‘Renewed Hope’: Tinubu Ya ba Gwamna Mukami gabanin Zaben 2027

‘Renewed Hope’: Tinubu Ya ba Gwamna Mukami gabanin Zaben 2027

  • Shugaba Bola Tinubu ya nada Gwamna Hope Uzodimma a mukami na musamman domin kara inganta ayyukan gwamnatinsa
  • Tinubu ya nada Uzodinma a matsayin “Jakadan Renewed Hope,” kuma zai jagoranci wayar da kan jama’a da tallata manufofin gwamnati
  • Uzodimma zai yi aiki tare da shugabannin APC da gwamnoni domin ƙarfafa goyon bayan shirye-shirye a dukkan kananan hukumomi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Gwamnan Jihar Imo a mukami na musamman domin wayar da kan yan Najeriya.

Tinubu ya nada Hope Uzodimma, a matsayin “Jakadan Renewed Hope” kafin kaddamar da shirin ci gaban yankuna a fadin kasar baki daya.

Tinubu ya nada gwamna Uzodinma mukami
Shugaba Bola Tinubu da Hope Uzodinma. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Hope Uzodinma.
Source: Twitter

Gwamna Uzodinma ya samu mukami daga Tinubu

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan bayanai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi: Tsohon gwamnan Bauchi, babban sarki, Abu Ali ya rasu

A sabon matsayi, Uzodimma zai zama Daraktan Yaɗa Manufofin Jam’iyya, wato jagoran sadarwa da tunkarar jama’a domin tallata manufofin gwamnatin Tinubu a sassan ƙasar.

Sanarwar ta ce Uzodimma, tare da shugabannin jam’iyyar APC da gwamnoni, zai jagoranci wayar da kai kan shirin gwamnatin tarayya.

Abin da Tinubu ke tsammani daga Uzodinma

A matsayinsa na Jakadan Renewed Hope, ana sa ran Uzodimma, wanda shi ne shugaban gwamnonin APC, zai tabbatar da daidaito, haɗin kai da tsari tsakanin jam’iyya da gwamnoni.

Zai kuma jagoranci ƙoƙarin samun goyon bayan jama’a musamman a matakin ƙananan hukumomi domin karfafa manufofin Tinubu a ƙasa baki ɗaya.

Tinubu ya dauko hanyar wayar da kan yan Najeriya kan gwamnatinsa
Shugaba Bola Tinubu yana jawabi a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Za a kaddamar da shirin tallafawa jama'a

Nadin ya zo ne yayin da gwamnatin tarayya ke shirin kaddamar da shirin ci gaban yankuna, wani muhimmin tsari 'Renewed Hope' da ke nufin kai ƙananan ayyuka, walwalar jama’a da tallafin rayuwa kai tsaye zuwa mazabu 8,809 na ƙasar.

Kara karanta wannan

Kano: Ganduje, 'yan APC sun fitar da 'dan takarar shugaban kasa da suke so a 2027

Shugaban ƙasa ya bayyana cewa yana sa ran Uzodinma da takwarorinsa za su yada nasarorin gwamnati tun daga 2023 domin ƙara karfafa sakon Renewed Hope a fadin ƙasa.

Fadar shugaban ƙasa ta kara da cewa Tinubu wanda ya hau mulki a Mayu 2023 yana ƙoƙarin karfafa bayanan siyasa kan abin da gwamnati ta cimma, musamman yayin da ake fama da tashin farashin kaya da tasirin cire tallafin man fetur.

A sakonsa ga Hope Uzodimma, Shugaba Tinubu ya umurce shi da ya tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun san nasarorin gwamnati kuma sun fahimci abin da ake kokarin cimmawa.

'Dalilin rashin kai wa 'yan bindiga farmaki'

Kun ji cewa hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana matsalolin da sojoji ke fuskannta wajen yaki da 'yan bindiga​.

Onanuga ya bayyana cewa dakarun sojojin sun san inda 'yan bindiga da ke sace mutane ke buya a cikin daji amma suna bi a hankali saboda gudun jawo matsaloli.

Ya bayyana cewa ba zai yiwu sojoji su kai farmaki wuraren da 'yan bindigan suke ba saboda gudun farmaki kan yaran da aka sace da sauran al'umma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.