"Mutane Suna da Mantuwa," Sheikh Gumi Ya Yi Magana kan Zargin Goyon Bayan 'Yan Bindiga

"Mutane Suna da Mantuwa," Sheikh Gumi Ya Yi Magana kan Zargin Goyon Bayan 'Yan Bindiga

  • Fitaccen malamin nan, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya ce ba shi da wata alaka ko goyon bayan ’yan bindiga, sulhu kawai yake nema
  • Malamin addinin musuluncin ya fadi haka ne yayin da kiran a kama shi ya ƙaru saboda da hare-haren da suka ta'azzara a Arewacin Najeriya
  • Sheikh Ahmad Gumi ya ce tattaunawa ce kadai hanyar warware rikicin da ya addabi jihohin Arewa, ba ƙarfin soji ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Sanannen malamin addinin Musulunci mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya maida martani ga masu zargin yana goyon bayan 'yan bindiga.

Wasu dai na zargin malamain na da alaka ko goyon bayan ayyukan 'yan bindiga duba da yadda ya nace kan bakarsa ta tattaunawar neman sulhu da 'yan ta'adda.

Sheikh Ahmad Gumi.
Fitaccen malamin islama a Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta tattaro cewa Sheikh Gumi ya musanta wannan zargi, yana mai cewa duk abin da yake yi na shiga tsakani ne kawai domin samar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

'Ka tanadi hujjojI': Pantami zai iya shiga kotu da aka zarge shi da kisan dalibin ATBU

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fara kiran a kama Sheikh Ahmad Gumi

A baya-bayan nan, kira ya ƙaru na a kama Gumi, musamman a yayin da sabon salon sace-sacen mutane da dalibai ya sake kunno kai a Arewacin Najeriya.

Wannan lamarin dai ya janyo rufe makarantu da kuma ƙarin matakan tsaro daga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi.

A wata tattaunawa da aka yi da shi, Shehin Malamin ya ce kiran da ake yi a kama shi ya yi kama da rashin fahimtar rawar da yake takawa.

Ahmad Gumi ya kuma danganta wannan kira da hukuncin da aka yanke wa shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, da kuma yadda gwamnati ta murkushe fafutukar Sunday Igboho.

Me Sheikh Ahmad Gumi yake kokarin yi?

Sheikh Gumi ya ce:

“Ni mai neman zaman lafiya ne. Ba na son zubar da jini. Mutane suna mantawa cewa sojojinmu ma suna mutuwa. Kwanan nan mun rasa wani Birgediya Janar saboda harin Boko Haram.”

Kara karanta wannan

Bayan ceto dalibai 25, shaidanin ɗan bindiga ya shiga hannun jami'an tsaro

Ya zargi wasu kasashen waje da taimaka wa 'yan ta'adda da makamai, yana mai cewa Najeriya ba da kungiyoyin 'yan bindiga take fada ba, da wasu kasashen ketare take yaki.

Dr. Gumi ya ce matsalar da makiyaya ke fuskanta ita ce rasa hanyar da za su kai kokensu ga gwamnati, wanda ya sa wasu suka dauki makamai.

"Kamar likita ne ke bayyanin cuta, za ka ga mutane sun zarge shi da goyon bayan wannan cutar. Don haka fahimtar ɓangaren su ita ce hanyar samar da magani.”

Ya dage cewa tattaunawar sulhu ce kadai hanyar da za ta iya kawo karshen matsalar tsaro, domin amfani da ƙarfin soji shi kaɗai ba zai kawo mafita ba.

Malam Gumi.
Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Gumi
Source: Facebook

Dalilin Gumi na damuwa da 'yan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Ahmad Gumi ya kare kansa daga masu zargin cewa ya fi damuwa da 'yan bindiga fiye da mutanen da ake kai wa hare-hare.

Sheikh Gumi ya ce matsalar tsaron da ke kara ta'azzara a Najeriya, ta na bukatar a shawo kanta tun daga tushe domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa Sheikh Gumi ya fi damuwa da 'yan bindiga fiye da wadanda ake kai wa hari

Babban malamin ya bayyana cewa mutane ne ba su fahimce shi ba, amma burinsa a magance matsalar tun daga tushe.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262