Gwamnatin Kebbi Ta Karbi Ƴan Matan Sakandaren Maga 24 da Aka Kuɓutar

Gwamnatin Kebbi Ta Karbi Ƴan Matan Sakandaren Maga 24 da Aka Kuɓutar

  • Rundunar tsaron Najeriya ta samu nasarar ceto daliban makarantar GGCSS Maga da ’yan bindiga suka sace a makon da ya gabata
  • A daren Talata, 25 ga watan Nuwamba ne aka mika yaran ga Gwamnan Kebbi, Dr. Nasir Idris, bayan sun shaida cewa suna cikin koshin lafiya
  • Duk da tabbatar da lafiyarsu, an shawarci gwamnatin Nasir Idris a kan ta tabbata likitoci sun kara bincikar lafiyan daliban baki dayansu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kebbi – Gwamnatin jihar Kebbi ta sanar da karbar dalibai mata 24 da 'yan ta'adda suka sace daga makarantar Maga a cikin koshin lafiya.

'Yan ta'addan sun kutsa makarantar Maga a makon da ya gabata tare da daliban bayan sun kashe mataimakin shugaban makarantar da ya yi kokarin hana su kwashe daliban.

Kara karanta wannan

Duniya na kallo: Harin Kebbi da wasu hare hare da suka girgiza Arewa a Nuwamba

An ceto daliban Kebbi lafiya lau
Daliban Maga da sojoji suka ceto, gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi Hoto: Bashir Ahmad/Yahaya Sarki
Source: Facebook

Sanarwar da Mashawarcin gwamnan Kebbi Yahaya Sarki ya wallafa a shafinsa na Facebook ta tabbatar da cewa gwamna Nasir Idris ya karbi daliban a hannunsa.

An mika daliban Kebbi ga gwamna

Gwamnan Jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris ya karbi daliban Kebbi a yammacin Talata a Birnin Kebbi bayan sun shafe kwanaki a hannun 'yan ta'adda.

An mika daliban bisa sahalewar karamin Ministan tsaro, Muhammad Bello Matawalle, wanda ya umarci shugabannin rundunar da su tabbatar da komawar daliban gida.

Shugaban rundunar sojojin yaki a yankin, Manjo Janar W. B. Idris, shi ne ya jagoranci mika yaran bayan bayan dakaru sun yi aikin ceto su daga hannun 'yan bindiga.

A cewarsa, bayan sojoji sun gano yaran, sai suka kewaye wurin gaba ɗaya, suka toshe dukkannin hanyoyin shiga da fita domin hana ’yan bindiga tserewa.

A cewar Manjo Janar Idris:

“Ranar 19 ga wannan wata, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci karamin Ministan Tsaro ya koma Kebbi kai tsaye, ya tabbatar da komawar dukkannin ɗaliban da aka sace. A yau muna mika ɗalibai 24, dukkanninsu suna cikin koshin lafiya.”

Kara karanta wannan

Shawarar da Gwamna Nasir ya ba daliban da 'yan bindiga suka saki a Kebbi

An shawarci gwamnatin Kebbi

Manjo Janar Idirs ya shawarci gwamnati ta tabbata likitoci sun duba yaran domin tabbatar da lafiyarsu gaba ɗaya.

Haka kuma ya isar da godiyar Shugaban Sojojin Ƙasa da kuma Shugaban Rundunar Tsaro ga Gwamnatin Kebbi, Ministan Tsaro, da sauran jami’an tsaro da suka taimaka wajen nasarar aikin.

Gwamnatin Kebbi ta karbi daliban Maga
Daliban Maga da sojoji suka ceto, Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Da yake karɓar ɗaliban, Gwamna Nasir Idris ya nuna jin dadinsa tare da godewa Allah SWT, ya godewa Shugaba Tinubu bisa jajircewarsa har aka ceto yaran.

Masawarcinsa a kan harkokin yada labarai, Sarki Yahaya ya tabbatar wa Legit cewa gwamnan ya yabawa sojoji da sauran jami’an tsaro kan jajircewa da haɗin kai da suka nuna tun daga lokacin da aka sace yaran har zuwa cetonsu.

Ya kuma gode wa ’yan Najeriya bisa addu’o’i, sakonni, da kulawa da suka nuna a lokacin tashin hankali, musamman malamai da manyan baki da suka isa jihar don jaje.

An ceto daliban makarantar Kebbi

Kara karanta wannan

Gwamnan Kebbi ya yi magana kan batun biyan 'yan bindiga kudin fansa kafin sako dalibai

A wani labarin, mun wallafa cewa a ranar Talata, 25 ga watan Nuwamba 2025, aka tabbatar da ceto dalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Jihar Kebbi bayan sojoji sun yi aikin ceto su.

Wannan labari ya kawo farin ciki da natsuwa ga iyaye, al’umma da kuma hukumomin tsaro da ke cikin damuwa tun bayan sace yaran da aka yi a makon da ya gabata tare da kashe malaminsu.

Mutane da dama sun rika tambayar yadda aka yi har dakarun suka samu damar kubutar da yaran cikin lafiya kalau, duba da yadda lamarin ya dauki hankali a fadin kasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng