Babbar Kotu Ta Yi Zama kan Shari'ar Tsohon Gwamnan da Aka Yi Jita Jitar Ya Mutu

Babbar Kotu Ta Yi Zama kan Shari'ar Tsohon Gwamnan da Aka Yi Jita Jitar Ya Mutu

  • Hukumar EFCC ta bukaci babbar kotun tarayya ta dage shari'ar tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano
  • Lauyan EFCC ya ce sun gabatar da wannan bukata ne domin a bari alkalin da ya fara shari'ar ya dawo ya karasa
  • Bayan sauraron kowane bangare, kotun ta dage zaman shari'ar har sai baba ta gani kamar yadda masu kara suka nema

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya mai zama a Abuja ta yi zama yau Talata, 25 ga watan Nuwamba, 2025 kan shari'ar tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano.

Wannan zaman kotu ya zo ne kwanaki kadan bayan an yada wata jita-jita da ke cewa Obiano ya mutu, rahoton da ya fito da kansa ya karyata.

Tsohon gwamnan Anambra, Willie Obiano.
Tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano a cikin kotu Hoto: Willie Obiano
Source: UGC

Kotu ta dage shari'ar Willie Obiano

Jaridar Vanguard ta ruwato cewa kotun tarayya ta dage shari'ar da ake tuhumar tsohon gwamnan Anambra da karkatar da akalla Naira biliyan 4 har sai baba ta gani.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: ASUU ta kira taron NEC bayan gama sauraron wakilan Gwamnatin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan bukatar da mai kara, Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC), ta gabatar na neman dage shari’ar har abada.

Lokacin da aka kira karar a gaban Mai Shari’a Mohammed Umar, Lauyan mai kara, Mista S.O. Obila, ya sanar da kotun cewa wannan ne karon farko da karar ta zo gaban Alkalin.

Dalilin EFCC na neman dage shari'ar

Sai dai, ya ce ya samu umarni daga Babban Lauyan mai gabatar da kara, ya roki kotu ta dage shari'ar har sai baba ta gani.

“Na samu umarni daga Babban Lauyan masu gabatar da kara a wannan shari’ar, Sylvanus Tahir, SAN, na roki alkalin cewa tun da mun kira shaidu tara a gaban Mai Shari’a Inyang Ekwo, ya kamata mu jira ya dawo don ya kammala shari'ar,” in ji shi.

Saboda haka, a madadin EFCC da babban lauyanta, S.O. Obila ya roki kotun da ta dage shari’ar har sai baba ta gani.

Kara karanta wannan

An yi yunkurin kashe alkalin da ya yanke wa Nnamdi Kanu hukunci? Kotu ta yi bayani

A nasa bangaren, Lauyan Obiano, Onyeachi Ikpeazu, SAN, ya ce ba ya adawa da bukatar a dage shari’ar, domin mai gabatar da kara ya fadaa masa matsalar da tawagarsa ke fuskanta wajen dawo da shaidu tara wadanda tuni suka yi sheda.

Matakin da kotun tarayya ta dauka

Mai Shari’a Mohammed Umar ya daga shari'ar har sai baba ta gani kamar yadda aka bukata, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Tun farko an gurfanar da Obiano, wanda ya kasance Gwamnan Anambra daga Maris 2014 zuwa Maris 2022, a gaban kuliya a ranar 24 ga Janairu, 2024, kan tuhume-tuhume tara da suka shafi almundahana.

Obiano da EFCC.
Tsohon gwamnan Anambra, Willie Obiano da ofishin EFCC Hoto: Willie Obiano, EFCC Nigeria
Source: Facebook

EFCC ta zarge shi da karkatar da fiye da Naira biliyan 4 daga asusun tsaron jihar, inda ya tura kudin zuwa kamfanoni masu zaman kansu tare da canza wasu zuwa kudin waje.

Da gaske Obiano ya mutu a Landan?

A baya, kun ji cewa tsohon gwamnan Anambra, Willie Obiano ya karyata labarin da ake yadawa cewa ya mutu a Landan.

Tsohon kwamishinan yada labarai a jihar Anambra, Don Adinuba ya fito ya yi bayani kan wannan jita-jitta, yana mai bayyana cewa ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Mutane sun ga abin da ba su taba gani ba bayan maida Nnamdi Kanu gidan yarin Sakkwato

Mista Adinuba ya bayyana cewa tsohon gwamnan yana nan a raye bai mutu ba, yanzu haka ya yi tafiya zuwa jihar Texas da ke kasar Amurka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262