'Yan Sanda Sun Yi Bayani game da 'Kutsen' Ƴan Ta'adda a Makarantar Ƴan Mata a Delta
- Rundunar yan sandan jihar Delta ta fusata bayan labarin cewa ƴan bindiga sun kai farmaki wata makarantar ƴan mata
- Rundunar ta ce da samun labarin, ta tura jami’ai a cikin gaggawa domin a kai agaji da daƙile duk wani mummunan al'amari
- Sai dai rundunar ta ce abin da aka tarar ya yi hannun riga da labarin da ya tayar da hankula iyaye da sauran jama'a a jihar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Delta – Rundunar ’Yan Sandan Jihar Delta ta bayyana takaici a kan jita-jitar cewa wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari makaranta.
An samu wasu labarai a ranar Litinin da ke cewa ƴan ta'adda sun kai hari makarantar sakandaren mata ta Utagba-Ogbe, Kwale, a jihar Delta.

Kara karanta wannan
Katsinawa sun sace iyalan ƴan ta'adda, an tilasta musayar mutanen da aka yi garkuwa da su

Source: Facebook
A sakon da rundunar ta wallafa a shafin Facebook ta ce labarin karya ne marar tushe, kuma an tayar da hankulan jama'a haka kawai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan sandan Delta sun fusata da labarin bogi
Sanarwar ta ce labarin ya ya samo asali ne daga bayanan da ba a tabbatar ba da wasu dalibai suka rika yadawa, daga baya kuma wasu shafukan sada zumunta suka dagula lamarin.
Rahotannin da aka rika yadawa sun ce ƴan bindiga sun kai hari , har da harbe-harbe Lamarin ya tayar da hankulan jama'a matuka.
Bayan samun labarin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Delta, CP Olufemi Abaniwonda, ya bada umarnin a gudanar da bincike a cikin gaggawa.
Rundunar ta ce an tura DCO na Kwale, SP Udofia Kufre, tare da tawagar sintiri domin tabbatar da gaskiyar zancen da sake nazarin tsaro a wurin.
Babu hari a makarantar Delta - Ƴan Sanda
An tattauna da Mataimakiyar Shugabar Makarantar da ma’aikacin tsaron da ke bakin aiki, kuma dukkanninsu sun tabbatar babu wani hari ko yunƙurin farmaki da aka kai masu.

Source: Facebook
Sun ce daliban sun tayar da hayaniya ba gaira babu dalilin saboda wani tsoro marar tushe.
Rundunar ta ce jami’an ’yan sanda sun kuma ziyarci sauran makarantun da ke cikin yankin Kwale domin tabbatar da cewa zaman lafiya ne.
Sun tabbatar cewa dukkanin makarantun na cikin koshin lafiya, tare da ci gaba da darussa ba tare da wata matsala ba.
An shawarci iyayen da suka garzaya domin daukar ’ya’yansu da su kwantar da hankalinsu, domin jita-jitar ce kawai.
CP Olufemi Abaniwonda ya yi gargadi a kan yada rahotanni marasa tushe wadanda ka iya tayar da hankula ko katse harkar karatu
Ƴan sanda sun ƙaryata labarin harin Borno
A baya, mun wallafa cewa rundunar ƴan sanda da gwamnati sun ƙaryata harin da aka ce an kai rantar mata a Maiduguri, a ranar Litinin, 24 ga Nuwamba 2025.
ASP Nahum Kenneth Daso, mai magana da yawun rundunar, ya ce rahotannin da ake yadawa a kafafen sada zumunta marasa tushe ne, ya kuma bukaci a yi watsi da su.
Rundunar ta yi kira ga iyaye da dalibai su kwantar da hankalinsu, su guji yada labarai marasa inganci da ka iya tayar da hankali tare da bayar da tabbacin an koma karatu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

