'Obi Ya Goyi Bayan Trump Ya Kawo Hari Najeriya,' Onanuga Ya Ce ba Za Su Yafe ba
- Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya zargi Peter Obi da goyon bayan kawo harin Donald Trump Najeriya
- Bayo Onanuga ya ce gwamnatin tarayya ba za ta yafe wa Obi ba saboda maganganun da aka ji yana yi
- Hakan na zuwa ne yayin da shugaban Amurka ya yi barazanar kawo hari Najeriya da sunan kare Kiristocin kasar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Mai magana da yawun shugaba Bola Tinubu, Bayo Onanuga, ya caccaki Peter Obi kan zargin yarda da Amurka ta kawo farmaki Najeriya.
Ya ce gwamnati ba za ta yafe wa Peter Obi ba bisa ga wata magana da aka ji yana yi da wasu suka fassara a matsayin maraba da yiwuwar Amurka ta yi amfani da karfin soja a Najeriya.

Source: UGC
Maganar Bayo Onanuga ta biyo bayan wani bidiyo da ya sake bayyana a shafukan X da Peter Obi ya yi wani jawabi game da tsaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maganar da aka ce Peter Obi ya yi
Wanda ya wallafa bidiyon Peter Obi ya yi rubutu da ya yi ikirarin cewa dan siyasar ya ce zai amince da kawo farmakin Trump Najeriya.
Wanda ya sanya bidiyon ya yi ikirarin cewa Obi ya ce:
“Idan Donald Trump ya ce zai kawo farmaki Najeriya, zan tarbe shi hannu bibbiyu domin tsaro ya fi komai muhimmanci.”
Maganar Obi ta ginu ne a kan sakon shugaban Amurka Donald Trump na ranar 1, Nuwamba 2025, inda ya umarci ma’aikatar yakin Amurka ta fara shirin kai farmaki Najeriya don kare Kiristoci.
Bayo Onanuga ya caccaki Peter Obi
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya yi kakkausar suka ga kalaman da aka jingina wa Peter Obi, yana cewa:

Kara karanta wannan
"Ya sha gaban shugabannin Najeriya": Sanatan Kaduna ya yi magana kan salon mulkin Tinubu
“Ba za mu yafe ko manta da maganar Peter Obi ta goyon bayan kasar waje da kawo farmaki Najeriya ba."
Duk da cewa Peter Obi ya yi magana a kwanakin baya game da barazanar Trump, bidiyon da aka wallafa a yanzu bai nuna wajen da ya yi sabuwar maganar ba.
Martanin Najeriya ga ikirarin Trump
Trump ya danganta barazanar da ya yi da hare-haren Boko Haram, ISWAP da kuma wasu makiyaya, yana cewa Amurka ba za ta yarda da “kisan gilla” ba.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta karyata ikirarin nasa, inda jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar harkokin waje, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya ce hare-haren sun shafi kowa da kowa a kasar.
Shugaba Tinubu, yayin wani taron tsaro a Abuja, ya ce gwamnatinsa ta nada Kirista a matsayin babban hafsan tsaro domin tabbatar da daidaito.

Source: Twitter
The Guardian ta rahoto ya kara da cewa yana ci gaba da tuntubar shugabannin addinai don karfafa zaman lafiya tsakanin mabambantan bangarori.
Kiristan Najeriya ya caccaki Donald Trump
A wani labarin, mun rahoto muku cewa wani Kiristan Najeriya, JJ Omojuwa ya caccaki shugaban Amurka kan barazanar da ya yi wa Najeriya.
Japheth Omojuwa ya ce duk da shi Kirista ne amma ba ya goyon bayan maganar da Donald Trump ya yi kan tsaron kasarsa.
Ya yi martani ne yayin da wani Sanatan Amurka ya yi magana game da Najeriya a taron tsaro na duniya da aka yi a Canada.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

