'Ana cikin Tsoro,' 'Yan Majalisar Sun Yi Zazzafar Muhawara kan Rashin Tsaro
- Majalisar wakilai ta yi zama na musamman inda ta danganta tabarbarewar tsaro da gazawar gwamnati, rashin tsaro a iyakoki da sauransu
- Shugabannin majalisa da dama sun ce dole ne a ɗauki matakai na gaggawa, ciki har da samar da rundunar tsaron iyaka da inganta dokoki
- An ce Najeriya ta fuskanci fiye da hare-hare 24,000 cikin shekara, lamarin da ya sa ake kira da a maida hankali kan dabarun tsaro na fasaha
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Majalisar wakilai ta gudanar da wani zama na musamman domin tattauna tsananin tabarbarewar tsaro a fadin ƙasar.
Mambobi sun yi jawaban da suka bayyana cewa al’amura sun kai matakin da bai kamata a yi shiru ba.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa ’yan majalisar da dama sun yi magana cikin takaici, suna mai kiran majalisa ta ɗauki alhakin da ya rataya a wuyanta domin kubutar da ƙasa daga halin da ta shiga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zaman ya yi karin haske kan abubuwan da ke haddasa tashin hankali, ciki har da tashe-tashen hankula na siyasa da sauransu.
Majalisa ta ce 'yan kasa na cikin tsoro
Hon. Kingsley Chinda, ya ce ’yan Najeriya na rayuwa cikin tsoro saboda gwamnati ta kasa aikinta na kare rayuka.
Punch ta rahoto cewa Kingsley Chinda ya bayyana cewa ba zai yiwu a shawo kan matsalar tsaro ba sai an yi gaskiya da haɗin kai.
Ya ce:
“'Yan Najeriya suna tafie-tafiye cikin fargaba, suna rayuwa a kasar da gwamnati ta gaza yin aikinta.”
Ya yi tambaya mai zafi da cewa:
"Idan gwamnati ba ta iya kare rayuka da dukiyoyi ba, shin ’yan majalisa sun cancanci ci gaba da zama a kujerunsu?"
Chinda ya yi gargadin cewa ya kamata a daina daurawa sabanin addini kadai laifin matsalar tsaro, domin akwai abubuwa da dama da ke haddasa rikice-rikicen.
Ya ce cikin abubuwan akwai siyasa, kaura da tashi daga wurare zuwa wasu sakamakon talauci, da kuma shigo da mutane ta iyakokin da ba a kula da su.
Kalu da Nwokolo sun magantu kan tsaro
Mataimakin shugaban Majalisa, Benjamin Kalu, ya ce matsalar tsaro a Najeriya ta kai wani matsayi da sojoji kadai ba za su iya magance ta ba.
Ya ce Najeriya na da dokoki masu tsauri, amma rashin aiwatar da su, tabarbarewar cibiyoyin kasa da rashin wadataccen kudi na kara dagula lamarin.

Source: Facebook
Shi ma Victor Nwokolo ya bayar da rahoton halin da ake ciki a jihar Delta, inda ya ce maharan da masu satar mutane suna samun bayanai daga 'yan acaba da masu Keke Napep.
An kai hare-hare 24,000 a shekara 1
Hon. Julius Ihonvbere, ya bayyana adadin hare-haren da aka kai daga Disamban 2023 zuwa Nuwamba 2024 ya kai fiye da 24,000.
Ya kara da cewa a Arewa maso Yamma, ’yan bindiga sun koma garkuwa da mutane ta hanyar kungiyoyin da suka tsara, yayin da Boko Haram da ISWAP ke ci gaba da kai hare-hare.
'Dan majalisar ya ce sama da mutane miliyan 1.5 na zaune a sansanonin ’yan gudun hijira daban-daban a fadin kasar nan..
Maganar Buba Galadima kan tsaro
A wani labarin, mun kawo muku cewa jigon NNPP, Injiniya Buba Galadima ya ce gwamnati ta gaza kare rayukan 'yan kasa.
Buba Galadima ya yi magana ne yayin da gwamnatocin jihohi ke rufe makarantu saboda sace dalibai da malamai.
'Dan siyasar ya bukaci gwamnati ta tashi tsaye wajen ba makarantu tsaro ba ta rika kulle su saboda tsoron 'yan ta'adda ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


