Abin da Muka Sani game da Oke, Are da Dalhatu, Sababbin Jakadu da Tinubu Ya Nada

Abin da Muka Sani game da Oke, Are da Dalhatu, Sababbin Jakadu da Tinubu Ya Nada

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya mika sunayen wasu fitattun mutane uku ga majalisar dattawa domin tantancewa a matsayin jakadun kasashen Amurka, Faransa da Birtaniya.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Mika sunayen sababbin jakadun uku ga majalisar dattawa ya kawo ƙarshen dogon lokaci da Najeriya ta shafe ba tare da jakadu a kasashen waje ba, kamar yadda muka ruwaito.

Shugaba Tinubu ya tura sunayen sababbin jakadu ga majalisar dattawa.
Ayodele Oke, dan jihar Oyo kuma tsohon shugaban NIA da Aminu Dalhatu, masanin diflomasiyya daga Jigawa. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Tinubu ya nada sababbin jakadu 3

Tun bayan hawan Tinubu mulki a 2023, bai nada jakadu ba, lamarin da masu suka ke amfani da hakan wajen caccakar gwamnati, in ji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda aka nada sun kunshi tsofaffin manyan jami’an leken asiri da diflomasiyya; Ayodele Oke daga Oyo, Lateef Kayode Are daga Ogun, da Aminu Muhammad Dalhatu daga Jigawa.

La'akari da shekarun kwarewarsu, hakan ya tabbatar da cewa Tinubu ya mayar da hankali wajen nada kwararru da za su wakilci Najeriya a kasashen waje.

Kara karanta wannan

Tinubu ya nada shugaban NIA da ya shiga badakalar $43m lokacin Buhari a matsayin Jakada

Shugaban ƙasa dai ya bayyana cewa wannan sabon mataki na cikin tsarin sabunta diflomasiyyar Najeriya, da kuma ƙarfafa huldar ƙasa da ƙasa domin amfanin tattalin arziki, tsaro, da siyasar ƙasa baki ɗaya.

Bayanin sababbin jakadu 3 da Tinubu ya nada

Legit Hausa ta tattaro wasu muhimman abubuwa game da sababbin jakadun da Tinubu ya nada:

1. Ayodele Oke

Shugaba Tinubu ya zabi Ayodele Oke a cikin sababbin jakadun da ya tura majalisar dattawa.
Ayodele Oke (tsakiya) ya na jawabi a wajen wani taron majalisar Atlantika, a Amurka. Hoto: @Imranmuhdz
Source: UGC

Ayodele Oke, wanda ya fito daga jihar Oyo, ya shafe fiye da shekaru 30 yana aikin diflomasiyya da leken asirin ƙasa.

Shi ne tsohon shugaban hukumar fikirar leken asiri (NIA) daga 2013 zuwa 2017, inda ya jagoranci muhimman ayyukan tsaro da suka shafi leken asirin ƙasashen waje da yaki da ta'addanci.

An zabe shi a lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan, kuma a lokacinsa an kara fadada rawar da Najeriya ke takawa a fannin diflomasiyyar fikirar tsaro.

Oke ya fuskanci bincike a shekarar 2017 bayan EFCC ta gano makudan kudade a wani gida a Ikoyi, wanda daga baya aka tabbatar a kotu cewa kudaden na ayyukan sirri ne na NIA.

A 2023, hukumar EFCC ta janye karar da aka shigar da shi, inda kotu ta wanke shi daga dukkan zarge-zarge gaba ɗaya, in ji rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Jira ya kare: Shugaba Tinubu ya nada jakadu bayan fiye da shekara 2 a mulki

Oke ya taba zama wakilin Najeriya a sakatariyar Commonwealth da ke birnin London, inda ya taka muhimmiyar rawa a muhawarar diflomasiyya ta kasa da kasa.

2. Lateef Kayode Are

Lateef Kayode Are ya fito daga jihar Ogun, kuma tsohon soja ne masanin leken asiri wanda tarihin aikinsa ya ratsa manyan matakan tsaro na Najeriya.

Ya kammala karatu a makarantar NDA sannan ya yi aiki a rundunar soja da kuma hukumar leken asirin sojoji (DMI) kafin daga bisani a nada shi shugaban hukumar SSS tsakanin 1999 zuwa 2007, shi ne shugaba mafi dadewa a tarihin hukumar.

Lateef Kayode Are ya rike muhimman mukamai a fadar gwamnati, ciki har da mukaddashin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a 2010, in ji sanarwar Bayo Onanuga, mai magana da yawun Tinubu.

Kwarewarsa a tattara bayanan sirri, tsare-tsaren kariyar cikin gida, da hadin gwiwar tsaro da kasashen waje ya sanya shi ya zama wanda ya dace ya wakilci Najeriya a kasar ketare.

3. Aminu Muhammad Dalhatu

Aminu Muhammadu Dalhatu ya shiga jerin sababbin jakadun da Tinubu ya tura sunayensu majalisa.
Aminu Muhammad Dalhatu, masanin diflomasiyya daga jihar Jigawa. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Aminu Dalhatu, masanin diflomasiyya ne na dogon lokaci daga Jigawa, kuma ya yi shuhura lokacin da ya yi rike jakadan Najeriya a Koriya ta Kudu tsakanin 2017 zuwa 2023.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Bola Tinubu ya dauka bayan sace dalibai a Kebbi da Neja

A wannan lokaci, ya kula da huldar tattalin arziki, musayar al’adu, da bunkasa zuba jari tsakanin Najeriya da kasar Koriya.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa an san Dalhatu da iya gudanar da muhimman shawarwari da kare muradun ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje.

Haka kuma, ya taka rawa wajen bude hanyoyin kasuwanci da kirkire-kirkire tsakanin biranen Seoul da Abuja.

A hukumar harkokin waje ta Najeriya, ya yi aiki a ofisoshi daban-daban da suka shafi manyan manufofi na diflomasiyyar ƙasa.

Nadin jakadu: DSS ta mika sunaye ga Tinubu

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya karɓi sabon jerin sunayen waɗanda za a naɗa jakadun Najeriya a kasashe daban-daban.

Majiyoyi daga fadar Shugaban kasa sun bayyana cewa yanzu abin da ya rage shi ne a sanya ranar da Tinubu zai aika jerin sunayen zuwa majalisar dattawa.

Wata majiya ta ce shugaban ƙasa ba zai fitar da duk sunayen jakadu baki ɗaya ba saboda nauyin kuɗin da ake bukata wajen tura su ƙasashe.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com