'Yan Majalisar Neja Sun Fusata, Sun Shirya Daukar Mataki kan Jinkirin Ceto Daliban Papiri
- Majalisar Dokokin Jihar Neja ta yi barazanar rufe zama gaba ɗaya idan ba a ceto dalibai da ma’aikatan St Mary Catholic School, Papiri ba
- Kakakin majalisa, Abdulmalik Sarkindaji, ya zargi jami'an tsaro da gazawa wajen ceto yaran bayan sun san hanyoyin da 'yan ta'addan ke bi
- Majalisa ta fusata, ta ce halin tsaron da ake fuskanta a yanzu ya lalata dukkannin ci gaban da gwamnatin jihar ke kokarin kawowa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Niger – Majalisar Dokokin Jihar Neja ta bayyana takaici game da tabarbarewar tsaro a wasu sassan jihar, musamman bayan sace dalibai da ma’aikata a makarantar St Mary Catholic.
Saboda tsananin matsalar tsaron, majalisar ta yi barazanar dakatar da dukkannin harkokin majalisa idan ba a gaggauta ceto mutanen tare da inganta tsaro ba.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Kakakin majalisar, Rt. Hon. Abdulmalik Sarkindaji, wanda ya yi magana a jiya yayin zaman majalisa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar Neja ta magantu a kan rashin tsaro
Daily Post ta wallafa cewa Rt. Hon. Abdulmalik Sarkindaji, ya sha halartar tarurrukan tsaro tare da Gwamna Mohammed Umar Bago domin kawo wa jihar sauki.
Sarkindaji, wanda ya nuna bacin rai sosai, ya ce:
“Wannan hanyar da ’yan bindiga ke bi sananniya ce ga jami’an tsaro. Ba su da wata hanya sai dai wannan. Ina da tabbaci cewa daliban da aka sace za a bi da su ta nan zuwa Zamfara, kuma kowa ya san haka. Amma me ake yi a kai?”
Kakakin majalisar ya gargadi gwamnati cewa halin tsaron da jihar ke ciki ya sa duniya ta maida idanu a kan Neja, sannan ya haifar da tsoro ga masu zuba jari.
Majalisa na son a tsare makarantu
A cewarsa, idan har za a iya rufe makarantu da kasuwanni, za a iya dakatar da majalisa har sai an samu inganta tsaro.
Ya ce:
“Idan ba a dauki mataki ba, ba mu da wani zabi sai mu rufe harkokin majalisa domin mu ne wakilan jama’a.”

Source: Original
Daga baya, majalisar ta tattauna kudurin gaggawa da dan majalisa mai wakiltar Agwara, Hon. Mohammed Nura Agwara, ya gabatar.
'Yan majalisar baki ɗaya sun amince cewa a gaggauta ceto daliban da ma’aikatan Papiri domin kada su shiga matakin rufe majalisa domin nuna takaicinsu.
An fitar da sunayen daliban Neja
A baya, mun wallafa cewa a yayin da jami’an tsaro ke kara zage damtse domin ceto daliban da aka sace daga St. Mary Catholic School, Papiri, an fitar da sunayen wadanda aka dauke.
Rahoton ya nuna cewa hare-haren da aka kai ranar Juma’a ya shafi daliban sakandare, daliban firamare, malamai, da ma’aikatan makarantar, lamarin da ya daga hankulan jama'a.
A takardar da cocin Katolika ta fitar, an bayyana cewa adadin mutanen da ake nema ya kai 265, inda suke kunshe da malamai 12, daliban sakandare 14 da kuma daliban firamare 239.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


