Gwamna Bala Ya Yi Magana kan Rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi a Asibiti

Gwamna Bala Ya Yi Magana kan Rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi a Asibiti

  • Babban malamin Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rasu ranar 27 ga Nuwamba, 2025 a wani asibiti a cikin garin Bauchi
  • Gwamna Bala Mohammed ya aika da sakon ta’aziyya a madadin gwamnatin Bauchi zuwa ga iyalansa, almajiransa da musulmin duniya
  • Ya ce marigayin babban malami ne da ya shahara wajen koyar da Alkur'ani, kuma ya ba da gudunmawa ga ilimin addinin Musulunci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya bayyana alhini bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Iyalan Shehin Malamin sun tabbatar da cewa ya rasu a safiyar Alhamis, 27 Nuwamba 2025 a wani asibiti a cikin garin Bauchi.

Gwamna Bala Mohammed.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Twitter

Gwamna Bala ya mika sakon ta'aziyya a wata sanarwar da ya wallafa a Facebook mai dauke da sa hannun Mai taimaka masa kan yada labarai, Mukhtar Gidado.

Kara karanta wannan

Shehin Darikar Tijjaniyya, Dahiru Usman Bauchi ya rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya sanar da rasuwar Dahiru Bauchi

Gwamnan ya mika sakon ta’aziyya a madadin iyalinsa, gwamnatin jihar Bauchi da al’ummar jihar, ga iyalan marigayin, almajiransa, mabiyansa da daukacin al’ummar Musulmi a Najeriya da ma kasashen waje.

Bala Mohammed ya ce:

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Cikin alhini da juyayi muke sanar da rasuwar fitaccen malamin addini, jagora kuma malamin Qur’ani, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya koma ga Mahaliccinsa a safiyar yau.”

Gwamna Bala ya tuna alheran malamin

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana marigayin a matsayin babban malami a fagen ilimin addinin Musulunci, wanda ya shahara da kamala, tawali’u, tsantseni da hikima,

Ya kuma kara da cewa Sheikh Dahiru Bauchi ya sadaukar da rayuwarsa gaba ɗaya wajen yaɗa addini da koyar da Alƙur’ani.

Ya ce darussan da ya gudanar a wuri daban-daban da tsangayoyinsa sun tara ɗaruruwan almajirai waɗanda suka haddace Qur’ani tare da yada ilimin Musulunci a Nahiyar Afirka baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Shawarar da Gwamna Nasir ya ba daliban da 'yan bindiga suka saki a Kebbi

Gwamnan ya kara da cewa ba za a taba manta da irin gudunmawar Sheikh Dahiru ya bayar a wajen Tafsirin Alkur'ani, Fiƙhu da daukaka addinin musulunci ba.

“Ya kasance jagora mai haɗa kai, zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin Musulmai da ma mabambantan addinai," in ji shi.
Gwamna Bala Mohammed.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi da Gwamna Bala Mohammed Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed
Source: Facebook

Gwamna Bala ya sha alwashin cewa gwamnatin Bauchi za ta ci gaba da girmama ilimi da tarbiyyar da Sheikh Dahiru Bauchi ya bari musamman wajen tallafawa addinin musulunci.

A ƙarshe ya yi addu’ar cewa:

“Allah Ya gafarta masa, Ya karɓe shi cikin rahama, ya ba iyalansa, almajiransa da daukacin al’ummar Musulmi haƙurin jure wannan babban rashi. Allah Ya saka masa da Aljannatul Firdaus. Ameen.”

Matsayar Dahiru Bauchi kan ganin Inyass

A wani rahoton, kun ji cewa Sayyid Ibrahim ya ce Sheikh Dahiru Bauchi bai yarda da masu cewa sun ga Shehu Inyass a bango ko bishiya ba.

'Dan Sheikh Dahiru Usman Bauchi , ya bayyana cewa mahaifinsa bai yada da akidar da ke cewa ana ganin Shehu Ibrahim Inyass a wurare daban-daban ba.

Malamin ya ce irin wannan magana yaudara ce da wasu ke amfani da ita don cutar da mutane, kuma ba gaskiya ba ce a addini.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262