Sarkin Musulmi Ya Amince a Shirya Fim Din 'Yar Dan Fodiyo, Nana Asma'u
- An samu sahalewar gwamnati da Sarkin Musulmi domin shirya fim kan tarihin Nana Asma’u, ‘yar Shehu Usmanu Dan Fodiyo
- Masarautar Sokoto ta amince da aikin bayan roƙo daga masu shirya fim ɗin, tare da buƙatar a rika ba ta rahoto lokaci zuwa lokaci
- Rahama Abdulmajid ta bayyana cewa fim ɗin zai ilmantar, ya nishadantar, ya kuma ƙarfafa haɗin kai da fahimtar juna a ƙasar nan
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya tare da Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’adu Abubakar III, sun amince da fim da zai yi nazari kan tarihin Nana Asma’u, ‘yar Shehu Usmanu Dan Fodiyo.
Aikin ya samu sahalewar hukumomi bayan shekaru hudu da aka shafe ana shiri da nazari kan rubuce-rubuce da tarihin marigayiyar.

Source: Facebook
Jagorar aikin, Rahama Abdulmajid ta wallafa a Facebook cewa manufar fim ɗin ita ce wayar da kai, samar da zaman lafiya da tabbatar da cewa tarihin Nana Asma'u ya cigaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin shirya fim din Nana Asma'u
Yayin da ta mika godiya ga Allah kan samun damar shirya fim din, Rahama Abdulmajid ta yi karin haske game da aikin, inda ta ce:
“Wannan ce ta mu gudunmuwar… Alhamdulillah. A lokacin da ake son bata wa addini suna da cewa mata ba su cancanci yin ilmi ba, har a ke sace su a makarantu a ke tilasta hukumomi wajen rufe makarantu.
"Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya ba mu cikakken izini na mu je mu karasa aikin da muka fara tun shekaru hudu.
"Masarautar ta ba mu shaidar halascin yin fim ɗin Nana Asma’u, ‘yar Shehu Usmanu Dan Fodio. Ita ma ma’aikatar zuba jari da kasuwanci ta bayar da wannan izini a rubuce.

Kara karanta wannan
Kano: Ganduje, 'yan APC sun fitar da 'dan takarar shugaban kasa da suke so a 2027
"Sai a biyo mu da addu’a ‘yan uwa. Allah Ya sa mu iya, Allah Ya sa mu ilmantar mu nishadantar.”

Source: Facebook
Sultan ya yarda da fim din Nana Asma'u
A cikin wasikar amincewar, masarautar Sokoto ta bayyana farin cikinta kan ɗaukar nauyin shirya fim game da Nana Asma’u.
Sanarwar ta ce Nana Asma'u ta kasance wata matashiya da ta taka rawa wajen yada ilimi, shiryar da mutane da rubuce-rubuce tun farkon ƙarni na 19.
Daily Trust ta rahoto cewa masarautar ta nemi a rika ba ta rahoto kan matakan da ake dauka, tare da halartar tantancewar ƙarshe kafin fitar da fim ɗin a bainar jama’a.
Gwamnati ta yarda da fim din Nana Asma'u
Ma’aikatar zuba jari da kasuwanci ta tabbatar da sahalewar aikin, wanda hakan ya ƙara tabbatar da halascin gudanar fim din.
Rahama Abdulmajid ta ce fim ɗin ba na 'yan Arewa kaɗai ba ne, domin tarihin Nana Asma’u tarihi ne da ya shafi ilimi, addini da shugabanci da dukkan al’ummar ƙasar nan za su amfana da shi.
Ta ce rayuwar Nana Asma’u hujja ce mai ƙarfi cewa ilimin mata ya samo asali tun fil azal a al’adun Hausawa da Fulani da addinin Musulunci, ba wani sabon abu da aka aro daga wajen ƙasa ba.
Sarkin Musulmi ya yi magana kan tsaro
A wani labarin, mun kawo muku cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi magana kan halin rashin tsaro da ake fama da shi a Najeriya.
Sultan ya yi kira ga jami'an tsaro da ke fagen daga da su kakkabe 'yan ta'adda ba tare da la'akari da addini ko kabilarsu ba.
Mai alfarman ya yi magana ne yayin da ake cigaba da fama da matsalar tsaro a Najeriya, musamman sace dalibai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

