Ana Zargin Gwamna Ya Wawure Kudin Kananan Hukumomi, Gwamnati Ta Yi Bayani

Ana Zargin Gwamna Ya Wawure Kudin Kananan Hukumomi, Gwamnati Ta Yi Bayani

  • Gwamnatin Kogi ta ce ana yada jita-jitar karkatar da kudin kananan hukumomi domin bata sunan Gwamna Usman Ododo
  • Ma'aikatar labarai ta ce kananan hukumomi na karɓar kudinsu kai tsaye, suna aiwatar da ayyuka da kuma biyan albashi da kansu
  • Gwamnatin ta ce kananan hukumomin na wallafa ayyukansu don jama'a su tantance, wanda hakan yake karyata zarge-zargen da ake yi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kogi - Gwamnatin Kogi, karkashin Ahmed Usman Ododo ta karyata zargin cewa tana karkatar da kudaden kananan hukumomi.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ana kirkirar waɗannan zarge-zargen ne kawai domin a bata sunan Gwamna Usman Ododo.

Gwamanti ta karyata zarge-zargen cewa Usman Ododo yana karkatar da kudaden kananan hukumomi.
Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo a wajen wani taro a Lokoja. Hoto: @OfficialOAU
Source: Facebook

Kogi: Ododo na karkatar da kudin kananan hukumomi?

Kwamishinan yada labarai, Kingsley Fanwo, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai, in ji rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Bayan korar ma'aikata, Ganduje zai kafa hukumar Hisbah mai zaman kanta a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kingsley Fanwo ya ce ana kokarin nunawa duniya cewa gwamnatin Ododo ta na tsoma hannu a kudin kananan hukumomi, duk kuwa da cewa babu hujja.

Ya ce gwamnati da yi niyyar ta yi shiru da farko, amma ta ga bukatar yin martani tare da warware rudanin da aka jefa al'umma a ciki.

Sanarwar ta ce ko nesa ko kusa, gwamnatin Usman Ododo ba ta karkatar da kudin kananan hukumomi, don haka jama'a su yi watsi da zarge-zargen da ake yi.

Kananan hukumomi na kashe kudinsu kai tsaye

Fanwo ya ce duk wanda ke yada wannan jita-jita yana yi ne don cimma wani muradin siyasa domin a cewarsa, babu wata hujja da aka kawo.

Ya kara da cewa gwamnati na mutunta ‘yancin kananan hukumomi, inda kowace karamar hukuma tana karɓar kudinta kai tsaye, tana tsara kasafin kudi da aiwatar da albashi da ayyuka ba tare da tsoma bakin gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Wasu 'yan Najeriya 2 sun damfari gwamnatin Amurka, sun girbi abin da suka shuka

Jaridar The Cable ta rahoto kwamishinan ya ce:

“Kananan hukumomi su ke karɓar kudadensu, su ke tsara ayyuka, su ke biyan ma’aikata, su ke kwangila da kansu.”

Fanwo ya kara nuna cewa dukkan kananan hukumomi 21 suna wallafa bayanan kudinsu a shafin gwamnati domin tabbatar da gaskiya ga jama’a.

Gwamnatin Kogi ta ce kananan hukumomin jihar na kashe kudadensuda kansu ba tare da tsoma bakin Ododo ba.
Taswirar jihar Kogi da ke a Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ayyukan da kananan hukumomin Kogi ke gudanarwa

Kwamishinan ya jera ayyukan da kananan hukumomi ke yi, ciki har da ginawa da gyaran cibiyoyin lafiya, samar da ruwan sha, gyaran hanyoyi, da shirye-shiryen karfafa matasa.

Ya ce kowace karamar hukuma ta horar da matasa 110 kan mayar da ababen hawa daga fetur zuwa CNG tare da samar da kayan aikin da za su raba su daga neman aiki zuwa samar da ayyuka.

Haka kuma an karfafa tsaro ta hanyar daukar mafarauta, tallafa wa kungiyoyin sa-kai, da samar da babura, motocci da ofisoshi.

Fanwo ya ce kananan hukumomi na biyan albashi da fansho yadda ya kamata tare da fara biyan wasu daga cikin tsoffin hakkokin da aka bari tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kaduna ta taso El Rufai a gaba kan zargin biyan 'yan bindiga N1bn

Mahaifin Gwamna Ododo ya rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, mahaifin Gwamna Ahmed Usman Ododo na jihar Kogi, Ahmed Momohsani Ododo ya rasu.

Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da rasuwar mahaifin gwamnan a wata sanarwa da ta fitar, ta ce ya rasu yana da shekaru 83 a duniya.

Sanarwar ta bayyana cewa za a yi jana'izar marigayin kamar yadda addinin musulunci ya tanada, ta yi addu'ar Allah ya gafarta masa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com