Yadda Shekau Ya Yi Jinya a Kano, Ya Boye Lokacin ana Fama da Yakin Boko Haram

Yadda Shekau Ya Yi Jinya a Kano, Ya Boye Lokacin ana Fama da Yakin Boko Haram

  • Bayanai sun fito a kan rayuwar fitinannen ɗan ta'addan Boko Haram, Abubakar Shekau wanda ya mutu a 2021
  • Rahotanni sun ce Shekau ya ɓoye a Kano bayan wani harin a 2009, inda aka harbe shi a cinyarsa, ya yi jinya a asibiti a jihar
  • Duk da bama-baman da Boko Haram suka rika tayarwa a jihohin Arewa da Abuja, Shekau ya cigaba watayawa a Kano

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Rahotanni sun bayyana yadda fitinannen ɗan ta'addan Boko Haram, Abubakar Shekau ya rayu na tsawon lokaci a Kano duk da ana nemansa ruwa a jallo.

Shekau, ya yi basaja inda ya ɓoye a Kano bayan wani hari a shekarar 2009, kuma ya yi jinya da sunan ƙarya Alhaji Garba.

Kara karanta wannan

Abu ya gagara: Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta baci kan matsalar tsaron Najeriya

Shekau ya shafe tsawon lokaci yana zaune a Kano
Abubakar Shekau, kasurgumin ɗan ta'addan da ya addabi Najeriya Hoto: @BenHopper
Source: Twitter

A labarin rayuwa da mutuwar shahararren ɗan ta'addan, Human Angle ta ruwaito cewa Shekau ya cigaba da rayuwa a cikin jama’a yana tserewa jami'an tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Abubakar Shekau ya ɓoye a Kano

Rahoton ya ce bayan harin dare da ya auku a Hedikwatar ’yan Sanda a ranar 27 ga Yuli, 2009, inda aka harbe shi a cinyarsa, Abubakar Shekau ya ɓace daga idon jama’a.

Ƴan ta'addan sun yi jigilar Shekau daga Maiduguri aka kai shi Kano, inda aka kwantar da shi a ƙashi na Dala.

Ya yi watanni yana jinya kafin ya koma wani gidan haya a yankin Rijiyan Zaki cikin birnin Kano, a nan ya ci gaba da rayuwa kamar mutumin kwarai.

A nan ne ya ɗauki sabon suna, Alhaji Garba, domin ya ɓoye asalin na kasurgumin ɗan ta'addan da ya ɓarnatar da rayuka daga maƙwabtansa.

Rayuwarsa ta kasance tsattsauran ra’ayi kamar yadda akidarsa take. Bayan rasuwar matarsa ta farko, ya sake aurene wata Hajara, ’yar’uwar ɗaya daga cikin matan Mohammed Yusuf.

Kara karanta wannan

An fara cika umarnin Tinubu game da janye 'yan sanda daga tsaron manyan mutane

Shekau ya koma jihar Borno, ya wuce dajin Sambisa
Taswirar jihar Borno, jihar da Abubakar Shekau ya kashe kansa Hoto: Legit.ng
Source: Original

Zuwa lokacin tashin Boko Haram a 2009, Shekau ya kasance da mata biyu, Yana da Hajara.

Bayan kashe Mohammed Yusuf, sai ya aure ɗaya daga cikin matansa, Hajja Gana, a matsayin mata ta uku.

Zuwa 2011, har yanzu yana zaune a Rijiyan Zaki, ya ƙara aure – Fatima daga Potiskum a Jihar Yobe, wato ya cike mata hudu cif.

Abubakar Shekau ya wataya a Kano

Duk da fashe-fashen bama-bamai a Hedikwatar ’Yan Sanda, UN House, gidajen jaridu, masallatai da coci-coci a Abuja da Arewa, shi kuma yana shawagi a kan manyan titunan Kano.

Shekau, ko kuma Alhaji Garba kamar yadda ya kira kansa, yana shiga gidajen abinci, har ma yana gaisawa a shingen binciken jami'an tsaro.

Sau da dama yana yawo a cikin babbar mota irin SUV, wani lokaci kuma cikin tsohuwar Golf ba tare da ya fuskanci wata matsala ba.

Da aka fara ƙoƙarin cafke shi a faɗin ƙasar, sai ya arce daga Kano zuwa Maiduguri, daga nan zuwa Bama – garin da ya mamaye – sannan ya bace cikin dajin Sambisa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ci karo da maɓoyar ƴan ta'adda a laluben ɗaliban da aka sace

Ya tafi da matansa huɗu da ’ya’yansa da dama. Mutuwar Mohammed Yusuf da daruruwan ƴan ƙungiyar da aka kashe ya buɗe sabon babi na ta’addanci ƙarƙashin Shekau.

Amma da ƙarshensa ya zo, kamar yadda ISWAP ta fitar, Shekau ya mutu tsakanin 18–19 ga watan Mayu 2021.

Rahotanni daga irinsu BBC sun nuna cewa ya tayar da abin fashewa da kansa yayin da aka cin masa a jeji.

Ƴan ta'adda sun kai hari Kano

A baya, mun wallafa cewa mazauna ƙaramar hukumar Rimin Gado sun kwana cikin firgici bayan wani hari da aka yi da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai a kauyen Gulu

Amma, a cewar tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da karɓar korafe‑korafe na jihar, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, maharan ba ‘yan ta’adda bane.

Wani mazaunin yankin, Hamza Haruna Gulu, ya ce maharan — kimanin huɗu zuwa shida — sun iso kauyen ne da 8.00 na dare tare da shiga shagon wani bawan Allah.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng