‘Maganganun Tinubu ne Suka Jawo’: Ministan Buhari kan Karuwar Rashin Tsaro
- Tsohon ministan matasa da wasanni a Najeriya, Solomon Dalung ya yi magana game da karuwar ayyukan ta'addanci a Najeriya
- Dalung ya zargi Shugaba Bola Tinubu da fallasa muhimman bayanan tsaro a fili, yana mai cewa hakan yana kara wa ’yan ta’adda karfin gwiwa
- Tsohon ministan ya ce karin hare-haren da ake gani yanzu na da alaka kai tsaye da kalaman gwamnatin Tinubu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon Ministan Wasanni da Cigaban Matasa, Solomon Dalung, ya caccaki gwamnatin tarayya kan yadda take tafiyar da harkokin tsaro.
Dalung yana zargin cewa kalaman Shugaba Bola Tinubu kan batun tsaro suna karfafa ’yan ta’adda tare da tsananta matsalolin hare-haren da ake fama da su a fadin kasar.

Source: Facebook
Yadda aka zargi Tinubu da kara rashin tsaro
Da yake magana a tashar Trust TV, Dalung ya ce Tinubu yana bayyana dabarun aiki na rundunar soja da sauran jami’an tsaro a fili, lamarin da ya zama abin da ya mayar da kokarin gwamnati baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce ya kamata a taya shi murna saboda yadda yake fadin dabarun tsaro inda ya tuna lokacin mulkin Buhari da idan an kai hari ake Allah wadai.
A cewarsa:
“Ya kamata ma in yi wa Shugaba Tinubu taya murna, domin ya sake yaudararmu. Na kasance cikin gwamnati a lokacin Buhari."
Ya ce duk lokacin da aka kai hari, gwamnati za ta ce mun la’anci, mun dauki mataki, muna kan shawo kan lamarin.
Dalung ya ce amma duk lokacin da shugaban kasa ya yi irin wannan magana, ’yan ta’adda sai su kara karfin kai farmaki.

Source: Getty Images
Dalung ya soki dabarun tsaro a Najeriya
Tsohon ministan ya ce karin hare-haren da ake gani a jihohi daban-daban yanzu ya samo asali ne daga irin bayanan da gwamnati ke yi a bainar jama’a.
“Tinubu ya fito ya ce an sauya hafsoshin tsaro, za a sake fasalin tsaro. Wa ya ce sai mun sani? Idan ’yan ta’adda za su kai hari, suna sanar da hakan ne? Fallasa dabarun tsaro a fili ba abu ne mai amfani ba."
- Cewar Dalung
Ya kara da cewa gwamnati mai tsanani da ke fuskantar barazanar tsaro ba za ta yi maganganun kwantar da hankali a talabijin ba, yayin da mutane ke shiga sakaci.
Ya ce lokacin da Amurkawa suka zo Najeriya suka ceto mutanensu, ka ji wani abu kafin su gama?
'Dan adawar bai tsaya a nan ba, ya ce gwamnati mai tsaro ba ta bayyana dabarunta a TV.
Dalung ya yi nuni da cewa ’yan ta’adda ne yanzu ke rike da akalar lamurra, suna iya yin garkuwa da mutane ba tare da tsoro ba. "
Dalung ya caccaki salon mulkin Tinubu
Mun ba ku labarin cewa tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya nuna ƙarara cewa ba ya ƙaunar talaka.
Ya yi zargin Tinubu ne shugaban Najeriya na farko da ke amfani da talauci da tsananin yunwa wajen daƙile al'ummarsa.
Dalung ya kara da cewa wannan na daga cikin dalilan da talakawa ke kara marawa hadakar su Atiku Abubakar baya gabanin 2027.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

