar Izala, Dr Ibrahim Jalo Jalingo, ya gabatar da ta’aziyya ga iyalan Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Dr Jalo Jalingo ya yi magana ne bayan labarin rasuwar fitaccen malamin da ya karade kafafen sada zumunta.

Sheikh Dahiru Bauchi da Dr Jalo Jalingo
Shugaban Malaman Izala, Dr Jalo da marigayi Sheikh Dahiru Bauchi. Hoto: Ibrahim Jalo Jalingo|Naziru Dahiru Usman
Source: Facebook

Shugaban malaman kungiyar Izala, Dr Jalo Jalingo ya yi magana ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Bukola Saraki: "Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi babban rashi ne ga Musulmai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan rubutun Dr Jalo da ya fito a safiyar Alhamis, mutane daga sassa daban-daban sun shiga bayyana alhini kan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi.

Ta’aziyyar Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

A cikin rubutunsa, Dr Jalo Jalingo ya ce su na gabatar da sakon ta’aziyya ga iyalan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda Allah ya yi masa rasuwa.

Dr Jalo ya roki Allah ya yafe masa kurakuransa:

"Muna gabatar da ta'aziyyarmu ga iyalan Sheikh Ɗahiru Uthman Bauchi wanda Allah Ya yi masa rasuwa a safiyar Alhamis ɗin nan. Allah Ya yafe masa kurakuransa."

Mutane da dama sun nuna godiya da jin dadi kan irin yadda Dr Jalo ya fitar da sakon ta'aziyyar a karkashin rubutun da ya yi.

Martanin jama’a bayan sakon Jalo Jalingo

Rubutun Dr Jalo ya jawo martani da yawa daga mabiyansa da sauran jama’a masu amfani da kafar Facebook.

Daga cikin masu magana, Hon Atiku Iliya ya bayyana rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin “Zamani guda da ya shude."

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi, ya fadi alherin da ya yi masa

Hon. Iliya ya yi doguwar addu’a ga marigayin, yana roƙon Allah Ya gafarta masa, Ya haskaka kabarinsa, Ya kuma ba makusantansa haƙurin jure rashi.

Dahiru Usman Bauchi da wani dansa.
Sheikh Dahiru Bauchi tare da wani dan shi. Hoto: Naziru Dahiru Bauchi
Source: Facebook

Cikin masu jimami, Sanusi Aliyu ya yi addu’a yana cewa Allah ya jikan Shehu Dahiru Bauchi da rahama.

Ya ce:

"Muna rokon Allah ya masa rahama."

Musa Hassan ya bayyana cewa babu abin da za a faɗa sai abin da Allah ya yi, yana mai karɓar abin da ya faru cikin haƙuri da tawakkali.

A nasa bangaren, Abubakar Mustapha ya ce Sheikh Dahiru ya yi rayuwa mai tsawo kuma cike da albarka da amfani:

"Ina roƙon Allah Ya gafarta masa, Ya haɗa shi da Annabi Muhammad (SAW). Wannan rashi ne babba ga al’umma."

'Yan Tijjaniyya sun ziyarci jihar Yobe

A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu shugabannin Darikar Tijjaniyya sun gana da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni.

Babban dan Dahiru Bauchi, Ibrahim ne ya jagoranci tawagar da zuwa gidan gwamnatin Yobe da wasu wurare a jihar.

Ibrahim Dahiru Bauchi ya bayyana cewa za su cigaba da addu'o'i domin kara samun zaman lafiya a Yobe da Najeriya baki daya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng