Gwamna Ododo Ya Shiga Yanayi da Allah Ya Yi Wa Sarki Mai Martaba a Najeriya Rasuwa
- Gwamna Ahmed Ododo ya yi alhinin rasuwar Sarkin Bassa Nge da ke jihar Kogi, Alhaji Abu Ali, wanda ya rasu yana shekaru 82
- Ododo ya bayyana kyawawan halayen marigayin, yana mai cewa Abu Ali mutum ne mai hikima da jajircewa wajen kawo ci gaba
- Gwamnan ya yi addu'ar Allah Ya ji kansa, kuma ya yi wa iyalansa da abokan arziki ta'aziyya bisa wannan babban rashi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi, Nigeria - Rasuwar mai martaba Sarkin Bassa Nge da ke jihar Kogi, Alhaki Abu Ali ta jefa Gwamna Ahmed Usman Ododo cikin yanayin alhini da jimami.
Gwamna Ahmed Ododo, ya bayyana matukar alhini bisa rasuwar Mai Martaba, Alhaji Abu Ali, Etsu na Masarautar Bassa Nge kuma tsohon Gwamnan Soja na Jihar Bauchi.

Source: Facebook
Tribune Nigeria ta rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin sakon ta'aziyya da aka fitar ta hannun Mashawarcinsa na Musamman kan Harkokin Yada Labarai, Ismaila Isah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Ododo ya fadi alheran Sarkin
Gwamna Ododo ya bayyana marigayi Sarkin a matsayin uba, mai hikima da tawali'u, wanda ya ba da gudummawa matuka ga zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba a Jihar Kogi da Najeriya.
Ya bayyana cewa ya samu labarin rasuwar Mai Martaba Etsu Bassa Nge da matukar bakin ciki, yana mai cewa Najeriya ta yi babban rashi.
Ododo ya tuno da hidima, ladabi, da jajircewa wajen kula jin dadin jama’arsa da Alhaji Abu Ali ya yi a tsawon rayuwarsa, ya kasance uba ga kowa kuma jajirtaccen soja.
"Ina tuna mulkinsa mai cike da mutuntaka da sanin ya kamata, shawarwarin da yake ba mu na hikima da jajircewarsa sun taimaka wajen ci gaban jiharmu da mutanenmu baki daya.
"Tabbas za a yi matukar rashin hidimarsa ta sadaukarwa da kuma hikimarsa, mun yarda da kaddarar Allah Madaukakin Sarki tare da gode masa bisa rayuwar da Sarki ya yi wajen kyautatawa jama'a.”
- Gwamna Ahmed Ododo.
Gwamnan Kogi ya mika sakon ta'aziyya
Gwamna Ododo ya yaba wa marigayi Etsu kasancewarsa sarki mai daraja kuma jagora abin koyi, yana mai cewa mulkinsa ya kawo da ci gaba ga Masarautar Bassa Nge.
Ya yi addu'ar Allah Ya ji kansa, tare da mika ta'aziyya ga iyalansa, Masarautar Bassa Nge, da dukkan wadanda ke cikin jimami rasuwar mai martaba.

Source: Facebook
Marigayi Alhaji Abu Ali, Birgediya Janar mai ritaya, ya yi aiki a matsayin gwamnan soja na Jihar Bauchi daga 1990 zuwa farkon 1992.
Bayan haka, ya ci gaba da kasancewa uban kasa kuma dattijo har zuwa rasuwarsa a ranar Litinin, 24 ga Nuwamba, 2025, yana da shekaru 82 a duniya, cewar Daily Trust.
Gwamna Bala ya yi ta'aziyya
A baya, kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya bayyana jimami da alhini sakamakon rasuwar tsohon gwamnan soja na jihar, Birgediya Janar Abu Ali (Mai ritaya).
Janar Abu Ali ya shugabanci Bauchi tsakanin Satumba 1990 zuwa Janairu 1992 a lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida, inda ya gudanar da ayyuka na ci gaban al’umma da suka bar tarihi.
Gwamna Bala ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai gaskiya, tawali’u da jajircewa ga al’ummarsa da kasa baki daya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


