Yajin Aiki: ASUU Ta Kira Taron NEC bayan Gama Sauraron Wakilan Gwamnatin Najeriya

Yajin Aiki: ASUU Ta Kira Taron NEC bayan Gama Sauraron Wakilan Gwamnatin Najeriya

  • Kungiyar ASUU ta shirya zama domin duba abubuwan da wakilan gwamnatin tarayya suka gabatar mata kafin yanke hukunci
  • Tuni dai wa'adin wata guda da ASUU ta bai wa gwamnatin tarayya ya kare, sai dai kungiyar ba ta yanke shawara ba har yanzu
  • Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa ya yi ikirarin cewa gwamnati ta biya kusan duka bukatun kungiyar ASUU bisa umarnin Bola Tinubu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Kwamitin Zartarwa ta Kasa (NEC) ta Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) za ta gudanar da taro gobe Laraba kan yiwuwar tsunduma yajin aiki.

A taron, NEC za ta yanke shawara kan mataki na gaba da kungiyar za ta dauka, bayan kammala tattaunawa da wakilan gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Yayale Ahmed.

Kungiyar malaman jami'o'i.
Hoton shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna da tambarin kungiyar Hoto: @asuunews
Source: Twitter

ASUU ta zauna da gwamnatin tarayya

Jaridar Punch ta ce tun farko tawagar gwamnatin tarayya da aka kafa ta sake zama da kungiyar ASUU a ranar Litinin domin kaucewa duk wani yunkuri na sake rufe jami'o'i.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kaduna ta taso El Rufai a gaba kan zargin biyan 'yan bindiga N1bn

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani babban jami'in NEC na ASUU, wanda ya yi magana da sharadin ba za a ambaci sunansa ba, ya ce taron wakilan gwamnatin Najeriya da na kungiyar zai karkare a yau Talata.

Wane mataki kungiyar ASUU za ta dauka?

"Mun fara wannan tattaunawa ne ranar Litinin kuma za a gama a ranar Talata.
Bayan haka, NEC za ta yi taro kuma ta yanke shawarar matakanmu na gaba nan da Laraba. Kowa zai san abin da muka yanke a lokacin,” in ji jami’in NEC.

Legit Hausa ta fahimci cewa wa'adin wata daya da ASUU ta bai wa Gwamnatin Tarayya ya cika a ranar Asabar, lamarin da ya jefa dalibai cikin zaman rashin tabbas.

Bukatun da ASUU ke so a cika mata

Kungiyar ta saba yin barazanar shiga yajin aiki har sai baba-ta-gani, inda take zargin gwamnati da nuna halin “ko-oho” game da bukatunta.

Bukatun sun hada da sake duba yarjejeniyar ASUU da Gwamnatin Tarayya ta 2009, biyan albashin da aka rike, alawus-alawus, da kuma fitar da kudade don farfado da jami'o'i.

Kara karanta wannan

An yi yunkurin kashe alkalin da ya yanke wa Nnamdi Kanu hukunci? Kotu ta yi bayani

Duk da wadannan korafe-korafe, Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, wanda a halin yanzu ba ya kasar, ya nace cewa Gwamnati ta biya bukatun kungiyar ASUU, in ji Bussiness Day.

Ministan ilimi, Tunji Alausa.
Hoton ministan harkokin ilimi na Najeriya, Dr. Tunji Alausa Hoto: @DrTunjiAlausa
Source: Facebook

Gwamnati ta biya bukatun ASUU

Da yake magana da manema labarai a Fadar Gwamnati makonni biyu da suka gabata, Alausa ya jaddada umarnin Shugaba Bola Tinubu na kada a bari ASUU ta rufe jami'o'i.

Alausa ya ce:

"Kamar yadda na fada muku, Shugaban Kasa ya ba mu umarnin cewa baya son ASUU ta shiga yajin aiki, kuma muna yin duk abin da za mu iya don tabbatar da cewa ɗalibanmu sun ci gaba da zama a makaranta."
“Mun cika kusan dukkan bukatunsu kuma mun dawo kan teburin tattaunawa. Za mu warware wannan matsa'ar nan kusa.”

NLC ta goyi bayan kungiyar ASUU

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar kwadagon Najeriya (NLC) ta bayyana goyon bayanta ga kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) a kokarin neman hakkokinta.

NLC ta lashi takobin taya kungiyar ASUU wannan yaki da ma yiwuwar shiga yakin aiki idan gwamnatin tarayya ta gaza biya mata bukatunta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fadi abin da tawagarta karkashin Ribadu ke yi a Amurka

Wannan na zuwa ne bayan barazanar da gwamnati ta yi wa kungiyar ASUU na hana albashi ga wadanda su ka tsunduma yajin aiki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262