Sheikh Gumi Ya Fadi yadda Dabararsa Ta Taimaki Gwamnatin Kaduna Aka Inganta Tsaro

Sheikh Gumi Ya Fadi yadda Dabararsa Ta Taimaki Gwamnatin Kaduna Aka Inganta Tsaro

  • Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya ce tsaron Kaduna ya inganta da 90% saboda gwamnati ta dauki shawara
  • Ya bayyana cewa ana ganin amfanin hawa teburin tattaunawa da 'yan ta'adda domin a samu matsayar kawo karshen kashe jama'a
  • Malamin fikihun ya jaddada cewa ba za a samu zaman lafiya ta hanyar zubar da jini kawai ba, illa ta hanyar hada kai da tattaunawa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Shahararren malamin adinin Musulunci a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa tsaron jihar ya samu gagarumin ci gaba.

Malamin ya danganta saukin matsalar tsaron da yadda gwamnatin Uba Sani ta fara amfani da tsarin tattaunawa da sulhu da miyagun 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Ahmad Gumi ya bada sharadin tsayawa Nnamdi Kanu a fito da shi daga kurkuku

Sheikh Gumi ya ce akwai alheri a tattaunawa da 'yan ta'adda
Sheikh Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi Hoto: Dr. Abubakar Mahmoud Abubakar Gumi
Source: Facebook

A hirarsa da Channels TV, Sheikh Gumi ya bayyana cewa a jihar Kaduna a yanzu ta samu daidaituwar tsaro da 90% idan aka kwatanta da yadda ake fama da hare-hare a baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gumi ya ce tsaron Kaduna ya inganta

Jaridar Leadership ta wallafa cewa Sheikh Gumi ya ce tsarin da yake kira hanyar samun zaman lafiya ba tare da zubar da jini ba yanzu ya fara samun karbuwa a matakan gwamnati.

Ya jaddada cewa duk wanda ke son a samu zaman lafiya a Najeriya dole ne ya saurari irin wannan tsari, kuma ana ganin amfaninsa a Kaduna.

Ya ce:

“Ina kokarin ganin mun samu zaman lafiya ba tare da zubar da jini ba, kuma ina ganin an fara fahimtarsa. Wasu gwamnatoci ma sun fara amfani da tsarin suna samun sakamako.”
Sheikh Gumi ya ce ana samun zaman lafiya a Kaduna
Taswirar jihar Kaduna, inda aka samu sassaucin matsalar tsaro Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sheikh Gumi ya ce Kaduna ta zama misali na yadda tattaunawa ke rage tarzoma, garkuwa da mutane da kuma hare-hare a yankunan karkara.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya fadi matsalar da ake fuskanta wajen kawar da rashin tsaro

A cewarsa:

“A Kaduna yanzu, a bangaren ’yan bindiga, mutane sun samu sauƙi da 90% yanzu. Jihar Kaduna ta yi kyau.”

Yadda tattaunawa ta rage ta'addanci, cewar Gumi

Malamin ya tunatar da cewa shekaru da dama yana shiga dazuka, yana ganawa da shugabannin ’yan bindiga kai tsaye, yana kuma fadakar da gwamnati kan muhimmancin sulhu.

Gumi ya ce yawancin wadannan kungiyoyi sun samo asali ne daga talauci, rashin kulawa da daukar fansa, wanda ya sa ake bukatar magance tushen matsalar, ba wai amfani da karfi ba.

Ya kara cewa:

“A Najeriya dole mu hada kan kowa. Idan kana da niyyar zaman lafiya, ina tare da kai.”

Gumi ya nuna sha'awar tsayawa Kanu

A wani labarin, kun ji cewa shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana aniyarsa na tsayawa daurarren shugaban IPOB, Nnamdi Kanu.

Sheikh Gumi ya kara da cewa Najeriya na bukatar hanyar sulhu da tattaunawa domin magance rikice-rikicen tsaro maimakon dogaro kacokan a kan amfani karfi da yaki da makamai.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya sanya ranar fara azumi, addu'o'i, ya shawarci Musulmi, Kirista

Ya bayyana cewa matukar shugaban 'yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu ya nuna nadama, zai shige gaba domin yi masa fafutukar samun afuwa daga gwamnatin Najeriya bayan ya sha dauri.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng