Tsohon Hadimin Buhari Ya Soki Yunkurin Ganduje a Kano, Ya Shawarci Gwamnati
- Bashir Ahmad, tsohon hadimin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana takaicin yunkurin Abdullahi Umar Ganduje
- Tsohon gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da yunkurin samar da hukumar Hisbah mai zaman kanta a jihar
- Sai dai Bashir Ahmad ya hango matsala a cikin wannan yunkuri, inda ya bayyana shakku a kan dalilan Ganduje na furta haka
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Tsohon mai taimaka wa shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya bayyana takaici a kan kalaman tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa yana shirin kafa hukuma mai zaman kanta da za ta riƙa ayyuka irin na hukumar Hisbah.

Source: Facebook
Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na X cewa wannan yunkuri na abu ne mai kyau ba kuma akwai ayar tambaya a kansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An fara sukar yunƙurin Ganduje a Kano
Bashir Ahmad ya bayyana takaici a kan yadda tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi niyyar kafa hukumar Hisbah.
Rahotanni sun bayyana Ganduje ya fara tunanin samar da hukumar domin ɗaukar ma'aikatan Hisbah ta Kano da gwamnati ta sallama daga aiki.

Source: Facebook
A cewar Bashir Ahmad:
“Ban san wane irin dalili tsohon gwamnanmu ya ke da shi wajen fitowa da irin wannan tunani a yanzu ba, amma gaba ɗaya ba daidai ba ne Gwamnatin Kano ta bari wani mutum ya kafa rundunar tsaro mai zaman kanta."
Ya kara da cewa:
"Tsaro nauyin gwamnati ne, ba wani abu da za a mika wa hannun masu zaman kansu ba. Saboda haka bai kamata wannan gwamnati ta amince da wannan ra’ayi ba.”
Ganduje: Jama'a sun yi martani ga Bashir
Wannan furuci ya sake tayar da mahawara a shafukan sada zumunta, inda al’umma ke tofa albarkacin bakinsu game da illolin da irin wannan tsari ka iya haifarwa a Kano da ma ƙasa baki ɗaya.
Wani mai amfani da X, @LNat_001, ya kwatanta lamarin da yadda Maiduguri ta kasance kafin shekarar 2009, yana mai gargadin cewa:
“Irin abin da ya faru a Maiduguri kafin 2009 na shirin sake faruwa. Yana da kyau mu daƙile shi tun yanzu.”
@abuabdallahie, ya ce:
"A ina aka yi maganar hukumar tsaro? Mutanenmu ba sa son karatu."
Wasu a gefe kuma su na ganin wannnan kokari na cikin dabarun da APC za ta yi domin @Oluchifight, ta ce:
“An yankewa MNK hukunci yanzu. Yanzu kuma za a kafa wata hukumar 'yan sandan addini? Wannan abu na iya ƙara zafin zargin cin zarafin Kiristoci.”
@Holyfam_sana ya yi zargin cewa:
"Ana son kafa hukumar da za ta taimakawa jam'iyyar APC ta ci zaɓen 2027."
A halin yanzu, babu wata sanarwa kai tsaye daga gwamnatin Kano da ke magana a kan batun da Ganduje ke shirin kinkimowa.
Ganduje zai kafa hukuma kamar Hisbah
A baya, mun wallafa cewa tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da shirin kafa wata kungiyar tsaro a jihar domin tallafawa zaman lafiya.
Majiyoyi sun ce kungiyar za ta yi kama da hukumar Hisbah amma karkashin gidauniyar Ganduje, domin taimakawa ma’aikatan da aka sallama a baya.
Ganduje ya bayyana wannan shirin ne lokacin da yake karɓar rahoton alkaluman ma’aikatan da aka sallama daga Dr. Baffa Babba Dan-Agundi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


