Katsinawa Sun Sace Iyalan Ƴan Ta'adda, An Tilasta Musayar Mutanen da aka Yi Garkuwa da Su
- Mutanen Runka a Safana, a jihar Katsina sun ceto mutane takwas da aka yi garkuwa da su ba tare da biyan kudin fansa ba
- Wasu ƴan ta'addan da ke daji ne suka faɗa masu, suka kwashe mutane sannan suka nemi a biya su fansar N25m
- Amma jama'an gari sun ramawa kura aniyarta, sun sun tilasta wa ƴan ta'addan sakin mutum takwas ba ko sisi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina – Mutanen garin Runka da ke ƙaramar hukumar Safana a Jihar Katsina sun samu nasarar kubutar da mutum takwas da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su.
Sun samu wannan nasarane ba tare da biyan ko kwabo daga cikin Naira miliyan 25 da miyagun suka nema ba a matsayin fansa ba.

Kara karanta wannan
Yan sanda sun yi bayani game da 'kutsen' ƴan ta'adda a makarantar ƴan mata a Delta

Source: Original
The Nation ta wallafa cewa Wannan lamari ya faru ne kwanaki kaɗan bayan da kungiyar ta kai farmaki garin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin harin, sun samu damar tafiya da mutane takwas tare da turo da bukatar kuɗin fansa daga baya kamar yadda suka saba.
Katsinawa sun bijire wa ƴan ta'adda
Wani mai amfani da shafin X, the_Lawrenz ya wallafa cewa sai dai a wannan karon, mazauna garin sun ƙi biyan fansa ko gana wa da ƴan ta'adda.
A Maimakon haka, suka shirya kansu cikin, suka bazama zuwa dazukan da ‘yan bindigar ke fakewa.
Da isar su wurin, suka yi samy nasarar kama wasu daga cikin iyalan miyagu – daga ciki har da mata, iyaye da yara.
Wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta ya nuna ɗan garin yana bayyana yadda suka ɗauki matakin.
Ya ce:
“Mun gaji. Su kan yi garkuwa da mutanenmu, mu ma mun kama nasu."
An shafe tsawon kwanaki a tsakanin mazauna ƙauye da ƴan ta'adda ana kallon kallo, kowa ya tsare iyalan kowa.
An cimma matsaya tsakanin Katsinawa da ƴan ta'adda
Rahoton ya ce bayan tsawon kwanaki uku, bangarorin biyu sun cimma matsaya da ta yi wa kowa dadi.

Source: Twitter
Matsayar mutanen Runka ta sa miyagun suka sake nazari, musamman ganin cewa rayuwar ‘yan uwansu na hannun mutanen gari.
A ƙarshe, ‘yan bindigar suka amince, suka saki dukkanin mutanen da suka yi garkuwa da su ba tare da wani aradi ba.
Wannan ya kawo ƙarshen tashin hankali a tsakanin bangarorin biyu bayan mutanen kauyen sun saki mutanen da suka tsare
Katsina: Amarya ta yi wa ango ta'addanci
A baya, kun ji cewa jama'a sun shiga cikin firgici da tashin hankali a kauyen Tashar Aibo da ke cikin ƙaramar hukumar Jibia, Katsina bayan amarya ta kashe ango.
Lamarin ya faru ne da yammacin Lahadi, inda ake zargin Aisha Muhammad ta daba wa angonta, Abubakar Dan Gaske, wuka a wuya kwanaki uku kacal da aurensu.
Rahotanni sun bayyana cewa Abubakar, shahararren mai sayar da masara a yankin, ya kwanta barci ne domin hutawa a gida lokacin da wannan abin takaicin ya faru.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

