Legas Ta Fara Rigakafi, An Kara Tsaro a Wuraren Ibada saboda 'Yan Ta'adda
- Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta dauki matakan riga-kafi bayan an samu karuwar matsalolin 'yan ta'adda a wasu jihohin Najeriya
- Jami'an tsaron sun sanar da ƙara tsaurara tsaro a makarantu wuraren ibada da muhimman cibiyoyi a jihar Legas domin karfafa tsaro
- Kwamishinan ’Yan Sandan Lagos, Olohundare Jimoh ya tabbatar da kama mutum 56 tare da kwato makamai daga hannun 'yan ta'adda
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Legas, Olohundare Jimoh, ya tabbatar wa jama’a cewa an kara tsaurara matakan tsaro a dukkannin sassan jihar.
Ya ce an bayar da karfi a kan tsaron muhimman wurare da suka hada da makarantu, masallatai, coci-coci da sauran wuraren da jama’a ke yawan ziyarta.

Kara karanta wannan
Yan sanda sun yi bayani game da 'kutsen' ƴan ta'adda a makarantar ƴan mata a Delta

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa Jimoh, wanda ya yi magana a hedikwatar rundunar a Ikeja a ranar Litinin, ya ce wannan shiri zai ci gaba har zuwa cikin sabuwar shekara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan sanda sun karfafa tsaro a Legas
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa rundunar za ta ci gaba da rike wuta wajen tabbatar da tsaro a wannan mataki har zuwa 2026 domin a kawar da duk wata barazana ga lafiyar mazauna jihar.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Legas, Olohundare Jimoh, jaddada cewa Legas na cikin kwanciyar hankali, kuma babu dalilin da zai sanya jama’a cikin damuwa.
Kwamishinan ya ce karin jami’an tsaro da ake tura wa sassan birnin na cikin sababbin matakan da ake dauka, tare da kara yawan rundunonin don kama masu laifi.
Wadannan tsauraran matakin tsaro ya biyo bayan jerin sace-sace da garkuwa da mutane da aka samu a wasu jihohi kamar Kwara, Kebbi da Niger kwanakin baya.
Kwamishinan yan sandan ya ce rundunar na aiki tukuru wajen dakile irin wadannan barazanar kafin su shafi Lagos.
'Yan sanda sun kama masu laifi
Kwamishinan ya bayyana sabuwar dabara da masu laifi ke amfani da ita na mayar da kansu direbobi ko ma’aikatan wankin mota domin sace motoci.

Source: UGC
A yayin bayani ga ’yan jarida, ya nuna motoci 10 da aka kwato, daga ciki har da Toyota Hilux, Range Rover, Land Cruiser, Lexus GX460, Honda CR-V da Toyota Corolla guda biyu.
An kuma kwato babur na Boxer Bajaj da aka yi amfani da shi wajen yunƙurin fashi, da kuma makamai iri daban-daban da suke ta'asa da ita.
Kwamishinan ya gargadi jama’a su guji barin makullan motarsu ga wanda ba su sani ba, musamman sababbin direbobi ko ma’aikatan wankin mota.
Babu hari a makarantar Delta - Yan Sanda
A baya, kun ji cewa Rundunar ’Yan Sandan Delta ta bayyana takaici da bacin rai kan jita-jitar da ta yadu a kafafen sada zumunta cewa wasu da ake zargin kai hari wata makaranta a jihar.
Wasu rahonni a ranar Litinin sun bayyana cewa ’yan bindiga sun kai hari makarantar sakandaren mata ta Utagba-Ogbe, Kwale, a karamar hukumar Ndokwa West, sun rika harbe-harbe.
Rundunar ta ce jita-jitar ta samo asali ne daga bayanan dalibai da ba a tabbatar ba, sannan wasu shafukan sada zumunta suka kara dagula batun ta hanyar yada shi ba a tantance ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

