Ahmad Gumi Ya Bada Sharadin Tsayawa Nnamdi Kanu a Fito da Shi daga Kurkuku
- Sheikh Ahmad Gumi ya ce zai jagoranci neman a yafewa Nnamdi Kanu idan ya nuna nadama da goyon bayan zaman lafiya
- Fitaccen malamin ya bayyana haka ne yayin da ya ke kara tsayawa a kan bakarsa na a rika tattaunawa da 'yan ta'adda don sulhu
- Jawabansa sun zo yayin da Najeriya ke fama da sabon tashin hankali da garkuwa da mutane, musamman dalibai a jihohi da dama
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya ce zai shiga sahun gaba wajen neman a yi wa shugaban IPOB da aka yanke wa hukunci, Nnamdi Kanu, afuwa.
Kanu, wanda Kotun Tarayya a Abuja ta kama da laifuffuka bakwai na ta’addanci, ya dade a tsare, lamarin da ya raba kan wasu ’yan Najeriya.

Kara karanta wannan
Sheikh Gumi ya fadi yadda dabararsa ta taimaki gwamnatin Kaduna aka inganta tsaro

Source: Facebook
A hirarsa da Channels TV, Sheikh Gumi ya kare kiransa na amfani da hanyar tattaunawa wajen magance rikicin tsaro a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ahmad Gumi zai tsayawa Nnamdi Kanu?
Sheikh Ahmad Gumi ya kara da cewa idan har shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB da aka yankewa hukuncin daurin rai da rai, ya nuna nadama, zai tsaya masa.
A kalamansa:
“Idan wannan Kanu da aka daure saboda ya bukaci a kashe sojojinmu ya nuna nadama, ya kuma kira zaman lafiya, wallahi zan kasance a gaba wajen neman afuwa da kuma a yafe masa.”
Ya tuna irin yadda Shugaban Kasa Shehu Shagari ya bai wa Ojukwu afuwa bayan yakin basasa, da yadda Umaru Musa Yar’Adua ya bai wa matasan Neja Delta afuwa.
Malamin ya kara da cewa kare matsayarsa na amfani da hanyar tattaunawa, wajen kawo rikice-rikice da sabani a tsakanin al'umma.
Sheikh Gumi ya magantu kan ta'addanci
Gumi ya ce ba za a taba shawo kan matsalar tsaro da makami kadai ba, yana mai jaddada cewa a Arewa, akwai dama sosai ta sasanci da dawo da zaman lafiya idan aka ba tattaunawa muhimmanci.
A cewarsa:
“Mun ga Fulani makiyaya suna amsa kiran zaman lafiya. Me yasa kullum sai mu dage a kan amfani da karfi? Ko Amurka ba ta ci nasara a Afghanistan ba, Isra’ila ma ba ta shawo kan karamin yanki gaba daya ba.”

Source: Facebook
Ya kara da cewa rundunar sojin Najeriya ba ta da tsarin yaƙi da irin kungiyoyin da ake fuskanta yanzu, saboda haka idan ana son zaman lafiya sai dai a tattauna.
Maganar Gumi ta zo ne a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar karuwar garkuwa da mutane, musamman dalibai da masu ibada a jihohi daban-daban.
Gumi ya goyi bayan yafewa Maryam Sanda
A wani labarin, mun wallafa cewa Sheikh Ahmad Ahmad Gumi, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga afuwar da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Maryam Sanda.
A cewar Gumi, hukuncin kisa da aka yanke mata bai dace da adalcin shari’ar Musulunci ba, domin addinin ya fi karkata ga yafiya idan iyalan wanda aka kashe sun amince.
Ya bayyana cewa iyalan mamacin sun riga sun yi mata afuwa, kuma a Musulunci, wannan mataki ne mai daraja fiye da hukuncin kashe ta, kuma an yi shi a lokacin da ya dace.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

