Abu Ya Gagara: Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta Baci kan Matsalar Tsaron Najeriya
- Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan tsaro a fadin Najeriya, matakin da ake ganin zai kawo karshen duk wani nau'in ta'addanci
- Mai girma shugaban kasar ya amince a dauki karin jami’an runsunar soji da ’yan sanda 20,000 domin karfafa yaki da yan ta'adda
- Ya kuma umarci hukumar DSS ta gaggauta tura dakarun rundunar tsaron daji da aka kammala bai wa horo domin zakulo duk wani bara gurbi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Laraba, ya ayyana dokar ta-baci kan tsaro a fadin ƙasar nan.
Mai girma Tinubu ya bada umarnin a dauki karin jami’an ’yan sanda da sojoji, domin dakile ta’addanci, ’yan bindiga da kuma karuwar sace-sacen mutane.

Source: Twitter
Hakan na kunshe a wata sanarwa da Shugaban kasa ya sanya hannu da kansa da hadiminsa, Dada Olusegun ya wallafa a X yau Laraba, 26 ga watan Nuwamba, 2025.

Kara karanta wannan
"Mutane suna da mantuwa," Sheikh Gumi ya yi magana kan zargin goyon bayan 'yan bindiga
Tinubu ya amince a dauki 'yan sanda, sojoji
Ya ba da umarnin a dauki karin 'yan sanda 20,000, wanda zai kai yawan sababbin jami’an da ake shirin dauka don tunkarar matsalar tsaro da su zuwa 50,000.
A wani mataki na murkushe ’yan ta’adda a dazuzzukan Najeriya, Tinubu ya umarci DSS da ta gaggauta tura dakarun tsaron daji da aka riga aka horas, domin zakulo ’yan ta’adda da ’yan bindiga da ke ɓoye.
“Ba za mu sake yarda da wata maboya ga miyagu ba,” in ji Tinubu.
Shugaban kasar ya kuma umurci hukumar DSS da ta dauki karin ma’aikata domin cika dazuzzuka da jami’an tsaro.
Tinubu ya goyi bayan kafa 'yan sandan jihohi
Ya kuma jaddada cewa yana goyon bayan Majalisar Dokoki wajen samar da dokar kafa rundunar ’yan sanda ta jihohi, domin ƙara ƙarfin tsaro a matakin ƙasa.
Tinubu ya tunatar da cewa kafa Ma’aikatar Raya Kiwo da ya yi a bara na daga cikin matakin da zai kawo karshen rikicin makiyaya da manoma, musamman a Arewa ta Tsakiya.
Shugaban kasa ya ce wannan lokaci ne da ake buƙatar haɗin kan kowa da kowa domin kare kasa daga miyagun 'yan ta'adda.
A cikin sanarwarsa ya ce:
“Wannan gaggawa ce ta ƙasa. Za mu tura ƙarin jami’an tsaro, musamman a yankunan da ke fama da matsaloli.”

Source: Twitter
Bola Tinubu ya jinjinawa rundunonin tsaro bisa aikin ceto dalibai mata 24 na Jihar Kebbi da masu ibada 38 da aka sace a Kwara.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati na ƙoƙarin ceto ragowar daliban Makarantar Katolika ta Jihar Neja da sauran ’yan Najeriya da ke hannun miyagu.
Tinubu ya nada jakadun Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Bola Tinubu ya aika da sunayen mutanen da yake so ya nada a matsayin jakadun Najeriya ga majalisar dattawa.
Wannan nadi na jadakun da za su wakilci Najeriya a kasashen ketare da Tinubu ya yi ya zo ne bayan fiye da shekaru biyu da kafa gwamnati.
Shugaba Tinubu ya aika da jerin sunayen mutane uku da ya zaɓa domin nada su a matsayin jakadu, domin majalisar dattawa ta tantance kuma ta tabbatar da su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
