Shugaban INEC na Tsaka Mai Wuya, MURIC Ta Dawo da Batun Wasikar da Ya Tura Amurka

Shugaban INEC na Tsaka Mai Wuya, MURIC Ta Dawo da Batun Wasikar da Ya Tura Amurka

  • Ana ci gaba da matsa wa Bola Tinubu lamba kan korafin da shugaban INEC, Joash Amupitan ya kai gaban Amurka da UN tun 2020
  • Wasu takardu sun nuna cewa Amupitan ya nemi Amurka da Majalisar Dinkin Duniya su kawo dauki don kare rayukan kiristoci
  • Bayyanar wadannan takardu sun tayar da kura a Najeriya, MURIC ta bukaci Shugaba Tinubu ya canza tunani kan nadin Amupitan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Kungiyar Kare Hakkin Musulmin Najeriiya (MURIC) ta dage kan matsayarta kan wasikar da shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Joash Amupitan ya rubuta.

MURIC ta nuna damuwa kan wasikar da J. Amupitan ya rubuta, ya tura Amurka da Majalisar Dinkin Duniya, wacce ake ganin ya nuna kiyayya ga Musulmi.

Shugaban INEC da Bola Tinubu.
Hoton shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan da Bola Ahmed Tinubu Hoto: INEC Nigeria, @aonanuga1956
Source: Facebook

MURIC ta dage a kori shugaban INEC

Daily Trust ta tattaro cewa MURIC ta sake yin kira, a karo na biyu, ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ta nemi ya tsige Amupitan daga shugabancin INEC.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Bola Tinubu ya dauka bayan sace dalibai a Kebbi da Neja

Wata sanarwa daga shugaban kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ta ce kiran ya samo asali ne daga wannan wasika da ake danganta wa ga Amupitan, wacce ya tura Amurka.

Farfesa Akintola, a cikin sanarwar ta ranar Litinin, ya tambayi Gwamnatin Tarayya dalilin da ya sa ba a cire sabon shugaban INEC bayan wasikar da ya rubuta ta fito kowa ya gani ba.

"Idan za ku iya tunawa a cikin sanarwar da muka fitar ranar 10 ga Nuwamba, 2025, mun nemi a cire sabon shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, wanda aka zarga da rubuta takardar doka zuwa Amurka kan kisan Kiristoci a Najeriya.
"Tun da farko, Majalisar Koli ta Shari’a a Najeriya (SCSN) da Majalisar Gudanarwa ta Da’awa ta Najeriya (DCCN) sun yi irin wannan kiran.
"Bayan wadannan kungiyoyi na Musulunci, wasu kungiyoyi da dama sun goyi bayan cire shi ciki har da Voice of Liberty Nigeria."

- Farfesa Ishaq Akintola.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fadi abin da tawagarta karkashin Ribadu ke yi a Amurka

Me yasa gwamnatin Najeriya ta yi shiru?

Ya ce abin mamakin shi ne yadda gwamnatin tarayya ta yi shiru kan lamarin kamar yadda Farfesa Amupitan ya gaza fitowa ya musanta rubuta wasikar.

Akintola ya ci gaba da cewa:

"A gwargwadon saninmu, sabon shugaban INEC bai musanta cewa shi ne ya rubuta wannan wasika mai cike da karya, ce-ce-ku-ce da raba kan 'yan kasa ba. Haka kuma Gwamnati ba ta musanta ba.”
“Duk da haka, shirun gwamnati kan wannan batu mai matukar muhimmanci ya ba mu mamaki.
"Shin Gwamnatin Tarayya tana ta na kokarin rufe wannan lamarin ne idan wasu batutuwan da suka fi muhimmanci suka taso?"

Wani bangaren wasikar Joash Amupitan

Shugaban na INEC ya rubuta wata takardar doka a 2020, inda ya zargi manyan jami'an gwamnati da hannu a ayyukan da ake zargin kisan kiyashi da kashe-kash ne a fadin kasar.

A cikin rahoton mai taken “Nigeria’s Silent Slaughtee," Amupitan ya yi kira ga Amurka da Majalisar Dinkin Duniya su kawo dauki don dakile kisan da musulmi ke wa kiristoci.

Kara karanta wannan

Amurka ta fara canza tunani kan shirin kawo farmaki Najeriya bayan ganawa da Ribadu

Wannan wasika ta ja hankalin yan Najeriya musamman a. Arewa, hakan ya sa MURIC ta bukaci Tinubu ya sauke Amupitan, cewar rahoton PM News

Farfesa Ishaq Akintola.
Hoton shugaban MURIC, Ishaq Akintola da na Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: MURIC, @OfficialABAT
Source: Facebook

Majalisar Shari'a ta bi sahun MURIC

A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar Shari’ar Musulunci ta bukaci Bola Tinubu ya sake nazarin nadin Farfesa Joash Amupitan a matsayin shugaban INEC.

Majalisar ta bayyana bacin ranta kan wasikar da Amupitan ya rubuta tun 2020, wacce aka ce ya nuna wariya da kiyayya karara ga musulmi.

Ta kuma yi nuni da cewa rubutun ya ƙunshi kalamai “masu tada hankali da rashin adalci” da suka shafi rikice-rikicen Arewa da jihadin Shehu Ɗan Fodiyo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262