Maganganun Sanata Sun Tada Kura yayin Wata Muhawara Mai Zafi a Majalisar Dattawa

Maganganun Sanata Sun Tada Kura yayin Wata Muhawara Mai Zafi a Majalisar Dattawa

  • Sanatocin Najeriya sun yi muhawara mai zafi a Majalisar Dattawa kan tabarbarewar tsaro a jihohin Kwara, Kebbi da Neja
  • Ana zargin janye dakarun sojoji kafin harin da yan bindiga suka kai Kebbi, lamarin da ya janyo tambayoyi da neman a yi bincike
  • Sanatoci sun yi gargadin cewa Najeriya na cikin barazana, inda wasu ke fargabar akwai cin amana a cikin gida

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Majalisar Dattawa ta Najeriya ta yi zazzafar muhawara kan kara tabarbarewar tsaro a ƙasar nan, musamman a jihohin Kwara, Kebbi da Neja.

Sanatoci sun yi muhawara mai zafi kan lamarin bayan wani muhimmin kudiri da Sanata Lola Ashiru (Kwara ta Kudu) ya gabatar domin gaggawar tunkarar matsalar.

Majalisar Dattawa.
Zauren Majalisar Dattawa ta Najeriya Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta ce kudirin ya tabo lalacewar harkar tsaro da ya haɗa da sace dalibai a Jihar Kebbi, da kuma zargin janye sojoji a lokacin da ake buƙatar su a makarantar Maga.

Kara karanta wannan

Mai Mala Buni: Gwamna ya hango hadari, ya rufe dukkan makarantun kwana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Sanatoci suka tafka mahawara

Mataimakin Shugaban Majalisa, Sanata Barau Jibrin, ya ce za a iya magance matsalar tsaron Najeriya amma sai an nemi taimako daga ƙasashen waje.

“Ya kamata mu nemi taimako daga ƙasashen waje. Hakan zai taimaka wajen dakile wannan bala’i,” in ji shi.

Shugaban masu rinjaye, Sanata Opeyemi Bamidele, ya ce halin da ake ciki na tsaro ya kai matakin da ba za a cigaba da tafiya a haka ba.

Ya yi maraba da ceto wasu daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su, amma ya ce abin damuwa ne ba a ji labarin ‘yan ta’addan da aka kashe ba.

Ya kuma yi Allah-wadai da maganganun wasu ’yan Majalisar Wakilai da ke cewa a rufe Majalisar Tarayya gaba daya.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce akwai rahotannin da ke nuna cewa an samu rudani kan wurin da Birgediya Janar ya rasa ransa a Borno, lamarin da ya sa aka fara zargin akwai cin amana.

Kara karanta wannan

Sojoji sun dauki mataki kan dakaru da ake zargi sun janye kafin sace daliban Kebbi

Ya nuna mamaki kan yadda duk da gargadi da horo kare kai da aka bai wa dalibai, amma ’yan bindiga suka kutsa makarantar Kebbi ba tare da wani cikas ba.

Maganganun Sanatan Bayelsa sun tada kura

A yayin muhawarar, maganganun Sanata Seriake Dickson daga Beyelsa kan cewa Najeriya ta fara “ragurgujewa" sun tayar da kura har sai da aka kashe masa makirufo.

Sanata Adams Oshiomhole ya kare shugaban ƙasa Bola Tinubu, yana mai cewa yana bakin ƙoƙarinsa, cewar rahoton Vanguard.

Ya yi kira da a binciki wanda ya bayar da umarnin janye sojojin daga makarantar Maga, kafin harin da yan bindigar suka kai a Kebbi:

“A gurfanar da wanda ya bayar da wannan umarni bisa laifin ta’addanci," in ji shi.
Sanata Akpabio.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Alpabio. Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Wasu sanatocin sun shiga goyon bayan kafa dokar hukuncin kisa kan masu garkuwa da mutane, suna mai cewa hakan na iya zama hanyar rage mummunar al’adar da ta ƙara zama ruwan dare.

Majalisa ta bukaci a dauki karin sojoji

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta bukaci a sake fasalin tsaro da binciken makudan kudin da aka zuba a shirin kare makarantu a 2014.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya, Katsina da wasu jihohi da suka rufe makarantu bayan an shiga dauke dalibai

Majalisar ta kuma nemi Shugaba Bola Tinubu ya amince da daukar karin sojoji 100,000 domin dakile sace-sacen dalibai da hare haren yan ta'adda.

Wannan kira da Majalisar Dattawa ta yi na zuwa ne bayan harin da 'yan bindiga suka kai makarantar sakandiren yan mata ta Maga a jihar Kebbi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262