An Fara Cika Umarnin Tinubu game da Janye 'Yan Sanda daga Tsaron Manyan Mutane
- Rundunar 'yan sandan Najeriya ta fara cika umarnin da Shugaban kasa, Bola Ahmd Tinubu ya bayar a kan jami'anta
- Shugaba Tinubu ya yi umarnin a janye dukkanin jami'an 'yan sanda da ke tsaron manyan mutane a fadin Najeriya
- Bola Tinubu ya bayar da umarnin bayan an samu karuwar hare-hare, musamman a makarantun da ke karkara a kasar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Rundunar tsaro ta musamman (SPU) ta ba da umarni kai tsaye ga dukkannin 'yan sandan da ke aikin gadin manyan mutane da wurare na musamman a fadin Najeriya.
Rundunar ta kuma ba su umarnin su gaggauta koma wa bakin aiki bayan da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce su dawo bakin aiki.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta ruwaito cewa a ranar 23 ga watan Nuwamba, ya bukaci a hanzarta janye dukkannin ’yan sanda da ke aiki a matsayin masu gadin manyan mutane a ko’ina cikin kasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An fara cika umarnin Bola Tinubu
TVC News ta wallafa wata takarda da Kwamandar SPU Base 16 da ke Legas, Neji Veronica, ta rattaba wa hannu ta umarci duk jami’an da abin ya shafa da su dawo sansanin yan sandan.
Takardar ta ce:
“Dangane da umarnin Shugaban Kasa kan janye dukkannin jami’an ’yan sanda daga gadin manyan mutane, Kwamandan SPU Base 16 na umartar a janye duk ma’aikata daga gadin manyan mutane a fadin tarayya, su koma sansani nan take. A tabbatar an dawo kafin ƙarshen yau Litinin 24/11/2025."
A cewar Fadar Shugaban Kasa, wannan sabon salo zai ba wa rundunar ’yan sanda damar komawa bakin aikinsu na asali — wato tsaro a al’umma.
Hakan zai yi tasiri musamman a yankunan karkara inda ofisoshin ’yan sanda ke fama da karancin jami'ai, hakan kuma na barin jama’a cikin hadari, inji sanarwar.
Za a musanya 'yan sandan da jami'an NSCDC
Gwamnati ta bayyana cewa daga yanzu duk wani babban mutum da ke bukatar jami’an tsaro mai dauke da bindiga zai nemi hakan daga hukumar tsaron fararen hula ta NSCDC.

Source: Facebook
Domin karfafa wannan mataki, Shugaban Kasa ya amince da daukar sababbin ’yan sanda 30,000 a fadin kasa, tare da shirin gyara cibiyoyin horas da jami'an.
Janye jami’an manyan mutane ya zo ne a daidai lokacin da hare-hare ke karuwa a Arewa, musamman jihohin Kebbi, Neja da Kwara.
'Yan sanda sun kai hari Gombe
A baya, mun wallafa cewa rundunar ’yan sanda ta jihar Gombe ta musanta rade-radin cewa wasu ’yan bindiga sun kai hari wani coci na ECWA jim kadan bayan hari a Kebbi da Neja.
Kakakin rundunar, Buharee Abdullahi Dam Roni, ya bayyana cewa babu wani hari da aka kai, ko sace mutane, kuma labarin da ake yadawa ba shi da kamshin gaskiya ko kaɗan.
A sanarwar, rundunar ta ce lamarin da ake yadawa ya samo asali ne daga rubutun wata mata mai suna Shallangwa da ta wallafa a shafinta na sada zumunta, sannan daga baya ta goge shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


