Sace Dalibai: Tinubu Ya ba Sojoji Umarnin Mamaye Dazuzzuka a Kwara da Jihohi 2

Sace Dalibai: Tinubu Ya ba Sojoji Umarnin Mamaye Dazuzzuka a Kwara da Jihohi 2

  • Shugaba Bola Tinubu ya umurci sojoji su fantsama cikin dazuzzukan Kwara, Neja da Kebbi don murƙushe ’yan ta’adda
  • Gwamnati ta tura jiragen yaki su rika shawagi a sama don taimaka wa sojojin kasa wajen ceto mutanen da aka sace
  • Jerin hare-haren 'yan bindiga a Kebbi, Neja da Kwara ya tayar da hankali sosai, yayin da aka rufe makarantu a jihohi da dama

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya ba sojoji umarnin mamaye dazuzzukan jihar Kwara sakamakon harin ’yan ta’adda da ya yi sanadin sace mutane da dama.

Wannan mataki ya zo ne bayan harin 'yan ta'adda a Eruku da kuma garkuwa da dalibai a jihohin Neja da Kebbi a cikin mako guda.

Shugaba Tinubu ya a sojoji umarnin kakkabe 'yan ta'adda da suke a dazuzzukan Kwara da jihohi 2
Shugaba Bola Tinubu ya na tattaunawa da hafsoshin tsaro da ministoci a fadar Aso Rock. Hoto: @SundayDareSD
Source: Twitter

Tinubu ya ba sojoji umarnin mamaye dazuzzuka

Kara karanta wannan

Bayan ceto dalibai 25, shaidanin ɗan bindiga ya shiga hannun jami'an tsaro

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Sunday Dare, ya bayyana matakin Tinubu a sanarwar da ya fitar a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya kuma umurci rundunar sojan sama ta fadada tsaron sama a cikin dazuzzukan Kwara domin gano maboyar ’yan ta’adda.

Mai ba shugaban kasar shawara ya ce wannan umarni ya shafi dukkan yankunan da ke tsakanin Kwara, Neja da Kebbi ne.

Sunday Dare ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a rika yawo da jiragen yaki a sama a ko da yaushe, domin su tallafa wa sojojin ƙasa da ke aikin fatattakar ’yan bindiga.

Ya ce ana bukatar al’umma su rika ba da bayanan gaggawa idan sun ga duk wani motsi da ba su saba gani ba.

Sace dalibai da masu ibada a Arewa

Matsalar tsaro ta ƙara ta’azzara ne bayan da ’yan bindiga sun mamaye makarantar St. Mary da ke Papiri, jihar Neja, inda suka sace fiye da dalibai 300 da malamai 12.

Kara karanta wannan

'Tinubu ne ya tsara komai': Yadda aka ceto Kiristoci 38 da aka sace a Kwara

A cikin makon, 'yan bindiga suka kuma sace dalibai 25 a makarantar GGCSS Maga, jihar Kebbi, sannan suka yi awon gaba da masu ibada 38 daga cocin Eruku a Kwara.

Daga baya, kungiyar CAN ta rahoto cewa fiye da dalibai 50 na makarantar St. Mary da aka sace sun gudo daga hannun 'yan bindiga, amma 'yan sanda sun ce ba su tabbatar da hakan ba.

Kwamishinan ’yan sandan Neja, Adamu Abdullahi Elleman, ya ce yana kokarin samun karin bayani daga CAN game da yadda yaran suka kubuta, in ji rahoton BBC.

Shugaba Bola Tinubu ya umarci rundunar sojin sama ta tura jiragen yaki don taimakawa sojojin kasa.
Shugaba Bola Tinubu a lokacin da za a fara taron majalisar zartarwa ta tarayya a Abuja. Hoto: @SundayDareSD
Source: Twitter

An rufe makarantu a jihohi da dama

A halin yanzu, rundunonin soji suna ci gaba da gudanar da babban samame domin ceto ragowar dalibai 253 da malamai 12 da ke hannun ’yan ta’adda, in ji rahoton Channels TV.

Bayan yawaitar hare-haren, gwamnati ta rufe makarantu da dama a jihohin Neja, Kebbi, Kwara, Katsina, Plateau da Bauchi domin hana karin barna.

Wannan ya sake tuno da babbar garkuwa da daliban Chibok da 'yan bindiga suka yi a 2014, inda har yanzu dalibai 90 ba su koma gida ba.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Bola Tinubu ya dauka bayan sace dalibai a Kebbi da Neja

An ceto daliban Kebbi da aka sace

A wani labarin, mun ruwaito cewa, an ceto daliban makarantar GGCSS Maga, jihar Kebbi da aka sace makon jiya daga hannun 'yan bindiga.

Ba a bayyana yadda aka yi nasarar ceto su, domin har yanzu babu ciakkun bayanai, amma ana sa ran gwamnati za ta fitar da sanarwa daga baya.

A ranar 17 ga Nuwambar 2025, ‘yan bindiga sun kai hari makarantar, inda suka dauke dalibai mata 25, suka kashe ma’aikaci sannan suka jikkata wani jami’in tsaro.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com