"Akwai Dalili": Hadimin Tinubu Fadi Abin da Ya Sa Sojoji ba Su Iya Farmakar 'Yan Bindiga
- Hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana matsalolin da sojoji ke fuskannta wajen yaki da 'yan bindiga
- Bayo Onanuga ya bayyana cewa dakarun sojojin sun san inda 'yan bindiga da ke sace mutane ke buya a cikin daji
- Mai ba Bola Tinubu shawaran ya bayyana cewa ba zai yiwu sojoji su kai farmaki wuraren da 'yan bindigan suke ba saboda gudun matsaloli
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwa da dabaru, Bayo Onanuga, ya yi magana kan matsalar rashin tsaro.
Bayo Onanuga, ya bayyana cewa hukumomin tsaro sun san sunaye da wuraren da ’yan bindigan da suke da alhakin sace-sacen ɗalibai suke buya, ciki har da waɗanda suka dauke 'yan makaranta a jihar Neja.

Source: Twitter
Onanuga ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na tashar Arise News a ranar Litinin, 24 ga watan Nuwamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa ba za a farmaki 'yan bindiga ba?
A cewarsa, duk da cewa jami’an tsaro suna da cikakkun bayanan sirri kan ’yan bindigan, ba za su iya kai farmaki kai tsaye ba saboda tsoron jikkata ko hallaka fararen hula da aka yi garkuwa da su.
“Jami'an tsaro sun san dukkan ’yan bindigan da ke aiki a wannan yankin. Sun san su, sun san inda suke.”
- Bayo Onanuga
Ya jaddada cewa gwamnati ba za ta iya kai hari ta sama a wuraren da aka gano ’yan bindigan suke ba.
“Mutanenmu suna zaune a yankin da suke aiki. Don haka ba za ka iya kawai tashi ka kai hari ta sama ba. Dole a yi taka-tsantsan kada a je a hallaka ’yan Najeriya marasa laifi.”
- Bayo Onanuga
Onanuga ya tuna wani lamari da ya faru a Borno inda dakarun sojoji suka kashe fararen hula a bisa kuskure.
“A wasu shekaru da suka wuce, a Borno, an yi tunanin an samu bayanai masu kyau daga tauraron dan adam, sai aka kai hari wurin da ba daidai ba. Dole su guji irin wannan kuskure.”
- Bayo Onanuga

Source: Facebook
Mene ne adadin daliban Neja da aka sace?
Ya kara da cewa har yanzu ba a san adadin ɗaliban da aka sace a jihar Neja ba, domin makarantar da kuma kungiyar CAN ta Neja ba su samar da cikakken jerin sunaye ba.
“Yanzu haka hukumomi ba su da cikakken bayani kan adadin mutanen da suka ɓace. Kuna cewa ɗalibai sun ɓace, to ku kawo sunayensu. Mu san su waɗanda muke nema.”
- Bayo Onanuga
Onanuga ya kuma yi zargin cewa shugaban makarantar ya ki bayyana kansa, lamarin da ya kara wahalar da tantance sahihin adadin mutanen da aka yi garkuwa da su.
Gwamna Bago ya fadi masu taimakon 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.
Gwamna Bago ya bayyana cewa masu bada bayanai ne ke taimakawa 'yan bindiga wajen sace dalibai a makarantu.
Hakazalika, Gwamna Bago ya bukaci jama’a su rika bayar da ingantattun bayanai ga jami’an tsaro, tare da jan kunnen al’umma kan nuna kiyayyar addini.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


